Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 5/15 pp. 3-5
  • ‘Abincina Shi Ne In Yi Nufin Allah’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Abincina Shi Ne In Yi Nufin Allah’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU JE KU YI ALMAJIRAI
  • KA YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI
  • KA KASANCE DA RA’AYI MAI KYAU
  • Ka Yi Farin Ciki A Aikin Almajirantarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Taimaka wa Mutane Su Zama Almajiran Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 5/15 pp. 3-5

‘Abincina Shi ne In Yi Nufin Allah’

Me ke sa ka farin ciki sosai? Shin aure ne ko kasancewa da iyali ko kuma yin abokai? Wataƙila kana jin daɗin cin abinci tare da masoyanka. Tun da yake kai bawan Allah ne, abin da ya fi maka muhimmanci shi ne yin nufin Allah da karatun Kalmarsa da kuma shelar bishara, ko ba haka ba?

Sarki Dauda ya rera waƙar yabo ga Mahalicci cewa: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” (Zab. 40:8) Duk da matsalolin da ya fuskanta, Dauda ya ji daɗin yin nufin Allah. Hakika ban da Dauda, akwai bayin Allah da yawa da suka ji daɗin bauta wa Allah na gaskiya.

Manzo Bulus ya yi ƙaulin Zabura 40:8 a lokacin da yake magana game da Almasihu ko kuma Kristi. Ya ce: “Domin wannan sa’anda [Yesu] yana shigowa cikin duniya, ya ce, Da hadaya da baiko ba ka so ba, amma jiki ka shirya mani; Hadaya tuli na ƙonawa da na zunubi ba ka ji daɗinsu ba: Sa’annan na ce, Ga ni, na zo (cikin littafi an rubuta a kaina) garin in aika nufinka, Ya Allah.”—Ibran. 10:5-7.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya ji daɗin kallon halittun Allah da kasancewa da abokai da kuma cin abinci tare da wasu. (Mat. 6:26-29; Yoh. 2:1, 2; 12:1, 2) Amma abin da ya fi masa muhimmanci da kuma sa shi farin ciki shi ne yin nufin Ubansa wanda ke cikin sama. Shi ya sa Yesu ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yoh. 4:34; 6:38) Misalin Yesu ya taimaki almajiransa su san abin da yake kawo farin ciki sosai. Saboda haka, sun yi shelar bisharar Mulkin da farin ciki da kuma ƙwazo.—Luk 10:1, 8, 9, 17.

KU JE KU YI ALMAJIRAI

Yesu ya umurci almajiransa cewa: ‘Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.’ (Mat. 28:19, 20) Bin wannan umurnin ya ƙunshi yin wa’azi ga mutane a duk inda za a iya samunsu da komawa a ziyarce waɗanda suka karɓi saƙonmu da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Yin wannan aikin yana kawo farin ciki sosai.

Ƙauna ce take motsa mu mu ci gaba da yin wa’azi ko da ba a sauraronmu

Ko da mutane sun so saƙonmu ko sun ƙi, wajibi ne mu kasance da ra’ayi mai kyau idan muna so mu yi hidimarmu da farin ciki. Me ya sa muke ci gaba da yin wa’azi duk da hamayya da ake mana? Domin mun fahimci cewa ta wajen yin shelar bishara da kuma yin almajirai, muna nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma maƙwabta. Ban da haka ma, ranmu da kuma na maƙwabtanmu suna cikin haɗari. (Ezek. 3:17-21; 1 Tim. 4:16) Yanzu za mu yi la’akari da abubuwan da suka taimaka ma wasu ’yan’uwanmu su ci gaba da kasancewa da ƙwazo duk da matsalolin da suke fuskanta a yankunan da suke wa’azi.

KA YI AMFANI DA KOWANE ZARAFI

Yin amfani da tambayoyi masu kyau a wa’azi yana kawo sakamako mai kyau. Wata rana, ’Yar’uwa Amalia ta ga wani mutum a mashaƙata yana karanta jarida. Sai ta je wajen shi ta tambaye shi ko ya karanta wani albishiri a cikin jaridar. Sa’ad da mutumin ya ce a’a, sai Amalia ta ce, “Na kawo maka albishiri game da Mulkin Allah.” Hakan ya sa mutumin ya so ya ji wannan saƙon kuma daga baya ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. A taƙaice dai, Amalia ta soma nazari da mutane uku a wajen.

Janice wata ce da ta yi wa’azi a wurin aikinta. Sa’ad da wani mai gadi da wani abokin aikinta suka so wani talifi a cikin mujallar Hasumiyar Tsaro, sai ta ci gaba da ba su mujallun a kai a kai. Wani abokin aikinta ma ya ji daɗin wasu talifofin da ke cikin Hasumiyar Tsaro da Awake!, kuma shi ma ya soma karɓan mujallunmu a kai a kai. Har ila, wani abokin aikinta ma ya so mujallunmu kuma ya ce a riƙa ba shi kowace fitowa. Janice ta ce: “Wannan albarka ce sosai daga Jehobah!” A kwana a tashi, ta sami mutane 11 da suke karɓan kowace fitowar mujallunmu.

KA KASANCE DA RA’AYI MAI KYAU

Wani mai kula mai ziyara ya ce sa’ad da masu shela suna wa’azi gida-gida, kada su kammala tattaunawarsu da magidanta ta wajen gaya musu cewa za mu dawo wata rana. A maimakon haka, za su iya tambayar maigidan: “Za ka so in nuna maka yadda ake nazarin Littafi Mai Tsarki?” ko kuma, “Wace rana ce za ka so in dawo don mu ci gaba da tattaunawarmu kuma a wane lokaci?” Mai kula mai ziyarar ya ce ta wajen bin wannan tsarin, ’yan’uwa a wata ikilisiya da ya je hidima sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki guda 44 a cikin mako ɗaya.

Idan muka koma ziyara nan da nan ko da bayan ’yan kwanaki ne, hakan yana da kyau sosai. Me ya sa? Domin hakan yana nuna cewa muna son taimaka wa masu zuciyar kirki su fahimci Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da aka tambayi wata mata dalilin da ya sa ta amince Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, ta ce: “Na yarda su soma nazari da ni don sun nuna cewa suna ƙaunata ƙwarai.”

Za ka iya tambayar maigidan, “Za ka so in nuna maka yadda ake nazarin Littafi Mai Tsarki?”

Wata ’yar’uwa mai suna Madaí ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 15. Ƙari ga haka, ta ce wasu masu shela su riƙa yin nazari da 5 cikin waɗannan ɗaliban. Hakan ya faru ne jim kaɗan bayan ta halarci Makarantar Hidima ta Majagaba. Wasu daga cikin ɗalibanta sun soma halartan taro a kai a kai. Me ya taimaka wa Madaí ta soma nazari da yawa haka? An koya musu a makarantar cewa yana da muhimmanci su ci gaba da koma inda suka yi wa’azi har sai sun sami waɗanda suka ji daɗin wa’azinsu tun farko. Wata Mashaidiya da ta taimaka wa mutane da yawa su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta ce: “Na koya cewa koma ziyara a kai a kai wajen mutane yana da muhimmanci idan muna so mu taimaka musu su san Jehobah.”

Koma ziyara nan da nan zai nuna cewa muna ƙaunar mutanen da suke so su fahimci Littafi Mai Tsarki

Komawa don mu ziyarci mutane da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su yana bukatar ƙwazo sosai. Amma yin hakan ƙwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Idan muka yi ƙwazo a yin wa’azin Mulkin Allah, za mu iya taimaka wa mutane su zo “ga sanin gaskiya” da zai iya sa su sami ceto. (1 Tim. 2:3, 4) Mu ma za mu yi farin ciki sosai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba