Za a Ba da Shaida Sosai
1. Ban da jawabin, mene ne kuma zai iya burge baƙi a lokacin Tuna Mutuwar Yesu? Ka ba da bayani.
1 A wane lokaci? A daren da za a Tuna Mutuwar Yesu. An yi ƙoƙari sosai wajen gayyatar mutane su halarta tare da mu. Ba abin da baƙi suka ji ba ne kaɗai zai iya burge su. Wata mata ta yi kalami musamman a kan abin da ta gani bayan ta halarci Tuna Mutuwar Yesu, ta faɗi cewa kowa yana da fara’a, kuma Majami’ar Mulkin tana da kyau da tsabta kuma waɗanda suka ba da kansu ne suka gina kuma suke kula da ita. Saboda haka, dukanmu za mu saka hannu don ba da shaida a wannan kiyayewa mafi muhimmanci da ake yi a duk shekara, ba mai jawabin kawai ba.—Afis. 4:16.
2. Ta yaya kowannenmu zai ba da shaida ga baƙi?
2 Ka Gai da Baƙi Sosai: Yin murmushi sosai tare da gai da baƙi cikin fara’a zai ba da shaida. (Yoh. 13:35) Ko idan ba za ka iya yin magana da kowa ba, za ka iya gabatar da kanka sosai ga mutanen da suke kusa da kai. (Ibran. 13:1, 2) Ka lura da baƙi da ba su san kowa ba. Wataƙila an gayyace su ne a lokacin kamfen ɗin. Kana iya tambayar su, “Wannan ne lokaci na farko da ka zo nan? Ka gayyace su su zauna tare da kai, kuma ka amsa duk tambayoyin da za su yi. Idan ikilisiyarku za su bar majami’ar da sauri don wata ikilisiya ta yi amfani da ita, kana iya cewa: “Ina son na san ra’ayinka game da tsarin ayyukan. Da akwai yadda zan tuntuɓe ka kuwa?”
3. Ta yaya za mu marabci waɗanda suka yi kasala?
3 Ka Marabci Waɗanda Suka Yi Kasala: Babu shakka, waɗanda suka daina halartar taro da fita hidimar fage za su halarta, har da waɗanda suke halartar Tuna Mutuwar Yesu kawai a kowace shekara. Ka marabce su, kuma ka sa su sani cewa kana farin cikin ganin su sosai. (Rom. 15:7) Dattawa suna iya zuwa gidansu ba da daɗewa ba bayan Tuna Mutuwar Yesu kuma su ƙarfafa su su ci gaba da cuɗanya da ikilisiyar. Muna addu’a cewa mutane da yawa da suka halarta za su motsa su ɗaukaka Allah ba don abin da suka ji kawai ba amma domin abin da suka gani don ‘nagargarun ayyukanmu da suke dubawa.’—1 Bit. 2:12.