SHIN KUNA CE I Kuma Daga Baya Ku Ce A’a?
Ka yi la’akari da wannan yanayin: Wani dattijo da ke cikin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ya yi shirin fita wa’azi da wani ɗan’uwa matashi a ranar Lahadi da safe. Sai wani ɗan’uwa ya yi wa dattijon waya cewa matarsa ta yi hatsari kuma an kai ta asibiti. Sai ɗan’uwan ya gaya dattijon ya taimaka wajen neman likitan da zai yarda ya yi wa matarsa jinya ba tare da jini ba. Sai dattijon ya fasa fita wa’azi da matashin don ya je ya taimaka wa wannan iyalin da yake bukatar jinyar gaggawa.
Ka yi la’akari da wani labari kuma: Wasu ma’aurata sun gayyaci wata mahaifiya da yaranta biyu da ke ikilisiyarsu zuwa gidansu. Sa’ad da ta gaya wa yaranta game da gayyatar, sai suka yi farin ciki ƙwarai. Kuma suka yi ɗokin ranar ta isa. Amma kafin ranar, sai ma’auratan suka gaya wa matar cewa wata larura ta taso, saboda haka, ba za su iya cika alkawarinsu ba. Daga baya, sai matar ta fahimci dalilin da ya sa waɗannan ma’auratan ba su cika alkawarinsu ba. Wane dalili ke nan? Bayan da ma’auratan suka gayyace su, wasu abokansu sun gayyaci ma’auratan zuwa gidansu a ranar da suka yi alkawari da matar kuma sun amince da hakan.
A matsayinmu na Kiristoci, ya kamata mu riƙa cika alkawarin da muka yi da mutane. Bai kamata mu sa kanmu a cikin yanayin da za mu ce i, kuma daga baya mu ce a’a ba. (2 Kor. 1:18) Amma kamar yadda waɗannan misalai biyu suka nuna, a wani lokacin, zai zama dole mu kasa cika alkawari saboda wata larura, a wani lokaci kuma, don wani dalilin da bai taka kara ya karya ba. Manzo Bulus ya taɓa samun kansa a irin wannan yanayin.
AN ZARGI BULUS DA YIN ƘARYA
Sa’ad da Bulus yake Afisa a tafiyarsa ta uku a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje a shekara ta 55 a zamaninmu, ya so ya ƙetare zuwa tekun Aegean daga wurin kuma sai ya je yankin Makidoniya. Da yake komawa Urushalima, ya yi nufin ziyartar ikilisiyar Koranti zuwa na biyu wataƙila don ya karɓi kyautar da suke da shi don ’yan’uwa da ke Urushalima. (1 Kor. 16:3) An ga hakan dalla-dalla a littafin 2 Korintiyawa 1:15, 16, wurin ya ce: “Da wannan amincewa fa ina da nufi in zo wurinku tun ba yau ba, domin ku sami abin farin ciki biyu: daga wajenku kuma in wuce zuwa cikin Makidoniya, daga Makidoniya kuma in sake koma wurinku, in sami rakiya a wurinku cikin tafiyata zuwa Yahudiya.”
Mai yiwuwa, Bulus ya gaya wa ’yan’uwan da ke Koranti game da tafiyar da zai yi a wata wasiƙar da ya rubuta musu. (1 Kor. 5:9) Amma jim kaɗan bayan Bulus ya rubuta wannan wasiƙar, sai ya sami labari daga iyalin Kuluwi cewa akwai matsala sosai a ikilisiyar. (1 Kor. 1:10, 11) Wannan ne ya sa Bulus ya fasa zuwa inda ya ce zai je da farko, kuma ya rubuta wasiƙarsa ta farko, wato Korintiyawa ta fari. A cikin wannan wasiƙar, Bulus ya ba da kashedi kuma ya tsauta musu. Ya kuma gaya musu cewa ya canja tafiyarsa, ya ce zai je Makidoniya da farko kafin ya je Koranti.—1 Kor. 16:5, 6.a
Wataƙila sa’ad da ’yan’uwa da ke Korinti suka sami wasiƙar Bulus, wasu “mafifitan manzanni” a ikilisiyar sun zarge shi da yin ƙarya, wato ba ya cika alkawari. Bulus ya ƙaryata su kuma ya tambaye su: “Yayin da na yi nufi haka fa, halin zara na nuna? ko kuwa abin da nake ƙudurtawa, kamar mutumin duniya ni ke ƙudurta su, har ya zama a gare ni akwai i, i, da a’a, a’a?”—2 Kor. 1:17; 11:5.
Za mu iya yin tambaya, A wannan yanayin, manzo Bulus bai ɗauki batun da muhimmanci ba ne? Babu shakka ya ɗauki batun da muhimmanci! Ana iya amfani da kalmar da aka fassara zuwa “zara” don kwatanta mutumin da ke saɓa alkawari. Tambayar nan da Bulus ya yi cewa “abin da nake ƙudurtawa, kamar mutumin duniya ni ke ƙudurta su?” da ya kamata ya taimaka wa Kiristocin da ke Koranti su fahimci cewa sake shawara da Bulus ya yi bai nuna cewa ba ya cika alkawari ba.
Bulus ya ƙaryata su sa’ad da ya ce: “Amma dai kamar yadda Allah mai aminci ne, maganarmu zuwa gareku ba i da a’a ba ce.” (2 Kor. 1:18) Babu shakka, Bulus ya canja shawararsa don ya so ya taimaka wa ’yan’uwa da ke Koranti ne. Littafin 2 Korintiyawa 1:23 ya gaya mana cewa Bulus ya fasa zuwa Koranti don ya “sawaƙa” wa ’yan’uwa. Hakika, Bulus ya fasa zuwa Koranti don su sami zarafin bin shawarar da ya ba su kafin ya ziyarce su. Kuma abin da suka yi ke nan. Sa’ad da Bulus ya ke Makidoniya, Titus ya ba shi labari cewa wasiƙar da ya rubuta ya taimaka wa ’yan’uwa da ke Koranti su fahimci cewa abin da suka yi bai dace ba kuma sun tuba. Hakan ya sa Bulus farin ciki sosai.—2 Kor. 6:11; 7:5-7.
YESU SHI NE “AMIN”
A lokacin da “mafifitan manzanni” suka zargi Bulus da rashin cika alkawari, wataƙila sun tuhumi wa’azin da yake yi ma. Amma Bulus ya tuna wa waɗannan ’yan’uwa da ke Koranti cewa shi ya yi musu wa’azi game da Kristi. Ya ce: “Ɗan Allah, Yesu Kristi wanda aka yi wa’azinsa a cikinku ta bakinmu, ni da Silwanus da Timothawus, ba i da a’a ba ne, amma cikinsa akwai i.” (2 Kor. 1:19) Yesu Kristi, wanda Bulus yake bin misalinsa ba mai saɓa alkawari ba ne. A rayuwar Yesu da kuma hidimarsa, ya koyar da gaskiya a kowane lokaci. (Yoh. 14:6; 18:37) Da yake Yesu ya koyar gaskiya kuma shi mai cika alkawari ne, za mu tabbata da wa’azin da Bulus ya yi domin hidimarsa ɗaya ne da na Yesu.
Hakika, Jehobah “Allah na gaskiya” ne. (Zab. 31:5) Mun ga hakan a abin da Bulus ya rubuta cewa: “Gama kome yawan alkawura na Allah, a cikinsa akwai i,” wato, ta wurin Kristi ke nan. Da yake Yesu ya kasance da aminci sa’ad da yake duniya, muna da tabbaci cewa alkawarin da ya yi mana zai tabbata. Bulus ya ƙara da cewa: “Domin wannan fa ta wurinsa [Yesu] akwai Amin, zuwa darajar Allah ta wurinmu.” (2 Kor. 1:20) Mene ne ake nufi sa’ad da ake ce Yesu ne “Amin”? Yana nufin cewa ta wurin Yesu ne dukan alkawuran Jehobah za su cika!
Hakika, kamar yadda maganar Jehobah da na Yesu suke da tabbaci, hakan ma na Bulus take. (2 Kor. 1:19) Shi mai cika alkawari ne, ba wai yana yin alkawari “kamar mutumin duniya” ba. (2 Kor. 1:17) Maimakon haka, ya “yi tafiya bisa ga ruhu.” (Gal. 5:16) Dukan abubuwan da Bulus ya yi sun nuna cewa yana ƙaunar ’yan’uwansa. Hakika, i da ya faɗa, i ne da gaske!
IDAN KA CE I, KANA CIKA ALKAWARINKA KUWA?
A yau, mutane sukan yi alkawari kuma su kasa cika alkawarin domin wani dalilin da bai taka kara ya karya ba ko kuma domin sun fi so su yi wani abu dabam a wannan lokacin. A batun kasuwanci, mutane ba sa yawan cika “i” da suke faɗa ko da an riga an rubuta yarjejeniya. Mutane da yawa ba sa ɗaukan aure a matsayin alkawarin da mutane biyu suka yi cewa ko da wahala za su zauna tare muddar ransu. Adadin mutane da suke kashe aure yana ƙaruwa sosai, kuma hakan ya nuna cewa ba sa ɗaukan alkawarin aure da muhimmanci kuma za su iya karya alkawarin a duk lokacin da suka ga dama.—2 Tim. 3:1, 2.
Kai kuma fa? Idan ka ce i, kana cika alkawarinka kuwa? Kamar yadda muka gani a farkon talifin nan, a wani lokaci zai zama dole ka kasa cika wani alkawarin da ka yi, kuma hakan ba ya nufin cewa ba ka cika alkawari, amma don wata larura da ta kama ka ne. Amma a matsayinmu na Kirista, ya kamata mu riƙa cika alkawarin da muka yi. (Zab. 15:4; Mat. 5:37) Idan muka yi hakan, za a san mu a matsayin mutanen da suke cika alkawari kuma suna faɗin gaskiya a koyaushe. (Afis. 4:15, 25; Yaƙ. 5:12) Idan mutane suka san ka da cika alkawari, za su so su saurare ka sa’ad da ka zo yi musu wa’azi game da Mulkin Allah. Saboda haka, ya kamata I ɗinmu ya zama I da gaske!
a Ba da daɗewa ba bayan Bulus ya rubuta littafin Korintiyawa ta fari, sai ya je Taruwasa, daga wurin kuma ya je Makidoniya, a can ne ya rubuta littafin Korintiyawa ta biyu. (2 Kor. 2:12; 7:5) Bayan haka, sai ya je Koranti.