Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 11/15 pp. 31-32
  • An Sami Haske a Kasar Japan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Sami Haske a Kasar Japan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • MAJAGABA MASU ƘWAZO
  • MANYA DA ƘANANAN “JEHU”
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 11/15 pp. 31-32

DAGA TARIHINMU

An Sami Haske a Ƙasar Japan

A RANAR 6 ga Satumba, 1926, wani haifaffen ɗan Japan mai kula mai ziyara da ke zama a Amirka ya koma ƙasarsu a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje. Wani da shi kaɗai ne mai karɓan littattafan Hasumiyar Tsaro ya tsaya yana jiran zuwansa. Wannan mutum ya kafa wani rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki a birnin Kobe. A nan ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi babban taronsu na farko a ranar 2 ga Janairu, 1927. Mutane 36 ne suka halarta kuma mutane 8 sun yi baftisma. Sun soma da kyau, amma ta yaya wannan ƙaramin rukuni za su kai bishara ga mutane miliyan 60 da ke ƙasar Japan da suke bukata su shaida hasken Littafi Mai Tsarki?

A watan Mayu na 1927, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma wa mutane kamfen game da wasu jawaban Littafi Mai Tsarki da za a bayar. Za a ba da jawabin farko a birnin Osaka, saboda haka, ’yan’uwan sun saka alamu a gefen hanya da kuma a manyan allon talla a wurare dabam-dabam a birnin. Ƙari ga haka, sun tura takardun gayyata guda 3,000 ga manyan mutane. Sun rarraba takardun gayyata guda 150,000 kuma sun sanar da jawaban a cikin sanannun jaridu a birnin Osaka da kuma a tikitin jiragen ƙasa guda 400,000. A ranar da za a ba da jawabin, jiragen sama guda biyu sun zagaya birnin kuma suka warwatsa takardun gayyata guda 100,000. Mutane 3,200 ne suka halarci taron kuma sun cika ɗakin maƙil don su saurari jawabi mai jigo: “The Kingdom of God Is at Hand” (Mulkin Allah Ya Kusa). An dakatar da mutane kusan dubu ɗaya don ɗakin ya yi kaɗan. Bayan jawabin, mutane fiye da 600 sun jira don sashen tambayoyi da kuma amsoshi. Watanni bayan haka, an ba da jawaban Littafi Mai Tsarki a birnin Kyoto da kuma wasu biranen da ke yammacin ƙasar.

A watan Oktoba na shekara ta 1927, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun shirya su riƙa ba da jawabai a birnin Tokyo. An sake tura takardun gayyata ga sanannun mutane, kamar su firayim minista da ’yan majalisa da limaman addinai da kuma shugabannin soja. An yi amfani da fosta da jaridu da kuma takardun gayyata guda 710,000 kuma mutane 4,800 ne suka halarci jawabai uku da aka bayar a babban birnin Japan.

MAJAGABA MASU ƘWAZO

Majagaba sun yi ƙwazo sosai wajen yi wa mutane wa’azi a gidajensu. Matsue Ishii da maigidanta Jizo, suna cikin majagaba na farko a ƙasar Japan, sun yi wa’azi a kashi uku cikin huɗu na ƙasar, daga birnin Sapporo da ke arewacin ƙasar, zuwa biranen Sendai da Tokyo da Yokohama da Nagoya da Osaka da Kyoto da Okayama da kuma Tokushima. ’Yar’uwa Ishii da kuma wata ’yar’uwa da ta manyanta mai suna Sakiko Tanaka, sun sanya tufafin gargajiya da ake kira kimono don su ziyarci manyan ma’aikatan gwamnati. A sakamakon haka, ɗaya daga cikin ma’aikatan ya ce a ba shi jerin littattafan The Harp of God da kuma Deliverance guda dari uku don a saka a laburare da ke gidajen yari.

Katsuo da Hagino Miura sun karɓi littattafai daga hannun ’yar’uwa Ishii kuma nan da nan suka fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Sun yi baftisma a shekara ta 1931, kuma suka soma hidimar majagaba. Haruichi da Tane Yamada, da wasu danginsu da yawa sun zama Shaidun Jehobah kafin shekara ta 1930. Iyalin Yamada sun soma hidimar majagaba kuma ’yarsu Yukiko, ta je hidima a Bethel da ke birnin Tokyo.

MANYA DA ƘANANAN “JEHU”

A lokacin, motoci suna da tsada sosai kuma hanyoyin ba su da kyau. Don haka, Kazumi Minoura da wasu matasa majagaba suna yin amfani da gidajen tirela da aka ba su suna Jehu, sunan wani ɗan karusa mai himma da ya zama sarki a Isra’ila. (2 Sar. 10:13-16) Manyan Jehu guda uku ne kuma kowanne yana da tsawon kafa 7.2, da faɗin kafa 6.2. Tsawonsa daga ƙasa kafa 6.2 ne, kuma kowanne yana ɗaukan majagaba shida. A ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar Japan, an ƙera Ƙananan Jehu guda 11 kuma kowannensu yana ɗaukan mutane biyu. Ƙari ga haka, keke ne yake jan kowannensu. Wani ɗan’uwa mai suna Kiichi Iwasaki, da ya ƙera waɗannan Jehu ya ce, “Kowane gida yana da tanti da kuma batirin mota da ke tanadar musu da lantarki don haske.” Majagaba suna ba da haske ta wajen wa’azin bishara da ƙwazo a faɗin ƙasar Japan, suna ta amfani da Jehu don hawa da sauka daga tsaunuka da kwari daga arewacin Hokkaido zuwa Kyushu da ke kudancin ƙasar.

Wani majagaba mai suna Ikumatsu Ota ya ce: “Sa’ad da muka isa wani birnin sai mu kafa Jehu a gaɓar kogi ko kuma a fili. Da farko mun ziyarci manyan mutanen garin kamar su magajin gari, bayan haka, sai mu bi gida gida muna ba da littattafanmu. Bayan mun gama wa’azi a garin, sai mu je wani gari.”

Babu shakka, “ranar ƙananan abu” ne ranar da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 36 suka halarci babban taronsu na farko. (Zak. 4:10) Bayan shekara biyar, wato a shekara ta 1932, majagaba da kuma masu shela 103 ne suka ba da rahoton wa’azi kuma sun ba da littattafai fiye da 14,000. A yau, ana yin wa’azi ga jama’a a manyan biranen ƙasar Japan. Ƙari ga haka, kusan masu shela 220,000 ne suke barin haskensu ya haskaka a faɗin ƙasar.—Daga tarihinmu a ƙasar Japan.

​

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba