Tsarin Ayyuka na Makon 2 ga Satumba
MAKON 2 GA SATUMBA
Waƙa ta 47 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 13, sakin layi na 10-17, da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Korintiyawa 1-9 (minti 10)
Na 1: 1 Korintiyawa 4:18–5:13 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Bin Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Zai Amfane Mu Ne a Yau?—td 30B (minti 5)
Na 3: Yadda Kiristoci Za Su Iya Kasancewa da Farin Ciki Sa’ad da Suke Rashin Lafiya—Filib. 4:6, 7 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 72
Minti 10: Yadda Za A Gabatar da Mujallu a Watan Satumba. Tattaunawa. Ka yi amfani da sakan 30 ko minti ɗaya don ka ambata dalilin da ya sa mutane a yankinku za su so mujallun. Bayan haka, sai ka ba masu sauraro dama su faɗi tambayar da za su yi da za ta sa mutane su so mujallar, kuma su faɗi nassin da za su karanta bisa ga jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro ɗin. Ka yi hakan ma da Awake! kuma idan da sauran lokaci, ka yi hakan da wani talifi dabam a cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! Ka sa a nuna yadda za a iya ba da kowacce cikin mujallun.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Ku Bi Misalin Barnaba. Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda bin misalin Barnaba zai taimaka mana sa’ad da muke wa’azi.
Waƙa ta 65 da Addu’a