Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/10 p. 8
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 8/10 p. 8

Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Yuli-Satumba

“Yin renon yara nagari ba shi da sauƙi. Ka san wani a cikin Littafi Mai Tsarki da iyaye za su iya yin koyi da misalinsa don su yi nasara kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Yohanna 13:15.] Wannan talifin ya tattauna fannoni uku kawai na misalan da Yesu ya kafa wa iyaye game da yadda za su iya yin nasara wajen yin renon yara.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 18.

Agusta

“Wasannin bidiyo da yawa a yau suna gabatar da aljanu, mayu, da maita. Kana tsammani cewa aljanu suna wanzuwa da gaske kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta 1 Korintiyawa 10:20.] Wannan talifin ya nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da aljanu da kuma yadda za mu iya kāre kanmu.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 20.

Yuli-Satumba

“Wasu mutane ba sa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Kana tsammani cewa irin waɗannan mutanen za su iya kusaci Allah kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35.] Akwai misalan mutane da yawa waɗanda Littafi Mai Tsarki ya taimaka musu su canja salon rayuwarsu zuwa mai kyau. Wannan talifin da ya soma daga shafi na 26 zai taimaka maka ka ga yadda hakan ya yiwu da kuma yadda suka amfana.”

Satumba

“Kana tsammani cewa wayar selula, i-mail, dandalin hira, da kuma wasu hanyoyin sadarwa da mutane na zamani ta magance matsalar kaɗaici ko kuwa matsalar ta ƙaru? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga shawara ɗaya da za ta taimaka mana mu jimre wa kaɗaici. [Karanta Ayyukan Manzanni 20:35.] Wannan mujallar ta ba da ƙarin shawara daga Littafi Mai Tsarki.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba