Sanarwa
◼ Littattafan da za a ba da a watannin Mayu da Yuni: Ku yi amfani da warƙoƙin da kuke da su a ikilisiya. Idan kuka sami wanda yake son saƙonmu, ku nuna masa yadda muke amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma ɗaya daga cikin ƙasidun nan Ka Saurari Allah ko Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada wajen nazari da mutane. Yuli da Agusta: Albishiri Daga Allah! ko ɗaya daga cikin ƙasidun nan masu shafuffuka 32: Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa? Idan kana wa Musulmi wa’azi, za ka iya ba shi ƙasidar nan Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa ko kuma Shiriyar Allah—Hanyarmu ta Samun Aljanna.
◼ Idan an kama ka a asibiti a yankinku kuma kana son dattawan ikilisiyarku su ziyarce ka ko kuma idan an kama ka a asibiti a babban birni kuma kana son dattawa da suke hidima da rukunin Masu Kai Ziyara ga Majiyyata su san inda kake, mene ne za ka yi? Sa’ad da kake bayyana kanka a matsayin Mashaidin Jehobah a asibitin, ka gaya musu cewa kana son wasu Shaidun Jehobah su ziyarce ka a wurin. Tsarin Dokokin Nijeriya da kuma dokokin jinya na asibitoci sun hana ma’aikatan asibiti ba da bayani game da marasa lafiya ga mutane haka kawai, amma idan ka ba su ’yanci, za su iya gaya wa dattawan yanayin da kake ciki don ka sami ƙarfafa.