Abin Da Ke Ciki
15 ga Disamba, 2014
© 2014 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
NA NAZARI
2-8 GA FABRAIRU, 2015
SHAFI NA 6 • WAƘOƘI: 92, 120
9-15 GA FABRAIRU, 2015
SHAFI NA 11 • WAƘOƘI: 97, 96
16-22 GA FABRAIRU, 2015
Yadda Za Mu Fuskanci Ƙarshen Zamani Tare
SHAFI NA 22 • WAƘOƘI: 107, 29
23 GA FABRAIRU, 2015–1 GA MARIS, 2015
Kana Godiya don Abin da Aka Ba Ka Kuwa?
SHAFI NA 27 • WAƘOƘI: 89, 135
TALIFOFIN NAZARI
▪ ‘Ka Saurara Kuma Ka Fahimta’
▪ Ka “Fahimci” Batun Kuwa?
Ta yaya za mu tabbata cewa mun fahimci ma’anar kwatance-kwatancen Yesu? Waɗannan talifofi biyu za su taimaka mana mu san yadda za mu bincika kwatance-kwatance bakwai na Yesu. Ƙari ga haka, za su taimaka mana mu san yadda za mu yi amfani da darussan da muka koya daga waɗannan kwatance-kwatancen a wa’azi.
▪ Yadda Za Mu Fuskanci Ƙarshen Zamani Tare
▪ Kana Godiya don Abin da Aka Ba Ka Kuwa?
Me ya sa ya kamata Kiristoci matasa su kasance da haɗin kai tare da mutanen Allah a wannan duniyar da matasa da yawa suna yawan son zuciya? A talifofin nan, za mu bincika wasu misalai masu kyau da marasa kyau na bayin Allah na dā. Ƙari ga haka, talifofin za su tattauna abubuwan da za su taimaka wa matasa da manya su yanke shawarwari masu kyau.
A FITOWAR NAN
4 Jehobah Yana Yi wa Masu Son Bayarwa Albarka
16 Ka Tuna?
17 Ya Kamata Ka Canja Ra’ayinka Ne?
BANGO: Wasu da suka zo shaƙatawa a Tamarindo Beach da ke bakin Tekun Fasifik a ƙasar Costa Rica sun yi farin ciki sa’ad da suka san cewa a nan gaba, duniya baki ɗaya za ta zama aljanna don mu kula da ita kuma mu ji daɗin rayuwa
COSTA RICA
MASU SHELA
29,185
MAJAGABA
2,858
Yadda ake kiran sunan Allah
Jéoba
a yaren Bribri
Jehová
da kuma a yaren Cabecar
Ikilisiyoyi biyu da rukunai biyu ne suke yin taro a yaren Bribri, kuma ikilisiyoyi uku da rukunai huɗu ne suke yin haka a yaren Cabecar. Asalin ’yan ƙasar Amirka ne suke yin waɗannan yarukan