Akwatin Tambaya
◼ Har tsawon wane lokaci ne za mu iya yin nazari da ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ke samun ci gaba?
Ya fi kyau a ci gaba da nazari da ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ke samun ci gaba har sai ya kammala littattafai biyu, wato, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.” Za a yi hakan ko idan ɗalibin ya yi baftisma kafin ya kammala littattafai biyun. Bayan ya yi baftisma za mu iya ci gaba da ba da rahoton sa’o’i da komawa ziyara da kuma nazarin da muka yi da shi. Idan wani mai shela ya bi mu zuwa wurin ɗalibin kuma ya sa baki a nazarin, zai iya ba da rahoto.—Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Maris 2009, shafi na 2.
Yana da muhimmanci sababbi su kafu cikin gaskiya sosai kafin mu daina nazari da su. Suna bukatar su zama “dasassu” cikin Kristi da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya’ don su jimre da gwaje-gwajen da za su fuskanta. (Kol. 2:6, 7; 2 Tim. 3:12; 1 Bit. 5:8, 9) Ƙari ga hakan, suna bukatar tacaccen “sanin gaskiya” don su koyar da mutane da kyau. (1 Tim. 2:4) Ta wurin kammala littattafai biyu da ɗalibanmu, muna taimaka musu su kafu sosai a kan ‘hanya wadda ta nufa wajen rai.’—Mat. 7:14.
Kafin dattawa su yarda wani ya yi baftisma, ya kamata su tabbata cewa ya fahimci muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki sosai kuma yana rayuwa da ta jitu da su. Ya kamata dattawa su mai da hankali musamman sa’ad da suke yin la’akari a kan ɗalibin da bai kammala littafin nazari na farko ba. Idan mutum bai cancanci yin baftisma ba, dattawa za su tabbata cewa ya samu taimako da ya dace don ya cancanci yin baftisma a nan gaba.—Ka duba ƙasidar nan ‘Ku je, Ku Almajirtar, Kuna yi Musu Baftisma’ shafuffuka na 57-60.
[Bayanin da ke shafi na 2]
Yana da muhimmanci sababbi su kafu cikin gaskiya sosai