Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Ta Wajen Rubuta Bayani Game da Wanda Ya So Saƙonmu
‘Ka mai da hankali ga kanka, da kuma koyarwarka.’ (1 Tim. 4:16) Wannan shawarar da Allah ya hure manzo Bulus ya ba wa Timotawus ya nuna cewa zai dace mu ƙoƙarta mu sami ci gaba a matsayin masu bishara, ko da mu sababbi ne ko kuma ƙwararru. Don a taimaka mana mu yi hakan, daga yanzu za a riƙa wallafa talifofi dabam-dabam da ke ɗauke da jigon nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi” a cikin Hidimarmu ta Mulki. Kowane talifi zai tattauna hanya guda mai muhimmanci na kyautata koyarwarmu, kuma zai ba da shawarwari a kan yadda za mu iya bin wannan hanyar koyarwar da kyau. Kowane wata, zai dace kowa ya yi amfani da shawarwarin da aka bayar don kyautata wa’azi a wannan watan. A ƙarshen watan, za a gudanar da wani sashen Taron Hidima da zai ba mu damar bayyana yadda muka amfana daga bin shawarwarin. A wannan watan Fabrairu, ana ƙarfafamu mu ƙoƙarta mu rubuta bayani game da duk wanda ya so saƙonmu.
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Idan muna so mu cim ma hakkin da aka danƙa mana, wajibi ne mu yi wa’azi kuma mu sake ziyartar waɗanda suka so saƙonmu don mu koyar da su. Hakan zai taimaka mana mu yi ban ruwa ga iri da muka shuka. (Mat. 28:19, 20; 1 Kor. 3:6-9) Domin wannan, muna bukata mu koma wajen mutanen don mu tattauna da su game da abin da ke damunsu ko kuma mu ci gaba da tattaunawar da muka soma sa’ad da muka haɗu da su farko. Saboda haka, idan muka haɗu da duk wani da yake son saƙonmu, yana da muhimmanci mu rubuta bayanan da za su taimaka mana a tattaunawarmu na gaba da shi.
Yadda Za Mu Iya Yin Hakan:
• Ku tabbata cewa kuna da littafin ɗaukar suna da kuma alƙalami a cikin jakarku. Ku rubuta bayanan daidai kuma su fita sarai, sa’an nan ku adana su da kyau. Ku yi wannan rubutun nan da nan bayan kun gama tattaunawa da mutumin.
• Ku rubuta abubuwan da kuka sani game da maigidan, kamar su sunansa da adireshinsa da lambar wayarsa da kuma Imel ɗinsa. Ƙari ga haka, ku rubuta wasu abubuwa da kuka lura game da shi da kuma iyalinsa.
• Ku rubuta abin da kuka tattauna da shi, kamar nassosin da kuka karanta masa da abin da ya faɗa game da imaninsa da kuma littattafan da kuka ba shi. Ku kuma rubuta lokaci da rana da kuma kwanan watan da kuka haɗu da shi.
• Ku rubuta abin da kuke niyyar yi idan kuka koma wurin da abin da kuka yi alkawarin tattaunawa da shi da kuma ranar da kuka shirya za ku dawo.
• A duk lokacin da kuka koma wurinsa, ku rubuta duk wani sabon abin da kuka gano. Ba laifi ba ne idan kuka rubuta bayanai fiye da waɗanda kuke bukata.
Ku Bi Shawarar Nan Wannan Watan:
• A duk lokacin da kuke so ku rubuta wani bayani, ku gaya ma wanda kuke wa’azi tare abin da kuke rubutawa.