Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/13 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 5/13 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Yuni

“Miliyoyin mutane a faɗin duniya sun taɓa jin labarin Yesu. Shin ka taɓa yin tunani a kan yadda rayuwarmu za ta kasance da ma’ana idan muka bi koyarwar Yesu? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da aka faɗa a cikin mujallar nan.” Ka nuna masa talifin da ke shafi na 6 na Hasumiyar Tsaro ta Mayu-Yuni. Ku karanta kuma ku tattauna ɗaya daga cikin ayoyin da aka yi ƙaulinsu. Ka ba mutumin mujallun, kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ka tattauna wata aya dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki da shi.

Abin lura: A gwada wannan gabatarwa sa’ad da ake taron fita wa’azi a ranar 1 ga Yuni.

Hasumiyar Tsaro Mayu-Yuni

“A wasu lokatai mutane sukan yi tunanin cewa zai yi wuya a ga ƙarshen mugunta da wahala. Shin kana ganin muna da dalilin gaskata cewa lokaci yana zuwa da Allah zai kawo ƙarshen dukan mugunta da wahala? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. [Ka karanta Matta 24:37-39.] Talifin da ke shafi na 10 na wannan mujallar ya tattauna yadda za mu kasance da bangaskiya kamar Nuhu kuma mu sami albarka.”

Awake! Yuni

“Muna so mu ji ra’ayinka a kan wani batu. Kowa yana son yin rayuwa mai inganci. Shin kana ganin za mu cim ma hakan ta wajen saye-sayen kayayyaki? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wani shawarar da Yesu ya bayar a nan. [Ka karanta Luka 12:15.] Wannan mujallar ta tattauna yadda za mu kasance da ra’ayi mai kyau game da mallakar abubuwan duniya, kuma ta ba da shawara a kan yadda za mu yi sayayya.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba