Tsarin Ayyuka na Makon 15 ga Afrilu
MAKON 15 GA AFRILU
Waƙa ta 6 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 3, sakin layi na 9-13, da akwati (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Luka 13-17 (minti 10)
Na 1: Luka 16:16-31 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Da Yake Mu Ajizai Ne, Hakan Yana Nufin Cewa Ba Mu da Mutunci Ne a Gaban Allah?—Zab. 103:8, 9, 14; Gal. 6:9 (minti 5)
Na 3: Yesu Yana Ƙarƙashin Uba—td 16B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 95
Minti 10: Tambayoyin Masu Shela. Tattaunawa.
Minti 10: Hanyoyin da Za Ku Iya Faɗaɗa Hidimarku—Sashe na 2. Jawabi a kan bayani da ke shafi na 112, sakin layi na 3, zuwa shafi na 114, sakin layi na 1 a cikin littafin nan Organized To Do Jehovah’s Will. Ka gana da majagaba ɗaya ko biyu game da yadda suka sami damar yin gyara a tsarin ayyukansu don su soma hidimar majagaba.
Minti 10: Kuna Wa’azi a Inda Kuke Aiki Kuwa? Ka tattauna waɗannan tambayoyin da ke gaba: (1) Me ya sa ya dace abokan aikinku su san cewa ku Shaidun Jehobah ne? (2) Ta yaya za ku sanar da su? (3) Waɗanne irin abubuwa ne za su iya faruwa a wurin aikinku da za su ba ku damar yin wa’azi? (4) Me ya sa ya dace ku riƙa kasancewa da Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafanmu a wurin da kuke aiki idan hakan zai yiwu? (5) Me ya sa bai kamata ku yi wa’azi na tsawon lokaci sa’ad da kuke wurin aiki ba? (6) Kuna da labarin wani abu da ya faru sa’ad da kuke yin wa’azi a wurin aikinku?
Waƙa ta 45 da Addu’a