Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 7/15 pp. 7-11
  • Jehobah “Ya San Wadanda Ke Nasa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah “Ya San Wadanda Ke Nasa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “NI UBANGIJI BA MAI-SĀKEWA BA NE”
  • ‘HATIMIN’ DA KE INGANTA BANGASKIYA GA JEHOBAH
  • YIN IBADA DA ZUCIYA ƊAYA BA AIKIN BANZA BA NE
  • AMINCI DA KE SA MU FARIN CIKI
  • Bayin Jehobah Suna Yin “Nesa da Aikata Mugunta”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Jehobah Ya San Ka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Jehobah Yana Kaunarka Sosai!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 7/15 pp. 7-11

Jehobah “Ya San Waɗanda Ke Nasa”

“Idan kowane mutum yana ƙaunar Allah, wannan mutum sananne ne gare shi.”—1 KOR. 8:3.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne ya tabbatar mana cewa ba wanda zai iya canja nufin Jehobah?

  • Waɗanne abubuwa biyu ne ƙa’idodin Jehobah suka ƙunsa?

  • Ta yaya darussan da muka koya a littafin 2 Timotawus 2:19 suka ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah?

1. Ka ba da wani labarin Littafi Mai Tsarki da ya nuna yadda wasu bayin Allah suka ruɗi kansu. (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

HARUNA Babban Firist ya tsaya a ƙofar mazauni da sanyin safiya, yana riƙe da kaskon ƙona turare. Korah da mutane 250 suna tsaye a gefensa kuma kowannensu yana riƙe da kaskon ƙona turare ga Jehobah. (Lit. Lis. 16:16-18) Za a ɗauka cewa dukansu amintattun bayin Jehobah ne. Amma a gaskiya, Korah da masu mara masa baya ’yan tawaye ne kuma suna da fahariya da son kai domin suna so su ƙwace matsayin Haruna na firist. (Lit. Lis. 16:1-11) Sun yaudari kansu ta wurin yin tunanin cewa Allah zai amince da ibadarsu. Amma zaton nan reni ne ga Jehobah wanda yake sanin abin da ke zukatan mutane kuma ya san cewa su munafukai ne.—Irm. 17:10.

2. Mene ne Musa ya ce zai faru, kuma ta yaya kalamansa suka cika?

2 Kafin wannan ranar, Musa ya ce: “Da safe Ubangiji za ya nuna waɗanda su ke nasa.” (Lit. Lis. 16:5) Jehobah ya bambanta waɗanda suke masa ibada da gaske da masu ibadar ƙarya. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye [Korah da] mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da ke miƙa hadaya da turare.” (Lit. Lis. 16:35; 26:10, Littafi Mai Tsarki) Amma Haruna bai mutu ba, yana tsaye. Kuma ta haka ne Jehobah ya nuna cewa Haruna ne ainihin firist wanda yake masa ibada da gaske.—Karanta 1 Korintiyawa 8:3.

3. (a) Wane abu ne ya faru a zamanin Bulus? (b) Mene ne za mu iya koya daga yadda Jehobah ya bi da masu tawaye a zamanin Musa?

3 Shekaru 1,500 bayan haka, wani abu ya faru makamancin hakan a zamanin manzo Bulus. Wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun soma koyar da ƙarya, kuma duk da haka sun ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya. Mutumin da bai sani ba ba zai ga bambancin da ke tsakanin waɗannan ’yan ridda da kuma ’yan’uwa da ke ikilisiya ba. Amma koyarwar ridda da suke yi haɗari ne ga Kiristoci masu aminci. Waɗannan ’yan ridda da suke da tufafin tumaki sun “jirkitar da bangaskiyar waɗansu.” (2 Tim. 2:16-18) Jehobah ya lura da abin da suke yi kuwa? Hakika. Bulus ya san abin da Jehobah ya yi wa Korah da magoya bayansa masu tawaye, don haka, ya tabbata cewa Jehobah ya san da yanayin sosai. Don haka, bari mu tattauna wannan Nassin da kyau don mu ga darasin da za mu iya koya.

“NI UBANGIJI BA MAI-SĀKEWA BA NE”

4. Mene ne Bulus ya tabbata da shi, kuma ta yaya ya nuna wannan tabbacin a wasiƙarsa zuwa ga Timotawus?

4 Manzo Bulus ya tabbata cewa Jehobah zai iya sanin masu ibada ta munafurci da waɗanda suke Masa ibada da zuciya ɗaya. Bulus ya nuna wannan tabbacin a kalaman da Allah ya hure shi ya rubuta wa Timotawus. Bayan da ya ambata irin gurɓatarwa da ’yan ridda suke yi wa wasu a cikin ikilisiya, Bulus ya ce: “Amma tushe mai-tsayawa na Allah ya tabbata, da shi ke yana da wannan hatimi, Ubangiji ya san waɗanda ke nasa: da kuma, Dukan wanda ya ambaci sunan Ubangiji shi rabu da [“mugunta,” LMT].”—2 Tim. 2:18, 19.

5, 6. Mene ne muhimmancin kalaman Bulus na “tushe mai-tsayawa na Allah,” kuma ta yaya waɗannan kalaman suka ƙarfafa Timotawus?

5 Mene ne muhimmancin kalaman da Bulus ya yi amfani da su a wannan ayar? A wannan wurin ne kaɗai aka ambata “tushe mai-tsayawa na Allah” a cikin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da “tushe” wajen kwatanta abubuwa da yawa. Kuma hakan ya ƙunshi wasu abubuwa kamar su babban birnin Isra’ila ta dā, wato Urushalima. (Zab. 87:1, 2) Har ila, an kwatanta matsayin Yesu a cikar nufin Allah da tushe. (1 Kor. 3:11; 1 Bit. 2:6) Shin mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya yi magana game da “tushe mai-tsayawa na Allah”?

6 Bulus ya ambaci “tushe mai-tsayawa na Allah” sa’ad da yake kaulin abin da Musa ya faɗa game da Korah da magoya bayansa kamar yadda aka rubuta Littafin Lissafi 16:5. Da alama Bulus yana nuni ne ga abubuwan da suka faru a zamanin Musa don ya ƙarfafa Timotawus kuma ya tuna masa cewa Jehobah ya san masu tawaye kuma ya ɗauki matakin da ya dace. Jehobah zai iya hana ’yan ridda daga gurɓata ikilisiya. Korah bai iya canja nufin Allah ba, hakazalika, ’yan ridda da suke cikin ikilisiya ba za su iya canja nufin Allah ba. Bulus bai bayyana dalla-dalla abin da “tushe mai-tsayawa na Allah” yake nufi ba. Duk da haka, abin da Bulus ya gaya wa Timotawus ya ƙarfafa shi ya tabbata da Jehobah kuma ya dogara a gare shi.

7. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah zai yi adalci da kuma jin ƙai?

7 Ƙa’idodin Jehobah ba sa canjawa. Zabura 33:11 ta ce: “Shawarar Ubangiji ta tabbata har abada, tunanin zuciyarsa kuma har tsararaki duka.” Wasu nassosi sun nuna cewa mulkin Jehobah da ƙaunarsa ta aminci da adalcinsa da kuma jin ƙansa za su dawwama. (Fit. 15:18; Zab. 106:1; 112:9; 117:2) Malakai 3:6 ta ce: “Ni Ubangiji ba mai-sākewa ba ne.” Hakazalika, Yaƙub 1:17 ta ce Jehobah “sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.”

‘HATIMIN’ DA KE INGANTA BANGASKIYA GA JEHOBAH

8, 9. Wane darasi za mu iya koya daga “hatimi” da Bulus ya yi kwatanci da shi?

8 A dā, mutane sun saba yin rubutu a tushen gini. Ana wannan rubutun ne wataƙila don a san wanda ya gina ko kuma mai maigidan. Bulus ne marubucin Littafi Mai Tsarki na farko da ya yi amfani da wannan kwatancin.a Hatimin “Tushe mai-tsayawa na Allah,” da Bulus ya ambata a littafin 2 Timotawus 2:19 yana ɗauke da abubuwa biyu. Na ɗaya, “Ubangiji ya san waɗanda ke nasa.” Na biyu, “Dukan wanda ya ambaci sunan Ubangiji shi rabu da [“mugunta,” LMT].” Wannan furucin ya tuna mana da abin da muka karanta a Littafin Lissafi 16:5.—Karanta.

9 Wane darasi za mu koya daga “hatimi” da Bulus ya ambata a kwatancinsa? Ƙa’idodin Jehobah sun ƙunshi abubuwa biyu: (1) Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke da aminci a gareshi, da kuma (2) Jehobah yana tir da mugunta. Ta yaya wannan batun ya shafi koyarwar ’yan ridda a cikin ikilisiya?

10. Ta yaya abubuwan da ’yan ridda suka yi ya shafi masu aminci a zamanin Bulus?

10 Timotawus da sauran amintattun bayin Allah a lokacin sun damu ƙwarai da abubuwan da ’yan ridda suke yi a cikin ikilisiya. Wataƙila wasu Kiristoci ba su ga dalilin da ya sa aka ƙyale irin waɗannan mutanen su kasance a cikin ikilisiya ba. Wasu bayin Allah masu aminci ma sun damu ko Jehobah zai iya sanin bambancin da ke tsakanin waɗanda suke ibada da aminci da kuma ’yan ridda masu munafurci.—A. M. 20:29, 30.

11, 12. Ta yaya wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Timotawus ta ƙarfafa shi?

11 Wasiƙar Bulus ga Timotawus ya ƙarfafa bangaskiyarsa sosai. Ya tuna wa Timotawus yadda Jehobah ya nuna cewa Korah da magoya bayansa munafukai ne. Jehobah bai amince da su ba don haka ya halaka su, amma ya amince da Haruna. Hakazalika, ko da yake akwai waɗanda suka yi da’awa cewa su Kiristoci ne a zamanin Bulus, Jehobah zai bambanta waɗanda suke bauta masa da aminci kamar yadda ya yi a zamanin Musa.

12 Za a iya tabbata da Jehobah domin ba ya canjawa. Yana yin tir da mugunta kuma zai hukunta masu zunubi da suka ƙi tuba. An tuna wa Timotawus cewa ya kamata ya guji tasirin masu mugunta da suke da’awa su Kiristoci na gaskiya ne, domin “dukan wanda ya ambaci sunan Ubangiji” wajibi ne ya yi tir da mugunta.b

YIN IBADA DA ZUCIYA ƊAYA BA AIKIN BANZA BA NE

13. Wane tabbaci muke da shi?

13 Za mu iya koya darasi mai kyau daga kalaman da Allah ya hure Bulus ya rubuta. Da farko, muna samun ƙarfafa wajen fahimtar cewa Jehobah yana sane da masu masa ibada da aminci. Kuma wannan ba sanin shanu ba ne. Maimakon haka, Jehobah ya damu da waɗanda suke masa ibada da gaske. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Laba. 16:9) Saboda haka, muna da tabbaci cewa Jehobah ya san da ibadar da muke yi masa da “zuciya mai-tsabta.”—1 Tim. 1:5; 1 Kor. 15:58.

14. Wace irin ibada ce Jehobah ya tsana?

14 Jehobah yana tir da ibadar munafunci. Yana san abin da ke cikin zukatan mutane kuma yana sane da waɗanda zuciyarsu bai “kamalta gareshi” ba. Littafin Misalai 2:23 ya ce, “mashiririci abin ƙyama ne ga Ubangiji,” wato irin mutumin da yake da’awa cewa yana biyayya ga Allah amma yana yin zunubi a ɓoye. Ko da yake wanda yake shiririta zai iya ɓoye hakan na ɗan lokaci, amma Jehobah yana da iko sosai da kuma adalci saboda haka, “wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba.”—Mis. 28:13; karanta 1 Timotawus 5:24; Ibraniyawa 4:13.

15. Mene ne ya kamata mu guje masa, kuma me ya sa?

15 Yawancin bayin Allah suna ƙaunarsa da dukan zuciyarsu. Saboda haka, zai yi wuya mutum ya yi munafurci a ibadarsa ga Jehobah da gangan. Duk da haka, da yake hakan ya faru a zamanin Musa da kuma zamanin Kiristoci na farko, zai iya faruwa ma a yau. (2 Tim. 3:1, 5) Shin hakan yana nufin cewa za mu riƙa tuhumar ’yan’uwanmu ko kuwa mu riƙa yin shakkar ibadarsu ga Jehobah ne? A’a. Ba zai dace mu riƙa tuhumarsu ba gyara ba dalili ba. (Karanta Romawa 14:10-12; 1 Korintiyawa 13:7.) Ƙari ga haka, idan muna tuhumar ’yan’uwanmu a ikilisiya za mu iya ɓata dangantakarmu da Jehobah.

16. (a) Mene ne ya kamata mu yi don mu kawar da halin munafurci a ibadarmu ga Jehobah? (b) Waɗanne darussa za mu koya daga akwatin nan “Ku Gwada Kanku . . . Ku Yi wa Kanku Ƙwanƙwanto . . . ”?

16 Ya kamata kowane Kirista ya “auna nasa aiki.” (Gal. 6:4) Da yake mu ajizai ne, za mu iya yin ibada ga Jehobah a hanyar da ba ta dace ba cikin rashin sani. (Ibran. 3:12, 13) Shi ya sa ya kamata mu riƙa bincika dalilan da suka sa muke bauta wa Jehobah. Za mu iya tambayar kanmu: ‘Me ya sa nake bauta wa Jehobah? Ina bauta masa ne don ina ƙaunarsa kuma ina son ya zama Sarkina? Ina mai da hankali ga rayuwa mai kyau da zan more a Aljanna ne kawai?’ (R. Yoh. 4:11) Hakika, yi wa kanmu irin waɗannan tambayoyin zai taimaka mana mu kawar da munafurci a ibadarmu ga Jehobah.

AMINCI DA KE SA MU FARIN CIKI

17, 18. Me ya sa ya kamata mu yi wa Jehobah ibada da zuciya ɗaya?

17 Za mu sami albarka sosai idan muka ɗauki matakai don mu kawar da munafurci a ibadarmu ga Jehobah. Wani marubucin zabura ya ce: “Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba, wanda ba shi da algus cikin ruhunsa ba.” (Zab. 32:2) Hakika, waɗanda suka ɗauki matakan kawar da munafurci a ibadarsu ga Jehobah suna farin ciki yanzu kuma za su sami albarka sosai a nan gaba.

18 Ba da daɗewa ba, Jehobah zai fallasa mugayen mutanen da suka ƙi su canja halinsu ko kuma masu yin zunubi a ɓoye. Zai bambanta “tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Mal. 3:18) Kafin wannan lokacin muna farin cikin sanin cewa “idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci, kunnuwansa kuma suna buɗe ga jin roƙonsu.”—1 Bit. 3:12.

a Littafin Ru’ya ta Yohanna 21:14, da aka rubuta shekaru da yawa bayan wasiƙun Bulus ga Timotawus, ya ambaci “fandeshon [tussa] goma sha biyu” da ke ɗauke da sunayen manzanni goma sha biyu.

b Talifi na gaba zai nuna yadda za mu yi koyi da Jehobah a yin tir da mugunta.

“Ku Gwada Kanku . . . Ku Yi wa Kanku Ƙwanƙwanto . . .”

TA YAYA za mu bincika tunaninmu da abubuwan da ke cikin zuciyarmu? Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan shawarar: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.” (2 Kor. 13:5) Wataƙila akwai wasu ɓangarori na musamman a rayuwarmu da muke bukata mu riƙa bincikawa sosai don mu tabbata cewa babu wata alamar munafurci a ibadarmu ga Jehobah. Ka yi la’akari da waɗannan tambayoyin da ke gaba da za su iya taimaka mana wajen bincika kanmu:

  • Shin kalaman yabo da nake yi wa ’yan’uwa da kuma ƙaunata gare su yana fitowa ne daga zuciyata?—Zab. 12:2, 3; 1 Bit. 1:22.

  • Shin ina nuna karimci kuma ina ba da kyauta da zuciya ɗaya?—Mat. 6:2-4.

  • Ina nuna wa waɗanda ke cikin iyalina ƙauna da sanin yakamata a gida da kuma a waje?—Kol. 3:18-21.

  • Shin halina ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da nake koya wa mutane da ƙwazo?—Rom. 2:21-23.

Idan muka tarar cewa muna da wasu halaye da ba su dace ba, zai dace mu kawar da su kafin su zama mana jiki. Idan muka yi hakan, kamar manzo Bulus, za mu iya cewa tsakaninmu da Allah, “ba a taɓa iske mu muna yin ta daɗin baki ba, ku ma kun san haka, ko kuwa mayafi na ƙyashi.”—1 Tas. 2:5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba