Kana Godiya don Abin da Aka Ba Ka Kuwa?
‘Mun . . . karɓa . . ruhun da ke daga wurin Allah; domin mu sansance da bayebayen da Allah yake ba mu a yalwace.’—1 KOR. 2:12.
1. Wane irin tunani ne yawanci suke yi?
MUTANE da yawa sun taɓa jin irin wannan furucin: “Ba za ka san amfanin abin da kake da shi ba sai ka rasa.” Ka taɓa yin irin wannan tunanin? Idan mutum yana da wasu abubuwa tun yana yaro, zai iya yin wasa da su. Alal misali, wanda ya girma a gidan masu kuɗi ba ya ganin darajar abubuwan da ya mallaka a wani lokaci. Hakan zai iya faruwa da matasan da har ila ba su san abin da yake da muhimmanci a rayuwa ba saboda rashin wayo.
2, 3. (a) Mene ne ya kamata Kiristoci matasa su guje wa? (b) Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki koyarwar da muka samu da muhimmanci?
2 Idan kai matashi ne ko ɗan shekara ashirin da wani abu, mene ne yake da muhimmanci a gare ka? Yawancin mutane a duniya suna gani cewa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwa su ne albashi mai tsoka da gida mai kyau da kuma na’urar yayi. Idan muka mai da hankali ga waɗannan abubuwan kawai, za mu rasa abin da ya fi muhimmanci a rayuwa, wato albarkar da ake samu a bautar Jehobah. Abin baƙin ciki, miliyoyin mutane a yau ba su mai da hankali ga wannan ba. Idan iyaye Kiristoci ne suka yi rainonka, wajibi ne ka mai da hankali don kada ka yi banza da tarbiyya ta ibada da ka samu daga iyayenka. (Mat. 5:3) Rashin nuna godiya zai iya jawo mugun sakamako da zai ɓata rayuwarka.
3 Amma, za ka iya guje wannan mugun sakamakon. Mene ne zai taimaka maka ka ɗauki abubuwan da iyayenka suka koya maka da muhimmanci? Bari mu yi la’akari da wasu misalai a Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa ya dace mu ɗauki wannan koyarwar da muhimmanci. Ba matasa ba ne kawai za su amfana daga misalan da za mu tattauna, amma misalan za su taimaka wa kowane Kirista ya ɗauki wannan koyarwar da muka samu daga Jehobah da muhimmanci.
BA SU NUNA GODIYA BA
4. Mene ne 1 Sama’ila 8:1-5 suka bayyana game da ’ya’yan Sama’ila?
4 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran wasu da suka yi watsi da tarbiyya ta ibada da suka samu daga iyayensu. Wasu daga cikin waɗannan su ne ’ya’yan annabi Sama’ila, wanda ya soma bauta wa Jehobah tun yana ƙarami kuma ya kasance da aminci ga Allah. (1 Sam. 12:1-5) Sama’ila ya kafa misali mai kyau wa ’ya’yansa Joel da Abijah. Amma, ba su bi gurbinsa ba kuma suka bijire. Littafi Mai Tsarki ya ce akasin Mahaifinsu, sun “ɓata shari’a.”—Karanta 1 Sama’ila 8:1-5.
5, 6. Mene ne ’ya’yan Josiah da kuma jikansa suka yi?
5 Haka ne ’ya’yan Sarki Josiah suka yi. Josiah ya kafa misali mai kyau a bautar Jehobah. Sa’ad da aka samo littafin Dokar Allah kuma aka karanta wa Josiah, ya mai da hankali sosai don ya bi umurnin Jehobah. Ya yi aiki tuƙuru don ya kawar da bautar gumaka da sihiri daga ƙasar, kuma ya ƙarfafa mutanensa su bauta wa Jehobah. (2 Sar. 22:8; 23:2, 3, 12-15, 24, 25) Hakika, Josiah ya kafa misali mai kyau wa ’ya’yansa! Yaransa uku da kuma jikansa ɗaya sun yi sarauta, amma babu ko ɗaya daga cikinsu da ya nuna godiya ga abin da ya gāda.
6 Ɗan Josiah mai suna Jehoahaz ne ya gāji mahaifinsa a matsayin sarki, amma ya aikata “mugunta a gaban Ubangiji.” Ya yi sarauta na wata uku ne kawai, sai wani Fir’aunar ƙasar Masar ya jefa shi a kurkuku kuma wurin ne ya mutu. (2 Sar. 23:31-34) Bayan haka, ɗan’uwansa mai suna Jehoiakim ya yi sarauta na shekara 11. Shi ma bai nuna godiya ba don bai bi gurbin mahaifinsa ba. Ya aikata mugunta sosai, saboda haka, Irmiya ya annabta cewa “za a bizne shi da biznewar jāki.” (Irm. 22:17-19) Waɗanda suka yi sarauta bayan waɗannan su ne ɗansa Zedekiah da kuma jikansa Jehoiachin, su ma ba su bi misali mai kyau da Josiah ya kafa ba.—2 Sar. 24:8, 9, 18, 19.
7, 8. (a) Ta yaya Sulemanu ya yi watsi da tarbiyya mai kyau da aka yi masa? (b) Wane darasi ne za mu koya daga wasu da suka yi banza da tarbiyya ta ibada da aka yi musu?
7 Sarki Sulemanu ya sami tarbiyya mai kyau daga wurin mahaifinsa Dauda. Ko da yake an yi rainon Sulemanu a bautar Jehobah kuma ya soma sarauta da kyau, daga baya, bai nuna godiya ga abin da ya gāda ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Lokacin da Solomon ya tsufa, matansa suka juyar da zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli; zuciyatasa ba ta kamilta zuwa ga Ubangiji Allahnsa kamar zuciyar ubansa Dauda ba.” (1 Sar. 11:4) Saboda haka, Sulemanu ya ɓata dangantakarsa da Jehobah.
8 Abin baƙin ciki ne cewa an yi rainon waɗannan mutanen a bautar Jehobah kuma yanayinsu ya ba su damar yin abin da ya dace amma sun yi watsi da shi! Duk da haka, ba dukan matasa ba ne suka bi mugun tafarkin a dā, kuma haka ma yake a yau. Bari mu yi la’akari da wasu matasa a dā da suka kafa misali mai kyau wa Kiristoci matasa a yau.
SUN NUNA GODIYA DON ABIN DA AKA KOYA MUSU
9. Ta yaya ’ya’yan Nuhu suka kafa misali mai kyau? (Ka duba hoton da ke shafi na 27.)
9 ’Ya’yan Nuhu sun kafa misali mai kyau. An ba wa mahaifinsu umurni cewa ya gina jirgi kuma shi da iyalinsa su shiga cikin jirgin. ’Ya’yan Nuhu sun ɗauki yin nufin Jehobah da muhimmanci. Babu shakka, sun ba wa mahaifinsu haɗin kai kuma sun taimaka masa wajen gina jirgin. Bayan haka, sun shiga cikin jirgin. (Far. 7:1, 7) Me ya sa suka yi hakan? Littafin Farawa 7:3 ta ce sun saka duka dabbobin a cikin jirgin “domin a wanzar da iri bisa fuskar duniya duka.”’Yan Adam ma sun tsira. Da yake ’ya’yan Nuhu sun ɗauki rainon da mahaifinsu ya yi musu da muhimmanci, sun sami gatan kasancewa cikin waɗanda suka sa ’yan Adam suka ci gaba da wanzuwa kuma sun sake tabbatar da bautar Jehobah a duniya.—Far. 8:20; 9:18, 19.
10. Ta yaya Ibraniyawa matasa huɗu a Babila suka nuna godiya ga abin da aka koya musu?
10 Wasu karnuka bayan haka, wasu Ibraniyawa matasa huɗu sun nuna cewa sun ɗauki rainon da iyayensu suka yi musu da muhimmanci. Su ne Hananiah da Mishael da Azariah da kuma Daniyel. An kai su bauta a Babila a shekara ta 617 kafin zamaninmu. Da yake waɗannan matasan kyawawa ne kuma suna da ilimi, koyan al’adun Babila ba zai yi musu wuya ba. Amma sun ƙi yin haka. Hakan ya nuna cewa ba su manta da tarbiyyar da aka yi musu ba. Allah ya albarkaci waɗannan matasa huɗun don su ƙi bauɗe wa abin da aka koya musu sa’ad da suke ƙanana.—Karanta Daniyel 1:8, 11-15, 20.
11. Ta yaya wasu suka amfana daga abin da Yesu ya koya daga wurin Ubansa?
11 Yesu ɗan Allah, shi ne wanda ya kafa misali mafi kyau a nuna godiya ga abin da ya koya. Ya koyi abubuwa da yawa daga wurin Ubansa kuma ya ɗauke su da muhimmanci. Ya nuna hakan sa’ad da ya ce: “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” (Yoh. 8:28) Ƙari ga haka, ya so mutane su amfana daga abin da ya koya. Ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk. 4:18, 43) Ya koya wa masu sauraronsa amfanin kasancewa “ba na duniya ba” don mutanen duniya ba sa ɗaukan bautar Allah da muhimmanci.—Yoh. 15:19.
KA NUNA GODIYA GA ABIN DA KA KOYA
12. (a) Ta yaya 2 Timotawus 3:14-17 ya shafi matasa da yawa a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata Kiristoci matasa su yi tunani a kai?
12 Wataƙila kai ma iyayenka sun yi rainonka don ka bauta wa Jehobah, kamar matasan da aka ambata ɗazu. Idan haka ne, abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Timotawus wataƙila ya shafe ka. (Karanta 2 Timotawus 3:14-17.) Iyayenka ne suka ‘koya’ maka yadda za ka bauta wa Allah na gaskiya da kuma yadda za ka faranta masa rai. Wataƙila iyayenka sun soma koyar da kai tun kana jariri. Ta yin hakan, sun “hikimtar da kai zuwa ceto ta wurin bangaskiya wanda ke cikin Kristi Yesu” da kuma taimaka maka ka kasance “shiryayye” don yin aikin Allah. Wata muhimmiyar tambaya ita ce, Shin za ka ɗauki rainon da suka yi maka da muhimmanci? Wataƙila, hakan zai bukaci ka bincika kanka. Za ka iya yin tunani a kan waɗannan tambayoyin: ‘Yaya nake ji idan na tuna cewa ina cikin shaidu masu aminci? Yaya nake ji idan na tuna cewa ina cikin mutane kaɗan a duniya da Allah ya amince da su? Ina ɗaukan wannan babban gata na sanin gaskiya da muhimmanci kuwa?’
13, 14. Waɗanne abubuwa ne wasu Kiristoci matasa suke fama da su, amma me ya sa bai dace su yi waɗannan abubuwan ba? Ka ba da misali.
13 Wataƙila wasu matasa da iyaye Kiristoci suka yi rainonsu ba za su fahimci bambancin da ke tsakanin ƙungiyar Jehobah da duniyar Shaiɗan ba. Har ma wasu sun so su ɗanɗana yadda rayuwa take a duniyar Shaiɗan. Amma za ka tsaya kan hanya kuma mota ta buge ka kawai don kana son ka san ko za ka ji rauni ko kuwa za ka mutu ne? A’a! Hakazalika, ba zai dace mu ɗanɗana “haukar lalata” na wannan duniyar don kawai muna so mu gane baƙin cikin da hakan yake jawowa ba.—1 Bit. 4:4.
14 An yi rainon wani matashi mai suna Gener a Asiya a iyalin Kirista. Ya yi baftisma a lokacin da yake shekara 12. Sa’ad da yake matashi sai ya soma sha’awar rayuwar mutanen duniya. Ya ce: “Ina son in ɗanɗana irin ’yancin da mutanen duniya suke mora.” Saboda haka, Gener ya soma yin abubuwan da ba su da kyau a ɓoye. Sa’ad da yake shekara 15, sai ya soma yin rayuwar banza irin na abokansa. Yana shaye-shaye da kuma baƙar magana kamar su. Yakan dawo gida da dare, bayan ya gama buga sunuka da wasannin kwamfuta da abokansa. Amma, da shigewar lokaci, sai ya soma gane cewa irin wannan rayuwar ba ta sa farin ciki. Rayuwar banza ce. Yanzu ya dawo ƙungiyar Jehobah kuma ya ce: “Har ila ina fuskantar ƙalubale da yawa, amma albarka da nake samu daga Jehobah ya ninka su duka.”
15. Mene ne ya kamata waɗanda ba a yi rainonsu a iyalin Kirista su tuna?
15 Hakika, akwai wasu matasa da ke ciki ikilisiya da ba a yi rainon su a cikin ƙungiyar Jehobah ba. Idan kai ɗaya daga cikinsu ne, ka yi tunanin gatan da kake da shi yanzu don ka san Mahaliccinka kuma kana bauta masa! A cikin biliyoyin mutane da ke duniya, Jehobah ya zaɓe ka kuma ya bayyana maka gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ba ƙaramin gata ba ne. (Yoh. 6:44, 45) A cikin kowane mutum dubu, ɗaya ne kawai ya san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma kai ɗaya ne daga cikin su. Shin bai kamata hakan ya sa mu farin ciki ba, ko da ta yaya ne muka koyi gaskiya? (Karanta 1 Korintiyawa 2:12.) Gener ya ce: “Idan na tuna wannan, sai in soma fargaba. Shin wane ne ni da Jehobah mahaliccin sararin sama zai san da zama na?” (Zab. 8:4) Wata ’yar’uwa Kirista daga yankin ta ce: “Ɗalibai sukan ji daɗi idan malaminsu ya san sunansu da wasu abubuwa game da su. Saboda haka, sanin cewa Jehobah Babban Malaminmu ya san da zamanmu ba ƙaramin gata ba ne!”
MENE NE ZA KA YI?
16. Wane tafarki ne ya dace Kiristoci matasa a yau su bi?
16 Da yake kana da wannan babban gata, shin bai kamata ka kuɗiri niyyar kasancewa cikin mutane ƙalilan da suka bi tafarki mai kyau a rayuwarsu ba? Ta hakan, za ka kasance cikin bayin Allah masu aminci. Ka nuna hikima don wannan matakin da ka ɗauka, a maimakon bin tafarkin matasa da yawa da suke kamar waɗanda ba sa cikin hankalinsu kuma suna bin tsarin rayuwar da za ta kai su ga halaka.—2 Kor. 4:3, 4.
17-19. Mene ne zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da kasancewa dabam da mutanen duniya?
17 Hakika, hakan ba ya nufin cewa kasancewa dabam da mutanen duniya yana da sauƙi a ko yaushe. Amma yin hakan shi ne abin da ya dace. Alal misali: Ka yi tunanin wanda yake son yin wasa a Olimfik. Wajibi ne ya kasance dabam da sauran mutane kafin ya cancanta. Wataƙila zai yi watsi da abubuwa da yawa da za su ɓata masa lokaci, wato abubuwan da ba za su ba shi damar horar da kansa ba. Amma, idan ya kasance dabam da tsaransa, zai sami zarafin horar da kansa sosai kuma ya cim ma burinsa.
18 Mutanen duniya suna rayuwar sha yanzu maganin yanzu. Idan kana hangen nesa, za ka fahimci cewa kasancewa dabam da mutanen duniya da kuma guje wa lalata da abubuwan da za su ɓata dangantakarka da Allah, zai sa ka sami “hakikanin rai.” (1 Tim. 6:19) ’Yar’uwar da aka ambata ɗazun ta ce: “Idan ka nace wa abin da ka yi imani da shi, a ƙarshe za ka yi farin ciki. Hakan ya nuna cewa kana da ƙarfin ƙin yin abubuwan da yawancin mutane suke yi a wannan duniya. Abu mafi muhimmanci, za ka san cewa Jehobah Allah ya amince da kai don kana faranta masa rai! Lokacin ne za ka fahimci cewa kasancewa dabam yana da kyau!”
19 Idan mutum ya mai da hankali ga abin duniya, rayuwarsa ba za ta kasance da ma’ana ba. (M. Wa. 9:2, 10) Idan kai matashi ne kuma ka yi la’akari sosai da yadda rayuwa take, za ka gane cewa hikima ce ka guji yin “irin tafiya da Al’ummai suke yi” kuma ka yi rayuwa mai ma’ana.—Afis. 4:17; Mal. 3:18.
20, 21. Idan muka ɗauki matakan da suka dace, wace albarka ce za mu samu, mene ne ake bukata a gare mu?
20 Idan muka ɗauki matakan da suka dace, za mu yi rayuwa mai gamsarwa yanzu. Ƙari ga haka, za mu “gāji duniya” mu zauna a cikinta har abada. Akwai abubuwa da yawa da za mu ji daɗinsu kuma ba za mu iya tuna da su duka ba. (Mat. 5:5; 19:29; 25:34) Ko da yake, Allah ba ya ba mu waɗannan abubuwan haka kawai. Ya bukace mu mu yi masa biyayya. (Karanta 1 Yohanna 5:3, 4.) Amma bauta masa cikin aminci yanzu yana da amfani!
21 Babu shakka, Allah ya albarkace mu sosai da abubuwa da yawa! Mun san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwar kuma mun san gaskiya game da Allah da kuma nufinsa. Muna da gatan amsa sunansa da na kasancewa Shaidunsa. Allah ya ce zai kasance tare da mu. (Zab. 118:7) Bari dukanmu yara da manya, mu nuna godiya ta yin abubuwan da ke nuna cewa mun ƙudiri niyyar ba wa Jehobah “ɗaukaka har abada.”—Rom. 11:33-36; Zab. 33:12.