Kuna Duba Allon Sanarwa a Kowane Lokaci Kuwa?
Dattawa da bayi masu hidima da kuma wasu da suke da ayyukan yi a cikin ikilisiya sukan duba allon sanarwa a kowane lokaci don su ga ko suna da aiki. Amma dukan ’yan’uwa a cikin ikilisiya za su iya samun bayanai masu muhimmanci a allon sanarwa. Kun san lokacin da aka ayyana wa rukuninku su share Majami’ar Mulki? Shin, ka san ko ikilisiyarku ta samu wata wasiƙa daga ofishin reshe ko kuma daga mai kula da da’irarku? Kun san jigon jawabi ga jama’a da za a yi a wannan makon don ku gayyaci ɗalibanku zuwa taron? An canja lokacin taro na ikilisiyarku ne ko kuma an canja wani tsari a rukuninku na fita wa’azi? An daina sanarwa game da yawanci waɗannan bayanai sa’ad da ake taro, kuma dattawa ba za su iya zuwa su sami kowane mai shela don su sanar da shi ba. Saboda haka, zai dace mu riƙa duba allon sanarwa a kowane lokaci. Idan muka tabbata cewa muna duba allon sanarwa a kowane lokaci, abubuwa za su ci gaba da gudana cikin ‘hankali kuma bisa ga ƙa’ida.’—1 Kor. 14:40.