Hali Mafi Muhimmanci na Ƙwararren Malami
1. Mece ce hali mafi muhimmanci na ƙwararren malami?
1 Mene ne ke sa mutum ya zama ƙwararren malamin Littafi Mai Tsarki? Makarantar boko? Gogewa? Iyawa? Halin nan ne da ke sa a cika Doka, wadda ta bayyana almajiran Yesu, kuma ita ce mafi girma cikin halaye na musamman na Jehobah. (Yoh. 13:35; Gal. 5:14; 1 Yoh. 4:8) Ƙauna ce. Ƙwararrun malamai suna nuna ƙauna.
2. Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci mutane?
2 Ka Nuna Ƙauna ga Mutane: Yesu, Babban Malami, ya nuna ƙauna ga mutane, kuma hakan ya motsa su su saurare shi. (Luk 5:12, 13; Yoh. 13:1; 15:13) Idan mun damu da mutane, za mu yi amfani da kowace damar da muka samu don yin wa’azi. Tangarɗa irin su tsanantawa da ƙin gaskiya ba za su sa mu yi sanyin gwiwa ba. Za mu nuna cewa mun damu sosai da waɗanda muke yi wa wa’azi, za mu daidaita tattaunawarmu da ainihin abubuwan da ke damun su. Za mu ɗauki lokaci da son rai mu kasance tare da kowane ɗalibinmu na Littafi Mai Tsarki da kuma sa’ad da muke shirya dukan nazarin da za mu je mu yi.
3. Ta yaya ƙaunar da muke yi wa gaskiyar Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mana a hidimar mu?
3 Ka Ƙaunaci Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki: Yesu ya ƙaunaci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya ɗauki wannan gaskiyar a matsayin dukiya. (Mat. 13:52) Idan muna ƙaunar gaskiya, za mu yi magana da ɗoki, kuma hakan zai iya sa mutane su saurare mu da farin ciki. Irin wannan ƙaunar za ta taimaka mana mu mai da hankali ga bayani mai tamani da muke koya wa mutane maimakon kasawarmu, kuma hakan zai iya rage faɗuwar gaba sa’ad da muke hidimar fage.
4. Ta yaya za mu gina ƙauna?
4 Ka Gina Ƙauna: Ta yaya za mu iya gina ƙauna wa mutane? Ta wajen yin tunani a kan ƙaunar da Jehobah da Ɗansa suka nuna mana da kuma mummunar yanayi na ruhaniya da mutanen da ke yankinmu suke ciki. (Mar. 6:34; 1 Yoh. 4:10, 11) Ƙaunar da muke yi wa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta zurfafa idan muna nazari da bimbini kullum. Ƙauna fanni ne na ’yar ruhu. (Gal. 5:22) Saboda haka, muna iya roƙon Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki kuma mu roƙe shi ya taimaka mana mu ƙara kasancewa da ƙauna. (Luk 11:13; 1 Yoh. 5:14) Kome iliminmu, ƙwarewarmu a cikin gaskiya, ko gogewarmu, za mu iya zama ƙwararrun malaman Littafi Mai Tsarki ta wajen nuna ƙauna.