Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 30 ga Agusta, 2010. Mai kula da makaranta zai yi bita ta minti 20 daga abubuwan da aka tattauna a makonnin 5 ga Yuli zuwa 30 ga Agusta, 2010.
1. Ta yaya yin bimbini a kan addu’ar keɓewa da Sulemanu ya yi zai daɗa godiyarmu ga mutumtakar Jehobah? (1 Sar. 8:22-53) [w05 7/1 shafi na 20 sakin layi na 3]
2. Kyautar garuruwa 20 a ƙasar Galili da Sulemanu ya yi wa Hiram Sarkin Taya ya jitu da Dokar Musa? (1 Sar. 9:10-13) [w05 7/1 shafi na 20 sakin layi na 2]
3. Wane darasi ne za mu iya koya daga 1 Sarakuna 12:13, 14? [w05 7/1 shafi na 21 sakin layi na 4]
4. Menene za mu iya kammalawa daga umurnin da Jehobah ya ba da cewa a yi wa Abijah kyakkyawar jana’iza? (1 Sar. 14:13) [cl shafi na 244 sakin layi na 11]
5. Me ya sa lokacin da Iliya ya ziyarci Ahab da farko yake da muhimmanci? (1 Sar. 17:1) [w08 4/1 shafi na 13 akwati]
6. Menene Iliya yake nufi da wannan furcin “ɗingishi a kan wannan imani da wancan”? (1 Sar. 18:21) [w08 1/1 shafi na 19 sakin layi na 2-3]
7. Kamar yadda aka nuna a batun Iliya, domin wane dalili ne Jehobah ya yi amfani da ikonsa game da bayinsa? (1 Sar. 19:1-12) [cl shafuffuka na 42-43 sakin layi na 15-16]
8. Me ya sa Naboth ya ƙi sayar wa Ahab gonar anab ɗinsa, kuma wane darasi ne za mu iya koya daga wannan aukuwar? (1 Sar. 21:3) [w97 8/1 shafi na 25 sakin layi na 18-20]
9. Ina ne “sama” da Iliya ya je “cikin guguwa”? (2 Sar. 2:11) [w05 8/1 shafi na 28 sakin layi na 1]
10. Me ya sa Elisha bai karɓi kyautar Na’aman ba? (2 Sar. 5:15, 16) [w05 8/1 shafi na 28 sakin layi na 2]