Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/11 p. 4
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Ɗauki Mataki Nan da Nan
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Tambayoyin Masu Shela
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43)
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 11/11 p. 4

Akwatin Tambaya

◼ Wane ne ya kamata ya cika kufon da kuma aika saƙo ta Intane?

A yawancin lokaci, littattafanmu suna ɗauke da kufon ɗin da za a iya cikawa kuma a aika wa ofishin reshe domin a nemi littattafai ko ziyara daga Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, ana iya yin amfani da Yanar Gizonmu na www.watchtower.org don a bukaci nazarin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan tanadodin suna taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiya. Amma, an samu matsaloli sa’ad da masu shela suka yi amfani da waɗannan hanyoyin domin aika wa ’yan’uwansu ko wasu littattafai ko kuma a taimaka musu a ruhaniyance.

Wasu da aka aika wa littattafai da ba su bukaci hakan ba daga ofishin reshe sun nuna rashin jin daɗinsu, suna tunanin cewa ƙungiyarmu tana yi musu barazana kuma ta saka sunayensu a jerin waɗanda take aika wa saƙo. Wasu masu shela da aka aika su ziyarci mutumin da bai aika saƙo da kansa ba cewa a ziyarce shi sun samu kansu a tsaka mai wuya sa’ad da mutumin ya nuna fushinsa. Saboda haka, bukatar yin nazari da aka aiko mana ta hanyar kufon ko Yanar Gizo ya kamata ya kasance daga ainihin mutanen da suke son yin nazari ne, ba daga masu shelan da suka aika saƙo a madadin su ba. Idan muka fahimci cewa mai shela ne ya aiko saƙo cewa a tuntuɓi wani, ba za a yi aiki a kan saƙon ba.

Ta yaya za mu iya taimaka wa dangi ko aboki a ruhaniyance? Idan kuna son ya karɓi littafi, me zai hana ku aika littafin kai tsaye ga mutumin a matsayin kyauta? Idan ya furta cewa yana son yin nazari kuma yana son Shaidu su ziyarce shi amma ba ka san yadda za ka tuntuɓi dattawan ikilisiyar da ke yankin da yake ba, ka cika fom ɗin Please Follow Up (S-43) kuma ka ba sakataren ikilisiyar ku, wanda zai bincika fom ɗin kuma ya tura zuwa ofishin reshe. Amma idan wanda ke son yin nazarin yana ɗaure ne a kurkuku, inda ake ajiye waɗanda suke shan ƙwayoyi masu sa maye, ko a asibitin jiha (state hospital), kada ka tuntuɓi ofishin reshe a madadinsa. A maimakon haka, kana iya ƙarfafa shi ya tuntuɓi ’yan’uwan da suke ziyartar wurin ko kuma ya rubuta wasiƙa ga ofishin reshe da kansa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba