Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 5/15 pp. 6-10
  • Yaya Ya Kamata Mu Ba da “Amsa” ga Kowane Mutum?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaya Ya Kamata Mu Ba da “Amsa” ga Kowane Mutum?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI TAMBAYOYI DON KA SAN ABIN DA KE ZUCIYAR MASU SAURARON KA
  • KA BAYYANA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
  • KA YI AMFANI DA KWATANCI DON A FAHIMCI BATUN SOSAI
  • KA KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE
  • Ka Yi Koyi Da Babban Malami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Aikin Da Aka Ba Ka Na Mai-bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Yi Koyi Da Babban Malami Mai Almajirantarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “Ba Ya Faɗa Musu Kome Ba Sai Game Da Misali”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 5/15 pp. 6-10

Yaya Ya Kamata Mu Ba da “Amsa” ga Kowane Mutum?

“Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, . . . domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”—KOL. 4:6.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa ya dace mu yi tambayoyi cikin ladabi don sanin abin da ke zuciyar masu sauraronmu?

  • Mene ne zai iya taimaka mana mu bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da kyau?

  • Ta yaya za mu yi amfani da kwatanci da kyau sa’ad da muke wa’azi?

1, 2. (a) Ka ba da misali da yake nuna muhimmancin yin tambayoyin da suka dace. (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Me ya sa bai kamata mu ji tsoron tattauna batutuwa masu wuya ba?

AKWAI wata rana da wata ’yar’uwa take tattaunawa da maigidanta wanda ba mashaidi ba ne. A dā yana zuwa coci kuma ya ce ya gaskata da koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya. Da ta lura cewa bai fahimci abin da Allah-uku-cikin-ɗaya yake nufi ba, sai ta tambaye shi cikin ladabi cewa “Ka gaskata cewa Allah Allah ne, ruhu mai tsarki Allah ne, Yesu Allah ne, duk da haka, waɗannan ba Alloli Uku ba amma Allah ɗaya ne?” Abin ya ba wa maigidan mamaki kuma ya ce: “A’a, ban gaskata da haka ba!” Hakan ya sa suka yi tattaunawa mai daɗi game da ko wane ne Allah.

2 Wannan labarin ya nuna cewa yin tambayoyi da suka dace kuma cikin basira yana da muhimmanci. Ƙari ga haka, ya nuna cewa bai kamata mu riƙa tsoron tattaunawa da mutane game da batutuwa masu wuya kamar Allah-uku-cikin-ɗaya da wutar jahannama ko kuma wanzuwar Mahalicci ba. Idan muka dogara ga Jehobah da kuma koyarwarsa, za mu iya ba wa mutane amsa mai ƙayatarwa, wato amsar da za ta iya ratsa zuciyar masu sauraronmu. (Kol. 4:6) Bari mu tattauna abin da ’yan’uwa da suka iya koyarwa suke yi sa’ad da suke tattauna waɗannan batutuwan. Za mu tattauna yadda za mu (1) yi tambayoyi don sanin abin da ke zuciyar wanda muke tattaunawa da shi, (2) bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun da kuma (3) yi amfani da kwatanci don a fahimci batun da kyau.

KA YI TAMBAYOYI DON KA SAN ABIN DA KE ZUCIYAR MASU SAURARON KA

3, 4. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tambayoyi don mu san abin da mutum ya gaskata da shi? Ka ba da misali.

3 Tambayoyi za su iya taimaka mana mu san abin da wani ya yi imani da shi. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Misalai 18:13 ta ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gareshi da kunya.” Hakika, kafin mu soma tattaunawa a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game wani batu, zai dace mu san abin da mai sauraronmu ya gaskata. In ba mu yi hakan ba, za mu ɓata lokaci muna ƙaryata wani batu, alhali mutumin bai yi imani da shi ba sam.—1 Kor. 9:26.

4 A ce muna tattauna batun jahannama da wani. Ba kowa ba ne ya gaskata cewa jahannama wuri ne da ake azabtar da mutane cikin wuta ba. Wasu sun gaskata cewa yanayi ne na rashin dangantaka da Allah. Saboda haka, za mu iya yin wannan tambayar: “Tun da mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da jahannama, mene ne ra’ayinka?” Bayan mun saurari amsarsa, za mu taimaka masa ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun.

5. Ta yaya tambayoyi za su sa mu san dalilin da ya sa maigida ya gaskata da wani batu?

5 Yin tambaya cikin ladabi zai iya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa mutumin ya gaskata da wani batu. Alal misali, idan muka haɗu da wani da ya ce bai yi imani da Allah ba fa? Zai iya zama da sauƙi mu kammala cewa mutumin bai gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa ba. (Zab. 10:4) Amma akwai waɗanda ba su gaskata da Allah ba don wahalar da suka sha ko kuma suka gani. Ba su yarda cewa Mahalicci mai ƙauna zai bar mutane su sha wahala ba. Saboda haka, idan mutumin bai amince da wanzuwar Allah ba, za mu iya yin wannan tambayar, “Ra’ayinka ke nan tun asali?” Idan mutumin ya ce a’a, za mu iya tambayarsa dalilin da ya sa yake shakka cewa Allah bai wanzu ba. Amsarsa za ta taimaka mana mu san hanyar da ta fi dacewa mu taimaka masa.—Karanta Misalai 20:5.

6. Mene ne ya kamata mu yi bayan mun yi wata tambaya?

6 Bayan mun yi tambaya, muna bukata mu saurari amsar da mutumin zai bayar kuma mu yi la’akari da yanayinsa. Alal misali, saboda wani hatsari, wani zai iya cewa bai gaskata cewa Allah ya wanzu ba, ya kamata mu tausaya masa kuma mu tabbatar masa cewa yin tunani a kan dalilin da ya sa ake wahala ba laifi ba ne. Bayan haka, za mu iya bayyana masa dalilan da suka sa mun gaskata cewa Allah ya wanzu. (Hab. 1:2, 3) Idan muka bi da shi cikin haƙuri da ƙauna, hakan zai iya sa shi ya so ƙarin bayani.a

KA BAYYANA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

7. Ƙwarewarmu a wa’azi ya dangana ga yin me?

7 Yanzu, bari mu tattauna yadda za mu bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Littafi Mai Tsarki shi ne ainihin littafin da muke amfani da shi sa’ad da muke wa’azi. Yana taimaka mana mu kasance ƙwararru kuma ‘shiryayyu sarai domin kowane managarcin aiki.’ (2 Tim. 3:16, 17) Ƙwarewarmu a wa’azi bai dangana ga karanta nassosi da yawa ba, a maimakon haka, ya dangana ne ga bayyana waɗanda muka karanta da kyau. (Karanta Ayyukan Manzanni 17:2, 3.) Misalai uku da suke gaba za su taimaka mana mu fahimci hakan.

8, 9. (a) Wace hanya ɗaya ce za mu iya tattaunawa da wanda ya gaskata cewa matsayin Yesu ɗaya ne da Allah? (b) Ta yaya ka taɓa tattaunawa da mutane game da wannan batun?

8 Yanayi na 1: Sa’ad da muke wa’azi, mun haɗu da wani da ya gaskata cewa matsayin Yesu da Allah ɗaya ne. Waɗanne nassosi ne za mu iya amfani da su wajen tattauna wannan batun? Za mu iya gaya wa mutumin ya karanta Yohanna 6:38, inda Yesu ya ce: “Na sauko daga sama, ba domin in yi nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.” Bayan ya karanta, za mu iya tambayarsa: “Idan Yesu Allah ne, wane ne ya aiko shi daga sama? Wanda ya aiko shi ya fi shi matsayi ne? A bayyane yake cewa wanda ya aiki wani ya fi wanda ya aika matsayi, ko ba haka ba?”

9 Ƙari ga haka, za mu iya karanta Filibiyawa 2:9, inda manzo Bulus ya kwatanta abin da Allah ya yi bayan Yesu ya mutu kuma ya tashi daga matattu. Ayar ta ce: “Allah kuma ya ba shi mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna.” Don mu taimaka wa mutumin ya yi tunani a kan wannan ayar, za mu iya yin tambayar nan: “Idan matsayin Yesu ɗaya ne da Allah kafin ya mutu kuma ayar nan ta ce Allah ya ɗaukaka Yesu fiye da yadda yake a dā, hakan ba zai nuna cewa matsayin Yesu a yanzu ya fi na Allah ba? Amma, shin akwai wanda ya fi Allah matsayi kuwa?” Irin wannan muhawwarar za ta taimaka wa mutane masu zukatan kirki su ƙara bincika batun.—A. M. 17:11.

10. (a) Ta yaya za mu iya tattaunawa da wanda ya gaskata da wutar jahannama? (b) Ta yaya ka taɓa taimaka wa mutane su yi tunani a kan wannan batun?

10 Yanayi na 2: Idan ka haɗu da wanda ya gaskata cewa Allah zai hukunta miyagu a cikin wutar jahannama. Wataƙila ya gaskata da jahannama ne don yana so a hukunta miyagu saboda muguntarsu. Ta yaya za mu tattauna da mutum da yake da irin wannan ra’ayin? Da farko, za mu iya tabbatar masa cewa za a hukunta miyagu. (2 Tas. 1:9) Bayan haka, za mu iya ce masa ya karanta Farawa 2:16, 17, inda aka nuna cewa hukuncin zunubi mutuwa ne. Za mu iya bayyana cewa dukan ’yan Adam sun gāji zunubi sanadin zunubin Adamu. (Rom. 5:12) Amma kuma za mu iya ambata cewa Allah bai ce zai halaka mutane a jahannama ba. Bayan haka, sai mu karanta Farawa 3:19 inda Allah ya gaya wa Adamu cewa zai koma turɓaya kuma wannan shi ne hukuncin zunubinsa kuma mu tambaye shi, “Shin zai dace Allah ya gaya wa Adamu cewa zai koma turɓaya, idan a wutar jahannama ne za a hukunta shi?” Irin wannan tambayar za ta sa mutumin ya yi tunani a kan batun idan shi mai hankali ne.

11. (a) Wace hanya ɗaya ce za mu iya tattaunawa da wanda ya gaskata cewa dukan adilai za su je sama? (b) Ta yaya ka taɓa tattaunawa da mutane game da wannan batun?

11 Yanayi na 3: Sa’ad da muke wa’azi, mun haɗu da wanda ya gaskata cewa dukan adilai za su je sama. Wanda ya gaskata da hakan yakan bayyana Littafi Mai Tsarki bisa ga wannan ra’ayin. Alal misali, a ce mun karanta masa Ru’ya ta Yohanna 21:4. (Karanta.) Mutumin zai iya tunani cewa abubuwan da aka kwatanta a ayar za su faru a sama ne. Ta yaya za mu iya taimaka masa? Maimakon karanta wani nassi da ya yi magana a kan batun, za mu iya bayyana masa abin da nassin nan ya ce. Nassin ya ce “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.” Za mu iya yi wa mutumin wannan tambayar: “Idan aka ce wani abu ba zai ƙara kasancewa ba, wato abin ya kasance a dā, ko ba haka ba? Zai iya ce haka ne. Bayan haka, za mu iya faɗa masa cewa ba a taɓa mutuwa a sama ba, a nan duniya ne ake mutuwa. Saboda haka, Ru’ya ta Yohanna 21:4 tana magana ne game da abubuwan da za su faru a nan duniya.—Zab. 37:29.

KA YI AMFANI DA KWATANCI DON A FAHIMCI BATUN SOSAI

12. Me ya sa Yesu ya yi amfani da kwatanci?

12 Yesu ya yi amfani da kwatanci sa’ad da yake wa’azi. (Karanta Matta 13:34, 35.) Kwatancin da Yesu ya yi amfani da su sun taimaka wajen sanin ainihin abin da ke zuciyar masu sauraronsa. (Mat. 13:10-15) Ƙari ga haka, kwatancin Yesu sun sa mutane sun ji daɗin koyarwarsa. Ban da haka, sun sa mutane sun tuna da darasin. Ta yaya za mu yi amfani da kwatanci sa’ad da muke koyarwa?

13. Ta yaya za mu kwatanta cewa Allah ya fi Yesu iko?

13 Kwatanci mafi amfani su ne waɗanda ke da sauƙin fahimta. Alal misali, sa’ad da muke ƙoƙarin bayyana wa mutane cewa Allah ya fi Yesu matsayi, za mu iya yin amfani da wannan kwatancin: Za mu iya cewa dangantakar Yesu da Allah tana kamar na uba da ɗa. Allah ya kwatanta Yesu a matsayin Ɗa, Yesu kuma ya kwatanta Allah a matsayin Uba. (Luk 3:21, 22; Yoh. 14:28) Daga baya, za mu iya tambayar mutumin: “Idan kana so ka yi mini kwatancen mutane biyu da ke da matsayi iri ɗaya, wane irin dangantaka na iyali ne za ka yi amfani da shi?” Mutumin zai iya ce yaya da ƙane ko kuma tagwaye. Idan ya ba da wannan amsar, za mu iya ce kwatancin da ya yi daidai ne. Bayan haka, za mu iya tambayarsa: “Idan har za ka iya tunanin irin wannan kwatancin, kana ganin Yesu wanda shi ne Babban Malami ba zai iya yin amfani da irin wannan kwatancin ba? Amma bai yi hakan ba. Maimako, ya ce Allah Ubansa ne. Ta hakan, Yesu ya taimaka mana mu fahimci cewa Allah ya fi shi iko.”

14. Wane kwatanci ne yake nuna cewa ba zai dace a ce Allah zai ba wa Shaiɗan damar hukunta mutane a wutar jahannama ba?

14 Ka yi la’akari da wani misali. Wasu sun gaskata cewa Shaiɗan ne zai hukunta mutane a wutar jahannama. Ta yaya za mu iya taimaka wa mahaifi ya gane cewa ra’ayin nan bai da kan gado? Za mu iya yin wannan tambayar: “A ce ɗanka ya yi maka tawaye kuma yana aikata mugunta sosai. Mene ne za ka yi?” Mahaifin zai iya ce zai yi wa ɗansa gyara kuma ya yi ƙoƙari wajen ganin cewa ɗan ya daina yin abubuwan nan da ba su da kyau. (Mis. 22:15) A nan, za mu iya tambayarsa kuma: “Mene ne za ka yi idan ɗanka ya ƙi amincewa da gyarar da kake yi masa?” Iyaye da yawa za su iya cewa idan ya ƙi gyarar, za su yi masa horo. Sai mu yi masa wannan tambayar, “Idan ka gano cewa wani mugun mutum ne yake rinjayar ɗanka fa?” Babu shakka, mahaifin zai yi fushi da wannan mugun mutumin da ke rinjayar ɗansa ya yi mugunta. Bayan haka, za ka iya tambayarsa: “Da yake ka san cewa wani mugu ne ya rinjayi ɗanka, za ka so ka miƙa wa wannan mutumin ɗanka don ya yi masa horo?” Hakika, mahaifin zai ce a’a. Sai ka kammala da bayyana cewa da yake Shaiɗan ne ya sa waɗannan mutanen su aikata mugunta, a bayyane yake cewa Allah ba zai yi amfani da shi wajen hukunta mutanen ba.

KA KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE

15, 16. (a) Me ya sa bai kamata mu ɗauka cewa dukan mutane da muka yi musu wa’azi za su amince da saƙon Mulkin ba? (b) Shin sai mun zama ƙwararru kafin mu iya koyarwa da kyau? Ka bayyana. (Ka kuma duba akwatin nan “Abubuwan da Za Su Taimaka Mana Mu Ba da Amsa.”)

15 Masu magana sun ce, dubu na so, dubu na ƙi. Saboda haka, ba dukan mutane ba ne za su amince da saƙon Mulkin ba. (Mat. 10:11-14) Ko da mun yi amfani da tambayoyin da suka dace, mun bayyana abin da Littafi Mai Tsarki ya ce dalla-dalla kuma mun yi amfani da kwatanci masu kyau. Mutane kaɗan ne suka ba da gaskiya ga koyarwar Yesu duk da cewa ba malamin da ya ƙware kamar shi tun farkon halitta!—Yoh. 6:66; 7:45-48.

16 Amma idan muna gani cewa ba mu iya koyarwa sosai ba fa? Za mu iya yin wa’azi da kyau. (Karanta Ayyukan Manzanni 4:13.) Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa dukan waɗanda Uban ya jawo za su amince da bisharar. (Yoh. 6:44) Saboda haka, bari mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu da kuma waɗanda muke musu wa’azin bisharar Mulki. Mu yi iya ƙoƙari mu ba da kanmu ga koyarwar da Jehobah yake tanadar mana, hakan zai amfane mu da waɗanda suka saurare mu. (1 Tim. 4:16) Jehobah zai iya taimaka mana mu san yadda ya kamata mu ba da “amsa” ga kowane mutum. Talifi na gaba zai tattauna yadda za mu yi nasara a hidimarmu ta wajen bin sanannen umurnin da Yesu bayar na bi da mutane yadda za mu so su bi da mu.

a Ka duba talifin nan “Halitta Tana Bayyana Allah Mai Rai” da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2013.

Abubuwan da Za Su Taimaka Mana Mu Ba da Amsa

An ɗauko wasu misalai da aka yi amfani da su a nan daga talifofin “Tattaunawa Tsakanin Shaidun Jehobah da Mutane” da kuma “Tattaunawa Tsakanin Wani Mutum da Mashaidin Jehobah.” Yana fitowa loto-loto a Hasumiyar Tsaro na wa’azi.b

Wata ’yar’uwa ta bayyana yadda waɗannan jerin talifofin sun taimaka mata a hidimarta, ta ce: “Ina koyan yadda ake tattaunawa mai ma’ana da yadda ake yin tambayoyi masu sa tunani da kuma yadda zan ba da amsar da ta dace ga tambaya. Ni mai son koyon abu ne ta wurin misali kuma waɗannan talifofin suna sa in cim ma burina.”

Wannan jerin ɗaya ne kawai daga cikin abubuwa da yawa da Jehobah yake tanadar mana don mu cika aikin da ya ba mu. (Zab. 32:8) Muna godiya sosai cewa Jehobah yana tanadar mana abubuwan da muke bukata don mu cika hidimarmu!

b Waɗannan talifofin da ke gaba su ne aka wallafa a yanzu: “Shin Dukan Masu Adalci Za Su Je Sama Ne?” (Oktoba–Disamba 2012) da “Allah Ya Damu da Wahalar da Muke Sha Kuwa?” (Satumba–Oktoba 2013) da kuma “Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala?” (Maris–Afrilu 2014).

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba