Rahotannin Hidimar Fage
A watan Yuli zuwa Nuwamba 2009, mutane 689 daga ikilisiyoyi dabam-dabam guda 73 a Nijeriya ne suka yi hidima a yankin da ba ikilisiyar da ke da shi. Sun yi amfani da awoyi 51,398 wajen neman masu kama da tumaki. ’Yan’uwan da suka yi wa’azi a ƙauyen Ndi Ogbaga, a Jihar Ebonyi, sun ba da wannan rahoton: “Wani mutum da ya halarci taro ya ce ya samu gaskiyar da ya daɗe yana nema. Ya halarci dukan tarurrukan har lokacin da muka bar ƙauyen.” Shin za ka iya shirya yanayinka don ka saka hannu a hidimar nan a wannan shekarar?