Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/13 p. 1
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Yunana

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Yunana
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Koyi Darasi Daga Kuskurensa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koya Daga Kuskurensa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ya Koyi Nuna Jin Ƙai
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ka Yi Ƙoƙari Ka Ɗauki Wasu Yadda Jehovah Yake Ɗaukansu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 4/13 p. 1

Ku Bi Gurbin Annabawa—Yunana

1. Waɗanne halaye masu kyau ne Yunana ya nuna?

1 Mene ne ra’ayinku game da annabi Yunana? Wasu suna masa kallon matsoraci ko kuma wanda ba shi da tausayi. Amma a bayyane yake cewa shi mutumi ne mai tawali’u da gaba gaɗi da kuma halin sadaukarwa. Ta yaya za mu bi “gurbin” Yunana a kasancewa da halaye masu kyau?—Yaƙ. 5:10.

2. Ta yaya za mu yi koyi da Yunana a yadda ya nuna tawali’u?

2 Tawali’u: Da farko, Yunana ya tsere zuwa wani ɓangare dabam da inda aka aike shi. Hakan ba abin mamaki ba ne, domin an san Assuriyawa da rashin imani sosai, har ma an kira Nineba “birni” mai alhaki. (Nah. 3:1-3) Jehobah ya yi masa horo kuma Yunana ya nuna tawali’u ta wajen idar da saƙon a lokacin da Allah ya sake ba shi damar yin hakan. (Mis. 24:32; Yun. 3:1-3) Ko da yake Yunana ya gudu da farko, amma daga baya ya yi nufin Allah. (Mat. 21:28-31) Shin, mun ƙudura mu ci gaba da yin wa’azin bishara ko da an yi mana horo ko kuma muna yankin da babu sauƙin yin wa’azi?

3. A wane lokaci ne kuke bukatar ku kasance da gaba gaɗi da kuma sadaukarwa a wa’azi?

3 Gaba gaɗi da Sadaukarwa: Sa’ad da Yunana ya fahimci cewa mummunar shawarar da ya yanke ta jefa ran masu jirgin ruwan cikin haɗari, Yunana ya yarda ya saɗaukar da ransa. (Yun. 1:3, 4, 12) Daga baya, da yake cika aikinsa a birnin Nineba, ya yi tafiya zuwa tsakiyar birnin, wataƙila yana neman wuri mai kyau don ya yi shelar hukuncin Jehobah a kan Nineba. Wannan ya nuna cewa Yunana ba matsoraci ba, amma annabi ne mai gaba gaɗi! (Yun. 3:3, 4) Mu kuma a yau fa? Hakika, muna bukatar mu roƙi Allah ya ba mu gaba gaɗi don yin wa’azi sa’ad da muke fuskantar hamayya. (A. M. 4:29, 31) Muna bukata mu kasance da halin sadaukarwa domin mu yi amfani da lokaci da muke da shi da kuma dukiyarmu wajen yin wa’azin bishara.—A. M. 20:24.

4. Me ya sa zai dace ku keɓe lokaci don yin bimbini a kan gurbi mai kyau da annabawan Jehobah suka kafa?

4 A duk lokacin da kuka karanta wani labari game da wani annabin Jehobah, za ku amfana idan kuka saka kanku a yanayinsa. Ku tambayi kanku: ‘Da a ce ni ne, da me zan yi? Ta yaya zan iya yin koyi da halayensa masu kyau?’ (Ibran. 6:11, 12) Za a tattauna ƙarin darussan da za mu iya koya daga wasu annabawan Jehobah masu aminci a Hidimarmu ta Mulki na nan gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba