Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/10 p. 4
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 7/10 p. 4

Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Yuli-Satumba

Ka karanta Fitowa 20:15. Sai ka ce: “Ko da yake yawanci suna ƙoƙarin bin wannan dokar, wasu suna jin cewa za a iya yin sata da wasu fasaloli na rashin gaskiya idan mutum ya samu kansa a tsaka mai wuya. Menene ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan talifin ya tattauna amfanin kasancewa mai gaskiya a kowane lokaci.” Ka gabatar da talifin da ya soma a shafi na 11.

Yuli

“A yau, ana naɗa mata su zama firistoci ko shugabanni a coci da yawa. Menene ra’ayinka game da hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mata. [Karanta 1 Korintiyawa 14:34.] Amma dai, wata ayar ta ce mata suna da matsayi mai daraja a cikin ikilisiya. Wannan talifin ya bayyana.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 28.

Yuli-Satumba

“Ka taɓa mamakin dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala? [Ka bari ya ba da amsa.] Dubi yadda wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya furta tambayar da mutane da yawa suke yi. [Karanta Zabura 10:1.] Wannan talifin da ya soma a shafi na 4 ya ambata abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala da kuma abin da yake yi don ya sauƙaƙa ta.”

Agusta

“Wataƙila, Shaidun Jehobah sun taɓa tattaunawa da kai a dā. Ka taɓa yin tunani game da dalilin da ya sa muke zuwa kofa-kofa, duk da cewa mutane da yawa ba su da marmarin abin da muke cewa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Matta 24:14.] Mun lura cewa mutane da yawa sun yi mana mummunar fahimta. Wannan mujallar ta bayyana ko su wanene Shaidun Jehobah.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba