Tsarin Ayyuka na Makon 10 ga Yuni
MAKON 10 GA YUNI
Waƙa ta 114 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 7, sakin layi na 11-18 da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayyukan Manzanni 1-4 (minti 10)
Na 1: Ayyukan Manzanni 1:15–2:4 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Wajibi Ne Dukan Kiristoci Su Yi Wa’azin Bishara—td 8A (minti 5)
Na 3: Me Ya Sa Za A Iya Kwatanta Tunanin Wasu Mutane da Iska Mai Guba?—Afis. 2:1, 2 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 85
Minti 10: Muhimmancin Haɗa Ido da Waɗanda Muke Musu Wa’azi. Jawabi a kan bayanin da ke shafi na 124, sakin layi na 1 zuwa shafi na 125, sakin layi na 4 a cikin littafin Benefit From Theocratic Ministry School Education. Ka sa a ɗan yi gwajin da zai nuna wani mai shela yana wa’azi amma ba ya kallon wanda yake masa wa’azi da kyau. Sa’an nan a sake maimaita gwajin, amma a wannan karon, mai shelar yana kallon wanda yake masa wa’azi da kyau.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma? Sakatare ne zai tattauna wannan sashen. Ka ambata abin da aka cim ma a lokacin Tunawa da mutuwar Yesu, kuma ka yaba wa ’yan’uwa a kan ƙoƙarin da suka yi. Ka ba masu sauraro dama su faɗi labarai masu daɗi game da abubuwan da suka faru sa’ad da suke rarraba takardar gayyata zuwa taron Tunawa da mutuwar Yesu, ko kuma a lokacin da suka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci.
Minti 10: “Kuna Shirye Ku Yi Wasu Canje-canje?” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 74 da Addu’a