Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 8/1 pp. 21-26
  • Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Aka Yi Mulkin Isra’ila ta Dā
  • “Kuna Son Matsayin Firist Kuma?”
  • Alƙalin Isra’ila Ya Sa Baki
  • Sanin Hanyar a Yau
  • Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Sandan Haruna Ya Yi Fure
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Ya San Ka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 8/1 pp. 21-26

Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah

“Ubangiji shi ne mai-mulkinmu, Ubangiji shi ne mai-bada shari’a, Ubangiji shi ne sarkinmu.”—ISHAYA 33:22.

1. Waɗanne abubuwa suka sa al’ummar Isra’ila ta dā ta bambanta da wasu al’ummai?

ASHEKARA ta 1513 K.Z., aka kafa al’ummar Isra’ila. A lokacin, ba ta da babban birni, ba ta da gari, kuma ba ta da sarki na zahiri. Talakawan al’ummar dā su bayi ne. Amma, wannan sabuwar al’umma ta bambanta a wata hanya. Jehovah Allah ne Mai Mulkinta, Mai Shari’arta, kuma Sarkinta marar ganuwa. (Fitowa 19:5, 6; Ishaya 33:22) Babu wata al’umma da take da wannan!

2. Wace tambaya ta taso game da tsari na Isra’ila, kuma me ya sa amsar take da muhimmanci a gare mu?

2 Tun da yake Jehovah, Allah ne mai tsari, kuma Allah mai salama, za mu yi zaton cewa duk al’ummar da shi yake mulkinta za ta kasance tana da tsari. (1 Korinthiyawa 14:33) Haka ya kasance da Isra’ila. Amma ta yaya Allah marar ganuwa zai shugabanci ƙungiyar da ake gani a duniya? Zai yi kyau mu bincika yadda Jehovah ya yi mulkin wannan al’umma ta dā, mu lura musamman da yadda sha’ani da ya yi da Isra’ila ya nuna muhimmancin miƙa kai da aminci ga ikon Allah.

Yadda Aka Yi Mulkin Isra’ila ta Dā

3. Wane shiri ne mai amfani Jehovah ya yi domin shugabancin mutanensa?

3 Ko da yake Jehovah ne Sarki marar ganuwa na Isra’ila, ya naɗa mutane masu aminci su zama wakilansa da ake gani. Da akwai sarakuna, galadima, da kuma dattawa da suka zama masu hukunci da alƙalai na mutanen. (Fitowa 18:25, 26; Kubawar Shari’a 1:15) Amma, ya kamata mu sani cewa idan ba tare da shugabancin Allah ba waɗannan mutane da suke da hakki za su yi kuskure kuma su yi ɓatar basira. Su ajizai ne, ba sa iya ganin zukatan ’yan’uwansu masu bauta. Har ila, alƙalai da suke tsoron Allah sun ba wa ’yan’uwa masu bi gargaɗi mai amfani daga Dokar Jehovah.—Kubawar Shari’a 19:15; Zabura 119:97-100.

4. Waɗanne halaye alƙalai masu aminci na Isra’ila suke lura don su guje wa, kuma me ya sa?

4 Amma, ana bukatar wani abu don zama alƙali fiye da fahimtar Doka kawai. Domin su ajizai ne, dattawan suna bukatar su magance munanan nufinsu—irinsu son kai, son zuciya, da kuma haɗama—da za su iya kawo cikas wajen hukunci. Musa ya gaya musu: “A cikin shari’a ba za ku yi tara, sai ku ji ta ƙaramin mutum tamkar ta babban mutum; ba za ku ji tsoron idon mutum ba; gama shari’a ta Allah ce.” Hakika, alƙalan Isra’ila suna shari’a a madadin Allah ne. Lallai gata ce mai girma!—Tafiyar tsutsa tamu ce; Kubawar Shari’a 1:16, 17.

5. Ban da tsarin alƙalai, waɗanne tanadodi kuma Jehovah ya yi domin ya kula da mutanensa?

5 Jehovah ya yi wasu tanadi don ya cika bukatun ruhaniya na mutanensa. Kafin ma su kai Ƙasar Alkawari, ya umurce su su gina mazauni, cibiyar bauta ta gaskiya. Ya kuma tsara firistoci su koyar da Dokar, su yi hadayun dabbobi, kuma su ƙona turare da safe da yamma. Allah ya naɗa Haruna, wan Musa, ya zama babban firist na farko na Isra’ila kuma ya naɗa ’ya’yan Haruna su taimaki ubansu.—Fitowa 28:1; Litafin Lissafi 3:10; 2 Labarbaru 13:10, 11.

6, 7. (a) Wace dangantaka ce take tsakanin firistoci da Lawiyawa da ba na firistoci ba? (b) Wane darasi muka koya cikin aiki dabam dabam da Lawiyawa suka yi? (Kolossiyawa 3:23)

6 Kula da bukatun ruhaniya na miliyoyin mutane, babban aiki ne, kuma firistocin ba su da yawa. Saboda haka, aka shirya wasu cikin ƙabilar Lawiyawa su taimaka musu. Jehovah ya gaya wa Musa: “Za ka sa Lawiyawa a hannun Haruna da ’ya’yansa; daga cikin ’ya’yan Isra’ila su ne an ba shi su tuttur.”—Litafin Lissafi 3:9, 39.

7 An tsara Lawiyawan da kyau. An rarraba su iyalai uku daidai—Gershonawa, Kohatawa, da kuma su Merari—kowanne da aikinsu. (Litafin Lissafi 3:14-17, 23-37) Ƙila wasu ayyukan ana musu ganin sun fi wasu muhimmanci amma ana bukatar dukansu. Aikin Kohatawa na Lawi ya bukaci su kasance kusa da tsarkakar sunduƙi na alkawari da kuma adana mazauni. Amma, kowanne Balawi, ko daga Kohatawa ne ko babu, suna da gata masu girma. (Litafin Lissafi 1:51, 53) Amma abin baƙin ciki wasu ba su da godiya game da gatarsu. Maimakon su miƙa kai da aminci ga ikon Allah, suka nuna rashin godiya suka shiga yin fahariya, da dogon buri, da kuma kishi. Balawi mai suna Kora haka ya yi.

“Kuna Son Matsayin Firist Kuma?”

8. (a) Wanene Kora? (b) Me ya sa wataƙila Kora ya fara ɗaukan firistoci bisa ra’ayin mutane?

8 Kora ba shi ne shugaban iyalin Lawi ba, kuma ba shi ne shugaban iyalin Kohatawa ba. (Litafin Lissafi 3:30, 32) Duk da haka, shi wani shugaba ne mai daraja a Isra’ila. Aikin Kora lallai ya sa ya shiga tarayya da Haruna da ’ya’yansa. (Litafin Lissafi 4:18, 19) Da yake yana ganin ajizancin waɗannan maza, mai yiwuwa Kora ya yi tunanin cewa: ‘Waɗannan firistoci ajizai ne, amma ana bukatar na yi musu biyayya! Ba da daɗewa ba Haruna ya yi ɗan maraƙin zinariya. Yin sujjada ga ɗan maraƙin ya sa mutanenmu sun faɗā cikin bautar gunki. Amma Haruna, ɗan’uwan Musa yana hidimar babban firist! Dubi halin son kai! ’Ya’yan Haruna, Nadab da Abihu kuma fa? Hakika, sun nuna rashin daraja gatarsu ƙwarai ta hidimar da ya sa Jehovah ya halaka su!’a (Fitowa 32:1-5; Leviticus 10:1, 2) Ko da menene tunanin Kora, a bayyane yake cewa ya fara ɗaukan tsarin firistoci bisa ra’ayin mutum. Hakan ya kai ga yi wa Musa da Haruna tawaye, a ƙarshe kuwa ga Jehovah.—1 Samu’ila 15:23; Yaƙub 1:14, 15.

9, 10. Wane zargi ne Kora da abokansa ’yan tawaye suka yi wa Musa, kuma me ya sa da ba su yi hakanan ba?

9 Domin shi shugaba ne, bai yi masa wuya ya tara wa kansa masu ra’ayi irin nasa ba. Shi, tare da Datan da Abiram, suka sami mutane 250—dukansu shugabannan taron ne. Tare suka zo wajen Musa da Haruna suka ce: “Dukan jama’a masu-tsarki ne, kowane ɗayansu, Ubangiji kuma yana tare da su; don menene fa ku ke ɗaukaka kanku gaba da taron jama’ar Ubangiji?”—Litafin Lissafi 16:1-3.

10 Domin abin da ya faru, da waɗannan ’yan tawayen ba su zargi ikon Musa ba. Ba da daɗewa ba Haruna da Maryamu suka nuna irin wannan hali. Har ma sun yi tunani irin na Kora! Daidai da abin da ke a Litafin Lissafi 12:1, 2, suka ce: “Ubangiji ya yi magana da Musa kaɗai ne? Ba ya yi magana kuma da mu ba?” Jehovah yana sauraronsu. Ya umurci Musa, da Haruna, da kuma Maryamu su je ƙofar tanti na taro domin ya nuna wanda ya zaɓa ya shugabanci jama’arsa. Sai kuma Jehovah ya ce filla-filla: “Ku ji maganata yanzu: idan da annabi a cikinku, ni Ubangiji zana bayyana kaina gareshi cikin ru’ya, in yi magana da shi cikin mafarki. Ba haka ni ke yi da bawana Musa ba: mai-aminci ne shi cikin dukan gidana.” Bayan wannan, Jehovah ya harbi Maryamu da kuturta na ɗan lokaci.—Litafin Lissafi 12:4-7, 10.

11. Yaya Musa ya bi da yanayi da ya shafi Kora?

11 Kora da waɗanda suke goyon bayansa lallai sun sani game da wannan aukuwan. Ba su da hujjar yin tawaye. Duk da haka Musa cikin haƙuri ya nemi ya sa su yi tunani. Ya aririce su su yi godiya ga gata da suke da ita, yana cewa: “Abu ƙanƙani ne a gareku, Allah na Isra’ila ya keɓe ku daga cikin jama’ar Isra’ila, domin ya kawo ku kusa da kansa?” A’a, ba ‘ƙanƙanin’ abu ba ne! Lawiyawan suna da abubuwa da yawa. Me suke nema kuma? Kalmomin Musa na gaba sun bayyana tunanin zuciyarsu: “Kuna son matsayin [firist] kuma?”b (Litafin Lissafi 12:3; 16:9, 10) To, me Jehovah ya yi game da wannan tawaye ga ikon Allah?

Alƙalin Isra’ila Ya Sa Baki

12. A kan menene ci gaba da dangantaka mai kyau na Isra’ila tare da Allah ya dangana?

12 Lokacin da Jehovah ya ba da Doka ga Isra’ila, ya gaya wa mutanen cewa idan sun yi biyayya, za su zama “al’umma mai-tsarki” kuma al’ummar za ta ci gaba da kasancewa da tsarki muddin sun amince da tsarin Jehovah. (Fitowa 19:5, 6) A wannan lokacin gaba gaɗi da kuma tawaye, lokaci ya yi da Alƙali da kuma Mai Ba da Doka na Isra’ila zai sa baki! Musa ya ce wa Kora: “Kai, da dukan jama’arka, da Haruna, ku bayyana a gaban Ubangiji: kowanne mutuminku shi ɗauki kaskon turare, a ɗibiya masa turare, kowanne kuma ya kawo kaskonsa na turare a gaban Ubangiji; watau kasko guda metan da hamsin ke nan: da kai, da Haruna kuma, kowa kaskon turarensa.”—Litafin Lissafi 16:16, 17.

13. (a) Me ya sa girman kai ne ga ’yan tawayen su ƙona turare a gaban Jehovah? (b) Yaya Jehovah ya yi da ’yan tawayen?

13 Daidai da Dokar Allah, firistoci ne kaɗai suke ƙone turare. Ra’ayin cewa Lawiyawa waɗanda ba firistoci ba su ƙona turare a gaban Jehovah da ya sa waɗannan ’yan tawayen su yi tunani sosai. (Fitowa 30:7; Litafin Lissafi 4:16) Wannan bai tunasar da Kora da masu goyon bayansa ba! Washegari ya “tara dukan jama’a a kansu [Musa da Haruna] zuwa ƙofar [tanti] na taruwa.” Labarin ya ce: “Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce, Ku keɓe kanku daga cikin jama’an nan, domin in halaka su farat ɗaya.” Amma Musa da Haruna suka yi roƙo cewa a ceci mutanen. Jehovah ya saurari roƙonsu. Kora da jama’arsa fa, “wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta cinye mutum metan da hamsin ɗin waɗanda suka ƙona turare.”—Litafin Lissafi 16:19-22, 35.c

14. Me ya sa Jehovah ya ɗauki mataki mai tsanani a kan taron Isra’ila?

14 Abin mamaki kuwa, Isra’ilawa da suka ga abin da Jehovah ya yi wa ’yan tawayen har ila ba su yi hankali ba. “Washegari dukan taron jama’ar ’ya’yan Isra’ila suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suka ce, Kun kashe jama’ar Ubangiji.” Isra’ilawan suna goyon bayan waɗannan ’yan tawaye! Daga bisani, haƙurin Jehovah ya kai ƙarshensa. Babu wani—ko Musa ko Haruna—da zai iya roƙo domin mutanen yanzu. Jehovah ya sa annoba ta auko a kan masu rashin biyayyan nan, “mutanen da suka mutu ta wurin annobar, mutum zambar goma sha huɗu ne da ɗari bakwai, banda waɗanda suka mutu a kan matsalar Kora.”—Litafin Lissafi 16:41-49.

15. (a) Domin waɗanne dalilai ya kamata da Isra’ilawa sun yi na’am da shugabancin Musa da Haruna babu musu? (b) Menene wannan labarin ya koya maka game da Jehovah?

15 Da mutanen nan ba su yi hasarar rayukansu ba haka kawai. Da dai sun yi tunani sosai a kan wannan batun. Da sun yi wa kansu waɗannan tambayoyi: ‘Su wa suka kasadar da ransu su tsaya a gaban Fir’auna? Su wa suka nace a ’yantar da Isra’ilawa? Waye aka gayyata ya hau zuwa Dutsen Horeb bayan ceton Isra’ilawa don ya yi magana da mala’ikan Allah fuska da fuska? Babu shakka cewa tarihin Musa da Haruna ya ba da tabbaci na amincinsu ga Jehovah da kuma ƙaunarsu ga mutanen. (Fitowa 10:28; 19:24; 24:12-15) Ba abin farin ciki ba ne wajen Jehovah ya kashe waɗannan ’yan tawaye. Amma, da ya zamana cewa mutanen sun nace ga tawayensu, ya ɗauki mataki mai tsanani. (Ezekiel 33:11) Dukan waɗannan suna da muhimmanci ƙwarai a gare mu yau. Me ya sa?

Sanin Hanyar a Yau

16. (a) Wane tabbaci ne Yahudawa na ƙarni na farko suke da shi cewa Yesu wakilin Jehovah ne? (b) Me ya sa Jehovah ya sake tsarin firistoci na Lawiyawa, kuma da me ya sake shi?

16 A yau, akwai sabuwar “al’umma” da Jehovah ne Alƙalinta marar ganuwa, Mai Ba da Dokarta, da kuma Sarkinta. (Matta 21:43) An kafa “al’ummar” a ƙarni na farko A.Z. A lokacin, an sake mazauni na zamanin Musa da kyakkyawar haikali a Urushalima, inda Lawiyawa har ila suke hidima. (Luka 1:5, 8, 9) Amma a shekara ta 29 A.Z., aka kafa wani sabon haikali, na ruhaniya wanda Yesu Kristi ne Babban Firist nasa. (Ibraniyawa 9:9, 11) Sai kuma batun iko na Allah ya sake aukowa. Waye Jehovah zai yi amfani da shi ya shugabanci wannan sabuwar “al’ummar”? Yesu ya tabbatar da kansa shi mai aminci ne ga Allah. Yana ƙaunar mutanensa. Ya kuma yi mu’ujizai masu girma. Amma, kamar kakanninsu masu taurin kai, yawancin Lawiyawan suka ƙi su amince da Yesu. (Matta 26:63-68; Ayukan Manzanni 4:5, 6, 18; 5:17) A ƙarshe, Jehovah ya sake tsarin firistoci na Lawiyawa da wani dabam—tsarin firistoci na sarauta. Wannan tsarin firistoci na sarauta ya ci gaba har wa yau.

17. (a) Wane rukuni ne ya zama tsarin firistoci na sarauta a yau? (b) Ta yaya Jehovah yake amfani da tsarin firistoci na sarauta?

17 Su wa suke cikin wannan tsarin firistoci na sarauta a yau? Manzo Bitrus ya amsa wannan tambayar a hurarriyar wasiƙarsa ta farko. Zuwa ga shafaffu waɗanda suke cikin jikin Kristi, Bitrus ya rubuta: “Amma ku zaɓaɓɓen iri ne, [tsarin firistoci], basarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.” (1 Bitrus 2:9) Daga waɗannan kalmomi a bayyane yake cewa, rukuninsu, mabiyan Yesu shafaffu su ne wannan “basarauci [tsarin firistoci],” da Bitrus ya kira “al’umma mai-tsarki.” Su ne hanyar da Jehovah yake amfani da ita ya koyar da mutanensa kuma ja-gorance su a ruhaniya.—Matta 24:45-47.

18. Wace nasaba take tsakanin dattawa da aka naɗa da kuma tsarin firistoci na sarauta?

18 Waɗanda suke wakilta tsarin firistoci na sarauta su ne dattawa da aka naɗa, da suke da hakki cikin ikilisiyoyin mutanen Jehovah a dukan duniya. Waɗannan mazan ya wajaba mu yi musu ladabi kuma mu ba su goyon baya da zuciya ɗaya, ko shafaffu ne ko babu. Me ya sa? Domin ta wurin ruhunsa mai tsarki, Jehovah ya naɗa dattawa su kasance a matsayinsu. (Ibraniyawa 13:7, 17) Yaya hakan zai kasance?

19. A wace hanya za a ce an naɗa dattawa da ruhu mai tsarki?

19 Waɗannan dattawa sun cika farilla da aka jera cikin Kalmar Allah, wadda ita ce ’yar ruhun Allah. (1 Timothawus 3:1-7; Titus 1:5-9) Domin haka ne za a ce an naɗa su ta wurin ruhu mai tsarki. (Ayukan Manzanni 20:28) Waɗannan dattawa, dole ne su fahimci Kalmar Allah sosai. Kamar Mafificin Alƙalin da ya naɗa su, dole ne dattawa su ƙi wani abin da yake kama da son zuciya cikin shari’a.—Kubawar Shari’a 10:17, 18.

20. Me ya sa za ka daraja dattawa masu aiki tuƙuru?

20 Maimakon mu zargi ikonsu, muna godiya ƙwarai ga dattawa masu aiki tuƙuru! Sau da yawa, yawan shekarunsu na hidima da aminci yana ƙarfafa dogararmu. Cikin aminci suna shirya kuma suna gabatar da taron ikilisiya, suna aikin wa’azin “bisharar mulkin” tare da mu, kuma suna ba da gargaɗi na Nassi lokacin da muke bukatar haka. (Matta 24:14; Ibraniyawa 10:23, 25; 1 Bitrus 5:2) Suna ziyararmu yayin da muke ciwo kuma suna yi mana jaje yayin da muke baƙin ciki. Cikin aminci kuma ban da son zuciya suna ba da goyon baya ga abubuwa na Mulkin. Ruhun Jehovah yana kansu; suna da amincewarsa.—Galatiyawa 5:22, 23.

21. Menene dole dattawa su kula da shi, kuma me ya sa?

21 Hakika, dattawan ba kamiltattu ba ne. Sun san kasawarsu, ba sa ƙoƙarin wahalar da garken, “gadōn Allah.” Maimakon haka, suna ɗaukan kansu ‘abokan aiki ne tare da ’yan’uwansu.’ (1 Bitrus 5:3; 2 Korinthiyawa 1:24) Dattawa masu tawali’u da suke aiki tuƙuru suna ƙaunar Jehovah, kuma sun sani cewa idan sun yi koyi da shi sosai, za su iya aiki da kyau domin amfanin ikilisiyar. Tunawa da wannan, kullum suna ƙoƙari su gina irin halaye na ibada na ƙauna, jinƙai, da kuma haƙuri.

22. Ta yaya sake bincika tarihin Kora ya ƙarfafa bangaskiyarka cikin ƙungiyar Jehovah da ake gani?

22 Abin farin ciki, Jehovah ne Sarkinmu marar ganuwa, Yesu Kristi kuma shi ne Babban Firist namu, waɗanda shafaffu ne a tsarin firistoci na sarauta kuma suke koya mana, Kiristoci dattawa kuma masu aminci suke yi mana gargaɗi! Ko da yake babu wata ƙungiya da mutane suke jagabanci da za ta kasance kamiltacciya, muna farin ciki muna iya bauta wa Allah tare da ’yan’uwa masu bi masu aminci, da suke farin ciki su miƙa kai ga ikon Allah!

[Hasiya]

a ’Ya’yan Haruna biyu maza, Eleazar da Ithamar, su masu kirki ne cikin hidimarsu ga Jehovah.—Leviticus 10:6.

b ’Yan goyon bayan Kora, Datan da Abiram, ’ya’yan Ruban ne. Domin haka, ba su yi hassadar tsarin firistoci ba. Batun nasu, sun ƙi shugabancin Musa ne kuma a lokacin bukatarsu su shiga Ƙasar Alkawarin ba ta cika ba.—Litafin Lissafi 16:12-14.

c A lokatan uban iyalai, kowanne shugaban iyali yana wakiltan matansa da yaransa a gaban Allah, har ma suna ba da hadayu a maimakonsu. (Farawa 8:20; 46:1; Ayuba 1:5) Amma dai, lokacin da aka kafa Dokar, Jehovah ya naɗa ’ya’ya maza na iyalin Haruna su zama firistoci da ta wurinsu za a yi hadayu. Hakika ’yan tawaye guda 250 ba su goyi bayan wannan tsarin ba.

Me Ka Koya?

• Waɗanne tanadi masu kyau Jehovah ya yi don ya kula da Isra’ilawa?

• Me ya sa Kora ba shi da hujjar yi wa Musa da Haruna tawaye?

• Wane darasi yake gare mu yadda Jehovah ya yi da ’yan tawayen?

• Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar tsarin Jehovah a yau?

[Hoto a shafi na 21]

Kana ɗaukan kowanne aiki cikin bautar Jehovah gata ne kuwa?

[Hoto a shafi na 22]

“Don menene fa ku ke ɗaukaka kanku gaba da taron jama’ar Ubangiji?”

[Hoto a shafi na 25]

Dattawa da aka naɗa suna wakiltan tsarin firistoci na sarauta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba