Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Agusta: Masu shela za su iya yin amfani da kowanne cikin waɗannan mujallu masu shafuffuka 32 da ke a ajiye: Allah Yana Kula Da Mu Kuwa da Gaske?, Ka More Rayuwa a Duniya Har Abada!, Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?, The Divine Name That Will Endure Forever, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu?, Minene Ma’anar Rai? Ina Yadda Zaka Same Shi?, Yayinda Wani Wanda Ka ke Ƙauna ya Mutu da kuma Za Ka Iya Zama Abokin Allah! Kuna iya ba da duk wata tsohuwar mujallar da ke ajiye a ikilisiya. Satumba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a haɗuwa na farko. Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! A inda masu gida suke da marmari, ka ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, kuma ka ƙudurta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Nuwamba: Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? Za a ba da cikakken bayyani game da yadda za a yi kamfen da wannan ƙasidar a dukan duniya a nan gaba. Ku gabatar da sabon ƙasidar tare da waɗannan ƙasidun: Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?, Za Ka Iya Zama Abokin Allah!
◼ Somawa daga watan Satumba, masu kula da da’ira za su ba da jawabi ga jama’a mai jigo “Ka Kawar da Idanunka Daga Abubuwan Banza!”
◼ An yi waɗannan gyare-gyare ga wuraren da za a halarci taron gunduma na shekara ta 2010/2011:
26-28 ga Nuwamba, 2010
BADAGRY na 9 (Turanci)
BENIN CITY na 9 (Yaren Kurame na Amirka)
3-5 ga Disamba, 2010
BADAGRY na 10 (Yaren Kurame na Amirka)
BENIN CITY na 10 (Edo)
7-9 ga Janairu, 2011
ULI na 12 (Yaren Kurame na Amirka)