Tsarin Ayyuka na Makon 18 ga Afrilu
MAKON 18 GA AFRILU
Waƙa ta 17 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 18 sakin layi na 1-7 (minti 25)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ayuba 28-32 (minti 10)
Na 1: Ayuba 30:1-23 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Baftisma Farilla Ne Na Zama Kirista—td 9A (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Tunani Kafin Mu Yi Magana—Mis. 16:23 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 54
Minti 5: Sanarwa. Ka tunasar da kowa su shirya sashen nan “Kana Amfana Daga Mujallar Awake! Kuwa?” wadda za a tattauna a mako na gaba.
Minti 10: Sa’ad da Mutane Suke Bukatar Bayani. Jawabin da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 177, sakin layi na 2, zuwa ƙarshen shafi na 178. Ka sa a yi gajeren gwaji na abokin aiki da ba mai bi ba ne yana yi wa mai shela tambaya game da imaninmu. Mai shela ya ɗan juya yana yi wa kansa magana yana tunani yadda zai ba da amsa, sai kuma ya ba da amsar.
Minti 10: Akwatin Tambaya. Tattaunawa da dattijo zai yi.
Minti 10: Hanyoyin Yin Wa’azin Bishara na Gida Gida. Tattaunawa da aka ɗauko daga littafin nan Organized To Do Jehovah’s Will, shafi na 92, sakin layi na 3 zuwa shafi na 95, sakin layi na 2. Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da suke yin wa’azi na gida gida duk da ƙalubale, kamar rashin lafiya ko kuma kunya. Ta yaya ƙoƙarce-ƙoƙarcensu ya kai ga sakamako mai kyau?
Waƙa ta 26 da Addu’a