Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 29 ga Afrilu, 2013. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan ne domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta a kowane mako.
1. Wace ƙa’ida mai muhimmanci ce Yesu ya bayar game da aure a Markus 10:6-9? [4 ga Maris, w08 2/15 shafi na 29, sakin layi na 11]
2. Shin mene ne ake nufi da a bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya? (Mar. 12:30) [4 ga Maris, w97 11/1 shafi na 9 sakin layi na 4]
3. Mene ne ma’anar “wahala” da aka rubuta a Markus 13:8? [11 ga Maris, w08 3/15 shafi na 12, sakin layi na 2]
4. Waɗanne littattafan tarihi ne Luka ya bincika sa’ad da yake rubuta labarin Linjila? (Luk 1:3) [18 ga Maris, w09 3/15 shafi na 32 sakin layi na 4]
5. Tun da yake Shaiɗan yana jiran ‘zarafi’ mai kyau don ya jarabce mu, mene ne ya kamata mu yi? (Luk 4:13) [25 ga Maris, w11 1/15 shafi na 23 sakin layi na 10]
6. Ta yaya za mu yi amfani da kalmomin da ke Luka 6:27, 28? [25 ga Maris, w08 5/15 shafi na 8 sakin layi na 4]
7. Me ya sa Yesu ya iya gafarta wa wata mata zunuban da ta yi tun kafin ya ba da ransa a matsayin fansa? (Luk 7:37, 48) [1 ga Afrilu, w10 8/15 shafuffuka na 6-7]
8. Ta yaya ne mabiyan Kristi za su “ƙi” danginsu? (Luk 14:26) [15 ga Afrilu, w08 3/15 shafi na 32 sakin layi na 1]
9. Wane sakamako ne kasancewar alamu “a cikin rana da wata da tamrari” zai kasance da shi a kan mutane? (Luk 21:25) [22 ga Afrilu, w97 4/1 shafi na 21 sakin layi na 8-9]
10. Wane darasi ne za mu koya daga yadda Yesu ya yi addu’a? (Luk 22:44) [29 ga Afrilu, w12 4/15 shafi na 17 sakin layi na 17]