Tsarin Ayyuka na Makon 6 ga Satumba
MAKON 6 GA SATUMBA
Waƙa ta 69
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 8 sakin layi na 1-7
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sarakuna 12-15
Na 1: 2 Sarakuna 13:1-11
Na 2: Hanyoyin da Za Mu Iya Samun Ruhu Mai Tsarki
Na 3: Ra’ayin Kirista Game da Bukukuwa (td 36A)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 60
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Ziyara ta Farko a Watan Satumba. Tattaunawa da masu sauraro. A watan Satumba za mu rarraba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa kuma za mu yi ƙoƙarin tattauna sakin layi ɗaya ko biyu da mai gida a ziyara ta farko. Ka tattauna shawarwari a kan yadda za a iya yin hakan. Ka sa a gwada gabatarwa ɗaya ko biyu.
Minti 10: Abin da Muka Koya Daga Wurin Yesu Game da Bauta ta Gaskiya. Jawabin da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba, 2010, shafuffuka na 16-17.
Minti 10: Ku Nanata Amfanin Bishara. Tattaunawa da masu sauraro na littafin nan Benefit from Theocratic Ministry School Education, shafi na 159. Ka gayyaci masu sauraro su ba da kalami a kan abubuwan da ke damun mutane a yankin. Ka nemi shawara a kan yadda za mu iya magance matsalolinsu a tattaunawarmu.
Waƙa ta 92