Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/13 p. 2
  • Tambayoyin Masu Shela

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyin Masu Shela
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Me ya kamata na sani game da aika sako ta wayar selula?
    Tambayoyin Matasa
  • Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?
    Tambayoyin Matasa
  • “Ban Sake Samunsa a Gida Ba!”
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ka Rika Yin La’akari da Mutane Kamar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 4/13 p. 2

Tambayoyin Masu Shela

◼ Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne suka shafi yin amfani da wayar salula sa’ad da muke halartan taron Kirista da kuma sa’ad da muka fita wa’azi?

“Akwai Lokaci Kuma Domin Kowane Abu” (M. Wa. 3:1): Wayar salula tana ba wa mutane damar yin magana da juna a kusan kowane lokaci. Amma akwai lokacin da bai kamata Kiristoci su bar waya ta raba musu hankali ba. Alal misali, lokacin taronmu lokaci ne da muke bauta wa Jehobah, muna samun koyarwa kuma muna ƙarfafa juna. (K. Sha 31:12; Zab. 22:22; Rom. 1:11, 12) Zai dace mu kashe wayarmu sa’ad da muke wajen taro kuma mu duba saƙonnin tes da aka aika mana bayan mun riga mun bar wajen taro, ko ba haka ba? Idan wani yanayi na gaggawa ya bukaci mu bar wayarmu a kunne, ya kamata mu saita wayar a yadda ba za ta dami mutane ba.

Ku Yi “Abu Duka Sabili da Bishara” (1 Kor. 9:23): A wasu lokatai, wayar salula tana taimakawa sa’ad da muka fita wa’azi. Alal misali, ɗan’uwan da ke ja-gora a wa’azi zai iya kira sauran ’yan’uwa da suke wa’azi tare don ya san yanayinsu. Wani lokaci, masu shela za su iya kiran wani da za su sake ziyarta ko kuma ɗalibinsu na Littafi Mai Tsarki kafin su ziyarce shi, musamman ma idan inda yake yana da nisa. Amma ya kamata mu mai da hankali ga yadda muke amfani da waya sa’ad da muka fita wa’azi, don kada ta raba mana hankali sa’ad da muke yi wa mutane wa’azi. (2 Kor. 6:3) Yayin da muke jiran sauran masu shela, bai kamata mu riƙa aika saƙonni ko kuma yin waya ga abokanmu ba. A maimakon haka, zai dace mu mai da hankali ga wa’azin da muke yi da kuma waɗanda muke wa’azi tare, ko ba haka ba?

Ku Nuna Sanin Yakamata (1 Kor. 10:24; Filib. 2:4): Kada mu riƙa makara da gangan sa’ad da muke zuwa taron fita wa’azi saboda mun san cewa za mu iya kiran wani daga baya ko kuma mu aika saƙon tes don mu san inda ake wa’azi. A duk lokacin da muka zo a makare, hakan yana ɓata tsarin da aka yi a rukuninmu. Hakika a wasu lokatai wani yanayi yana iya sa mu makara. Amma, idan mun saba zuwa da wuri, hakan zai nuna cewa muna daraja tsarin ƙungiyar Jehobah da kuma nuna sanin yakamata ga ɗan’uwan da ke ja-gorar rukunin da kuma sauran ’yan’uwa da muke wa’azi tare.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba