Bayin Jehobah Suna Yin “Nesa da Aikata Mugunta”
“Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yā yi nesa da aikata mugunta.”—2 TIM. 2:19, Littafi Mai Tsarki.
1. Mene ne yake da muhimmanci sosai a ibadarmu?
SHIN ka taɓa ganin sunan Jehobah a rubuce a wani babban gini ko kuma a kayan tarihi? Babu shakka, ka yi mamaki. Sunan Jehobah yana da muhimmanci a ibadarmu don mu Shaidun Jehobah ne. A faɗin duniya, babu mutanen da suke yawan amfani da sunan Jehobah kamar yadda muke yi. Duk da haka, mun san cewa gatan amsa sunan Allah yana tattare da hakki.
2. Wane hakki ne ke tattare da gatan da muke da shin a amsa sunan Allah?
2 Yin amfani da sunan Allah ba shi ne kawai zai sa Jehobah ya amince da mu ba. Wajibi ne mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa da suka shafi ɗabi’a. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce dole ne mutanen Jehobah su “rabu da mugunta.” (Zab. 34:14) Manzo Bulus ya ambata wannan ƙa’idar dalla-dalla sa’ad da ya rubuta cewa: “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yā yi nesa da aikata mugunta.” (Karanta 2 Timotawus 2:19, LMT.) A matsayin Shaidun Jehobah, an san mu ƙwarai da yin amfani da sunan Allah. Amma ta yaya za mu yi tir da mugunta?
KA “ƘAURACE WA” MUGUNTA
3, 4. Wane nassi ne ya kasance da wuyar fahimta ga masanan Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa?
3 A littafin 2 Timotawus 2:19, Bulus ya yi maganar “tushe mai-tsayawa na Allah.” Bayan haka, sai ya faɗi abubuwa biyu da wannan tushen yake ɗauke da su. Na farko, “Ubangiji ya san waɗanda ke nasa.” An yi ƙaulin wannan furucin daga Littafin Lissafi 16:5. (Ka duba talifi na baya.) Bayani na biyu, wato “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yā yi nesa da aikata mugunta” furuci ne da masanan Littafi Mai Tsarki sun yi wuyar fahimta. Me ya sa?
4 Kalmomin da Bulus ya yi amfani da su ya nuna cewa ya yi ƙaulin wani wuri daga Attaura ne. Amma babu kalamai a cikin Attaura da suka zo daidai da ƙaulin da Bulus ya yi. Saboda haka, mene ne manzon yake nufi sa’ad da ya ce: “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yā yi nesa da aikata mugunta”? Bulus ya ɗauko furucin da ya yi da farko daga Littafi Lissafi Sura 16 ne, inda aka ba da labarin tawayen da Korah ya yi. Shin furuci na biyun yana da alaƙa da abubuwan da suka faru a lokacin tawayen ne?
5-7. Mene ne ya faru a zamanin Musa da Bulus ya yi maganarsa a 2 Timotawus 2:19? (Ka duba hoton da ke farkon talifi.)
5 Littafi Mai Tsarki ya ce Dathan da Abiram ’ya’yan Eliab suna haɗa kai da Korah a matsayin masu ja-goran tawayen. (Lit. Lis. 16:1-5) Sun yi wa Musa rashin kunya kuma suka ƙi bin umurnin da Allah ya ba shi. Waɗannan ’yan tawayen sun ci gaba da kasancewa cikin mutanen Allah, kuma ta hakan, sun saka dangantakan amintattu cikin haɗari. Sa’ad da lokaci ya yi da Jehobah zai bambanta amintattunsa da masu tawayen, ya ba da umurni dalla-dalla.
6 Labarin ya ce: “Sai Ubangiji ya ce wa Musa, ‘Ka faɗa wa jama’a su tashi, su nisanci alfarwar Korah, da ta Datan, da ta Abiram. Musa kuwa ya tashi ya tafi wurin Datan, da Abiram. Dattawan Isra’ilawa suka bi Musa. Sai ya ce wa jama’a, ‘Ina roƙonku, ku ƙaurace wa alfarwan waɗannan mugayen mutanen, kada ku taɓa kowane abu da ke nasu, domin kada a shafe ku saboda zunubansu.’ Sai jama’a suka tashi daga inda Korah, da Datan, da Abiram suke zama.” (Lit. Lis. 16:23-27, LMT) Jehobah ya halaka dukan waɗanda suka yi tawaye. Amma ya kāre amintattun bayinsa, wato, waɗanda suka ƙaurace kuma ta hakan suka nuna cewa sun yi tir da mugunta.
7 Jehobah ya san abin da ke cikin zuciyar mutum! Ya san bayinsa da ke da aminci. Duk da haka, wajibi ne bayinsa masu aminci su ɗauki mataki ta wajen fita sha’anin masu mugunta. Zai iya yiwuwa cewa Bulus yana magana game da labarin da ke Littafin Lissafi 16:5, 23-27, sa’ad da ya ce: “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yā yi nesa da aikata mugunta.” Saboda haka, za mu iya ce wannan furuci yana da alaƙa da furucin farko da manzo Bulus ya ambata sa’ad da ya ce: “Ubangiji ya san waɗanda ke nasa.”—2 Tim. 2:19.
‘KA ƘI BINCIKE NA WAUTA DA NA JAHILCI’
8. Me ya sa amsa suna Jehobah ko kuma kasancewa a cikin ikilisiyar Kirista kaɗai bai isa ba?
8 Bulus ya ambaci abin da ya faru a zamanin Musa don ya ƙarfafa Timotawus ya ɗauki mataki nan da nan don ya kāre dangantakarsa da Jehobah. Kamar yadda amsa sunan Jehobah kaɗai a zamanin Musa bai isa ba, kasancewa a cikin ikilisiya kaɗai bai isa ba. Wajibi ne amintattun bayin Allah su yi tir da mugunta. Shin mene ne hakan yake nufi ga Timotawus? Kuma waɗanne darussa ne bayin Jehobah za su koya daga wannan shawarar Littafi Mai Tsarki?
9. Ta yaya ‘bincike na wauta da na jahilci’ yake shafan ’yan’uwa a ikilisiya?
9 Kalmar Allah ta ba da takamaiman shawara game da irin mugunta da ya kamata Kirista ya yi tir da shi. Alal misali, Bulus ya gaya wa Timotawus kada ya “yi muhawwara a kan kalmomi” kuma ya “guje ma zantattukan banza.” (Karanta 2 Timotawus 2:14, 16, 23.) Me ya sa ya yi wannan maganar? Domin wasu cikin ikilisiyar suna koyarwar ridda. Wasu suna yaɗa koyarwa da yake jawo saɓani da kuma gardama. Ko da yake wasu koyarwa da suke yaɗawa ba su saɓa wa Littafi Mai Tsarki kai tsaye ba, amma suna raba kan ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Shi ya sa Bulus ya ƙarfafa Timotawus ya ‘ƙi bincike na wauta da na jahilci.’
10. Wane mataki ne ya kamata mu ɗauka sa’ad da muka gamu da koyarwar ridda?
10 A yau, mutanen Jehobah ba sa fuskantar ridda a cikin ikilisiya a ko yaushe. Amma ya kamata a duk lokacin da muka gamu da ra’ayoyin da suka saɓa koyarwar Littafi Mai Tsarki, wajibi ne mu yi tir da su ba tare da ɓata lokaci ba ko da daga ina ne waɗannan ra’ayoyin suka fito. Ba zai dace mu yi gardama da ’yan ridda ba, ko da mun haɗu da su ido da ido ko ta intane ko kuma ta wata hanya dabam. Idan muka yi muhawwara da su, muna rashin bayayya ga Allah ne ko da muna so mu taimaka wa mutumin ne. A maimakon haka, ya kamata mu guji ridda ko kuma mu tir da ita gaba ɗaya da yake mu bayin Jehobah ne.
11. Mene ne zai iya haifar da ‘bincike na wauta,’ kuma ta yaya dattawa za su kafa misali mai kyau?
11 Ban da koyarwar ridda, akwai wasu abubuwa da za su iya hana ikilisiya ta kasance da salama. Alal misali, bambancin ra’ayi game da nishaɗi zai iya haifar da ‘bincike na wauta da na jahilci.’ Amma, idan wani yana ɗaukaka nishaɗin da ya saɓa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki fa? Bai kamata dattawa su yi shiru don suna gudun gardama ba. (Zab. 11:5; Afis. 5:3-5) Duk da haka, dattawa ba sa ɗaukaka ra’ayinsu. A maimakon haka, sun bin umurnin Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, . . . ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.”—1 Bit. 5:2, 3; karanta 2 Korintiyawa 1:24.
12, 13. (a) Ta yaya Shaidun Jehobah suke sanin irin nishaɗi da ya kamata su yi, kuma waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne suke bi? (b) Ta yaya ƙa’idodin da aka tattauna a sakin layi na 12 suka shafi ɓangarori dabam-dabam na rayuwa?
12 Ƙungiyar Jehobah ba ta bincika finafinai da wasannin kwamfuta da littattafai da waƙoƙi don zaɓan waɗanda bai kamata mu yi amfani da su ba. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce kowa ya horar da lamirinsa don sanin bambancin “nagarta da mugunta.” (Ibran. 5:14) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodi da za su taimaka mana mu zaɓi nishaɗi mai kyau. Burinmu shi ne mu riƙa yin “abin da ke na yarda ga Ubangiji.” (Afis. 5:10) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce shugabannin iyali suna da ikon tafiyar da al’amuran iyalinsu, saboda haka, za su iya yanke shawara kada a yi wasu irin nishaɗi a gidajensu.a—1 Kor. 11:3; Afis. 6:1-4.
13 Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da aka ambata a baya za su taimaka mana mu a dukan ɓangarorin rayuwa. Bambancin ra’ayi game da kula da lafiya da abinci da kuma wasu abubuwa za su iya jawo gardama. Bai kamata a yi gardama ba idan batun bai saɓa wa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba. Hakika, “bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa.”—2 Tim. 2:24.
KA GUJI MUGUN TARAYYA!
14. Wane kwatanci ne Bulus ya yi amfani da shi don ya nanata amfanin ƙin mugun tarayya?
14 A wace hanya ce kuma waɗanda suke ‘ambata sunan Ubangiji suke rabuwa da rashin adalci’? Ta wajen ƙin yin tarayya da mutanen da suke rashin adalci. Ta yaya Bulus ya kwatanta hakan? Bayan ya ambata “tushe mai-tsayawa na Allah,” ya yi magana game da wani “babban gida.” A cikin wannan gidan, akwai “kaya, ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma na itace da na ƙasa; waɗansu zuwa daraja, waɗansu kuwa ƙanƙanci.” (2 Tim. 2:20, 21) Bayan haka, Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi tir da kayan da ba su da daraja.
15, 16. Wane darasi ne za mu iya koya daga kwatancin “babban gida”?
15 Mene ne ma’anar kwatancin Bulus? Za a iya kwatanta “babban gidan” da ikilisiyar Kirista. Za a kuma iya kwatanta ‘kayan’ da ke gidan da kowane mutum a cikin ikilisiya. Alal misali, idan muna da tukunya mai datti a cikin gida zai iya yi mana lahani. Idan hakan ya faru, wajibi ne mai gidan ya ware shi daga sauran tukwane masu tsabta.
16 Hakazalika, ya kamata bayin Jehobah a yau da suke ƙoƙartawa su kasance da tsabta su guji yin tarayya da mutane a cikin ikilisiya da ba sa son bin ƙa’idodin Jehobah. (Karanta 1 Korintiyawa 15:33.) Idan muna so mu guji mugun tarayya a cikin ikilisiya, wajibi ne mu ƙi yin tarayya da mutanen da ba sa cikin ikilisiya ma. Hakan yana da muhimmanci domin mutane da yawa da ba sa cikin ikilisiya masu-son kuɗi ne da ‘marasa-bin iyaye, marasa-tsarki, masu-tsegumi, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, mafiya son annishuwa da Allah’!—2 Tim. 3:1-5.
JEHOBAH ZAI ALBARKACI MATAKIN DA MUKA ƊAUKA
17. Ta yaya Isra’ilawa masu aminci suka yi tir da mugunta?
17 Sa’ad da Jehobah ya ba da umurni cewa a “tashi daga wajen tent na Korah, da Dathan, da Abiram,” Isra’ilawa masu aminci sun yi hakan da gaggawa. (Lit. Lis. 16:24, 27) Ba su ɓata lokaci wajen janyewa daga waɗannan ’yan tawaye ba. Sun ‘tashi daga . . . ko’ina.’ Isra’ilawa masu aminci sun kasance a shirye su yi biyayya da dukan zuciyarsu. Sun suna sarai cewa sun goyi bayan Jehobah amma sun yi tir da mugunta. Wane darasi za mu iya koya daga wannan labarin?
18. Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce wa Timotawus ya “guje wa sha’awoyin ƙuruciya”?
18 Muna daraja dangantakarmu da Jehobah sosai. Wajibi ne mu ɗauki mataki nan da nan don mu kāre ta. Abin da Bulus yake magana a kai kenan sa’ad da ya ce wa Timotawus ya ‘guje wa sha’awoyin ƙuruciya.’ (2 Tim. 2:22) A lokacin Timotawus ya riga ya girma, wataƙila ya yi wa shekara 30 baya. Duk da haka, mutanen da suka yi girma za su iya kasance da “sha’awoyin ƙuruciya.” Sa’ad da Timotawus ya fuskanci waɗannan sha’awoyin, ya “guje” su, wato Timotawus ya “rabu da rashin adalci” ke nan. Yesu ya yi irin wannan maganar sa’ad da ya ce: “In kuwa idonka na sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar.” (Mat. 18:9, LMT) Wajibi ne waɗanda suke so su bi wannan shawarar su kāre dangantakarsu da Allah kuma su ɗauki mataki ba tare da ɓata lokaci ba.
19. Ta yaya wasu suka kāre dangantakarsu da Jehobah?
19 Ta yaya wasu Kiristoci suke kāre dangantakarsu da Jehobah? Wasu mutane da suke yin maye da giya a dā sun tsai da shawara cewa ba za su sake sha kuma ba. Wasu kuma da suke fama da wasu irin sha’awoyi sun guji kowane irin nishaɗin da zai ta da sha’awarsu. (Zab. 101:3) Alal misali, kafin wani mutum ya zama Mashaidi, yana jin daɗin zuwa fati da ’yan iska suke cāshewa. Amma bayan ya koyi gaskiya, sai ya yanke shawara cewa ba zai yi rawa ba sam-sam, ko da Shaidu ne suke liyafa. Me ya sa? Don kada wannan muguwar sha’awarsa ta dā ta taso. Ko da yake hakan ba ya nufin cewa dukan Kiristoci suna bukatar su guji shan giya ko yin rawa ko kuma wasu abubuwa da ba a haramta ba. Amma, ya kamata dukanmu mu yi hankali kuma mu kāre dangantakarmu da Jehobah.
20. Wane abin ban ƙarfafa ne muke da shi ko da yake ba shi da sauƙi mu “yi nesa da aikata mugunta”?
20 Kiran mu Shaidun Jehobah babban gata ne. Saboda haka, wajibi ne mu “yi nesa da aikata mugunta” kuma mu “rabu da mugunta.” (Zab. 34:14) Yin hakan ba shi da sauƙi sosai. Amma abin ƙarfafa ne sosai sanin cewa Jehobah zai ci gaba da yin ƙaunar “waɗanda ke nasa” kuma suke bin ƙa’idodinsa.—2 Tim. 2:19; karanta 2 Labarbaru 16:9a.
a Ka duba wannan talifin dandalin jw.org/ha “Shin Kun Haramta Kallon Wasu Fina-Finai ko Karanta Wasu Littattafai ko Kuma Saurarar Wasu Wakoki Ne?” a ƙarƙashin GAME DA MU > TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI.