Dole ne a Yi wa Iri Ban Ruwa Don Ya Girma
1. Mene ne ake bukatar a yi wa ban ruwa idan ana son ya yi girma?
1 Irin da aka shuka a lambu yana bukatar a yi masa ban ruwa idan ana son ya girma. Abin da muke bukatar mu yi ke nan ga irin gaskiyar da muka shuka a zukatan mutane a yankinmu. (1 Kor. 3:6) Wajibi ne mu sake komawa ziyara kuma mu yi ban ruwa ga waɗannan iri na alama ta wajen yin amfani da Kalmar Allah idan muna son su yi saiwa, kuma su girma.
2. Ta yaya za mu iya sa maigida ya yi marmarin abin da za mu tattauna a ziyararmu ta gaba?
2 Ka Yi Tambaya: Sa’ad da kake shirya abin da za ka ce, me zai hana ka shirya tambaya mai sa tunani wadda za ka iya amsawa sa’ad da ka koma ziyara? Ka ta da tambayar a ƙarshen tattaunawarku ta farko, kuma ka tabbatar da cewa ka koma. Masu shela da yawa sun ga cewa yana da kyau su zaɓi wani batu daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? wanda zai ba su dama su nuna yadda ake yin nazarin Littafi Mai Tsarki.
3. Waɗanne bayanai ne ake bukatar daɗawa sa’ad da ake rubuta abubuwan da suka faru a tattaunawa ta farko?
3 Ka Rubuta Abin da Kuka Tattauna: Da zarar kun kammala tattaunawarku ta farko, ka rubuta dukan abubuwan da kuka tattauna. Ka rubuta sunan mutumin da adireshinsa. Yana da kyau ka rubuta kwanan wata da lokacin da ka tattauna da shi, abin da kuka tattauna, da kuma littafin da ka ba shi, idan akwai. Ya ambata cewa shi ɗan addini kaza ne? Yana da iyali? Ya ambata abubuwan da yake so da waɗanda ke damunsa? Irin waɗannan bayanan za su taimaka maka ka tattauna abubuwan da yake so sa’ad da ka sake komawa ziyara. Ka kuma rubuta ranar da ka ce za ka sake komawa ziyara da kuma tambayar da za ka amsa.
4. Me ya sa ya kamata mu nace wajen komawa ga waɗanda suka nuna cewa suna marmarin gaskiya?
4 Ka Nace: Shaiɗan ba zai huta ba a ƙoƙarce-ƙoƙarcensa na ‘amshe maganar’ da aka shuƙa a zuciyar mutane. (Mar. 4:14, 15) Saboda haka, kada ka yi ƙasa a gwiwa idan samun wanda ya nuna marmari a gaskiya a gida yana da wuya. Kana iya aika masa wasiƙa ko kuma ka ajiye ’yar wasiƙa a bakin ƙofarsa. Wata majagaba ta soma nazari a bakin ƙofa da wata mata amma ta kasa samun ta a gida, saboda haka, ta aika mata wasiƙa. Sa’ad da ’yar’uwar ta samu ganin ta a gida, matar ta furta cewa yadda aka nuna cewa an damu da ita ya ratsa zuciyarta sosai. Yayin da muke yin ban ruwa ga irin gaskiya, za mu iya shaida farin cikin da ake samu sa’ad da suka girma, suka ƙware, kuma suka “bada anfani, wani riɓi talatin, wani sattin, wani kuma ɗari.”—Mar. 4:20.