Tsarin Ayyuka na Makon 6 ga Mayu
MAKON 6 GA MAYU
Waƙa ta 26 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 5, sakin layi na 1-7 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Yohanna 1-4 (minti 10)
Na 1: Yohanna 3:22-36 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Ake Nufi da Yin “Tafiya Bisa ga Ruhu”?—Gal. 5:16 (minti 5)
Na 3: Ruhu Mai-Tsarki Ikon Allah Ne—td 16D (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 57
Minti 10: Yadda Za A Gabatar da Mujallu a Watan Mayu. Tattaunawa. Ka yi amfani da sakan 30 ko minti ɗaya don ka gabatar da wasu talifofi da mutane a yankinku za su so. Ta wajen yin amfani da jigon da ke bangon gaba na Hasumiyar Tsaro, ka ba masu sauraro dama su faɗi tambayar da za su yi da za ta sa maigidan ya so mujallar, sa’an nan su faɗi inda za su karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Ka yi hakan ma da Awake! kuma idan da lokaci ka yi hakan da wani talifi dabam a cikin Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! Ka sa a nuna yadda za a gabatar da kowacce cikin mujallun.
Minti 5: “Kuna Duba Allon Sanarwa a Kowane Lokaci Kuwa?” Tattaunawa.
Minti 15: “Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.” Tattauna bayanin da ke cikin wasiƙar da aka samu daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, wadda aka haɗa da wannan Hidimarmu ta Mulki. Ka ba masu sauraro dama su faɗi fitattun rahotanni daga cikin rahoton aikinmu na shekara ta 2012. Idan zai yiwu, ka shirya tun da wuri don wasu su faɗi labarai masu ƙarfafa zuciya daga littafin nan, 2013 Yearbook of Jehovah’s Witnesses. Kafin ka kammala, ka ƙarfafa waɗanda suke karanta Turanci su ƙarasa karatun littafin.
Waƙa ta 47 da Addu’a