Ku Ƙarfafa ’Yan’uwa Su Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane a Asabar ta Farko
A watan Mayu 2011, an ƙaddamar da tsarin nan na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a Asabar ta farko na kowane wata, kuma aka ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa yin haka. Don a taimaka mana mu cim ma hakan, an shirya wani talifi a fitowar Hasumiyar Tsaro na wa’azi mai jigo: “Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki.” Saboda haka, ya kamata a tattauna yadda za a yi amfani da wannan talifin wajen soma nazari da mutane a taron fita wa’azi na Asabar ta farko kuma a yi amfani da gabatarwar da ke cikin Hidimarmu ta Mulki wajen nuna yadda za a yi hakan.
Dattawa za su iya yin shawara cewa ’yan’uwa su haɗu a inda rukuninsu ke taron fita wa’azi a Asabar ta farko, ko kuma za su iya yin shawara cewa dukan ’yan’uwa su haɗu a Majami’ar Mulki don a yi taron. Amma idan ikilisiya fiye da ɗaya ne ke amfani da Majami’ar Mulkin, kada wata ikilisiya ta canja wannan rana da aka keɓe musamman don soma nazari a Asabar ta farko saboda cewa ana so a yi taron fita wa’azi tare a matsayin ikilisiya.