Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/15 p. 26-p. 28 par. 11
  • Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Korinthiyawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Korinthiyawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘KU YI TSARO, KU YI ƘARFI, KU ƘARFAFA’
  • (1 Kor. 1:1–16:24)
  • ‘KU CI GABA DA YIN GYARA’
  • (2 Kor. 1:1–13:14)
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ta Yaya Za A Ta da Matattu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Za A Yi Tashin Matattu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mu Bi Raꞌayin Jehobah Game da Wadanda Suka Yi Zunubi Mai Tsanani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/15 p. 26-p. 28 par. 11

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Korinthiyawa

MANZO Bulus ya damu da ikilisiya da ke Korinthi. Ya ji cewa akwai matsala a tsakaninsu. Sun yarda da lalata. Ikilisiyar ta rubuta wa Bulus game da wasu batutuwa. Saboda haka, a shekara ta 55 K.Z., sa’ad da yake Afisa a lokacin tafiyarsa ta uku na wa’azi, Bulus ya rubuta wasiƙarsa guda biyu ga Korinthiyawa.

Wasiƙa ta biyu da ya rubuta ’yan watanni bayan wasiƙa ta farko, ci gabawar wasiƙarsa ta farko ne. Tun da yanayin da ke cikin ikilisiyar da kuma na waje a ƙarni na farko ya yi daidai da na zamaninmu, saƙon da Bulus ya rubuta wa Korinthiyawa yana da muhimmanci a gare mu.—Ibran. 4:12.

‘KU YI TSARO, KU YI ƘARFI, KU ƘARFAFA’

(1 Kor. 1:1–16:24)

Bulus ya yi gargaɗi: “Ku yi magana ɗaya.” (1 Kor. 1:10) ‘Ba wani gindi dabam da an rigaya an kaga ba, Yesu Kristi,’ wato, tushen halayen Kirista. (1 Kor. 3:11-13) Game da masu lalata a ikilisiya, Manzo Bulus ya ce: “Ku fitarda mugun nan daga cikinku.” (1 Kor. 5:13) Ya ce, “jiki ba domin fasikanci ya ke ba, amma domin Ubangiji ne.”—1 Kor. 6:13.

Game da ‘al’amuran da suka rubuta,’ Bulus ya ba da gargaɗi mai kyau game da masu aure da marasa aure. (1 Kor. 7:1) Bayan da ya yi magana game da shugabanci na Kirista, tsarin taron Kirista, da kuma tabbacin tashin matattu, Bulus ya yi wannan gargaɗi: “Ku yi tsaro, ku tsaya da ƙarfi cikin imani, ku mazakuta, ku ƙarfafa.”—1 Kor. 16:13.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:21—Da gaske ne Jehobah yana amfani da “wauta” don ya ceci masu ba da gaskiya? A’a. Da yake “duniya ba ta san [Allah] ba,” abin da ya yi amfani da shi ya ceci duniya ta zama kamar wauta a gare su.—Yoh. 17:25.

5:5—Menene ake nufi da a “bada wannan irin [mugun] mutum ga Shaiɗan garin a hallaka jiki, domin ruhu shi tsira”? Idan aka yi wa wani mai zunubi da ya ƙi tuba yankan zumunci daga ikilisiya, ya zama ɗaya daga cikin mugun duniya na Shaiɗan. (1 Yoh. 5:19) Hakika, shi ya sa aka ce an ba da shi ga Shaiɗan. Abin da ya sa aka cire mutumin shi ne don kada ya lalata ko kuma don a cire mugu daga cikin ikilisiya kuma a kāre ruhun Allah.—2 Tim. 4:22.

7:33, 34—Menene “abin da ke na duniya” da ma’aurata suke damuwa da shi yake nufi? Bulus yana nufin abubuwa na rayuwa da ya kamata ma’aurata Kirista su damu da su. Wannan ya ƙunshi abinci, tufafi, da kuma wajen kwana, ban da mugayen abubuwa na duniya da ya kamata Kirista su guje musu.—1 Yoh. 2:15-17.

11:26—Ta yaya za a tuna da mutuwan Yesu “kowane lokaci” kuma “har” yaushe? Bulus bai ce wai a tuna da mutuwar Yesu a kowane lokaci ba. Kalmar Hellenanci da aka fassara “kowane lokaci” yana nufin “sa’ad da” ko kuma “duk lokacin da.” Bulus yana nufin cewa a duk lokacin da shafaffu Kiristoci suka ci ishara na tuna mutuwar Yesu, sau ɗaya a shekara, a 14 ga Nisan, suna “shelar mutuwar Ubangiji” ne. Suna yin haka ne “har [sai] ya zo,” wato, har sai lokacin da ya karɓe su a sama ta wurin tashin matattu.—1 Tas. 4:14-17.

13:13—Ta yaya ne ƙauna ta fi bangaskiya da bege? Sa’ad da “abin da mu ke begensa” ya yiwu, za mu ga cewa bege da bangaskiya ba su da muhimmanci kamar dā. (Ibran. 11:1) Ƙauna ta fi bangaskiya da bege saboda tana kasancewa har abada.

15:29—Menene ake nufi da “baftisma saboda matattu?” Bulus ba yana nufin cewa za a yi wa mutane masu rai baftisma a madadin waɗanda suka mutu ba tare da yin baftisma ba. A nan Bulus yana magana cewa shafaffun Kiristoci sun soma bin wani tafarkin rayuwa da ya sa suka kasance da aminci har mutuwarsu da kuma tashiwarsu zuwa rayuwa na ruhu.

Darussa Dominmu:

1:26-31; 3:3-9; 4:7. Yin fahariya ga Jehobah ba don kanmu ba, yana kawo haɗin kai a cikin ikilisiya.

2:3-5. Sa’ad da yake wa’azi a Korinthi, cibiyar ussan ilimi na Hellenanci da kuma koyarwa, Bulus ya damu da yadda zai sha kan masu sauraransa. Duk da haka, bai ƙyale kumamancinsa da tsoron mutane su hana shi yin hidimar da Allah ya ce ya yi ba. Hakazalika, bai kamata mu bar yanayi mai wuya ya hana mu shelar bisharar Mulki Allah ba. Ya kamata mu dogara ga Jehobah kamar yadda Bulus ya yi.

2:16. Sanin “nufin Kristi” yana nufin mu fahimci yadda yake tunani, mu yi tunani kamarsa, mu san halayensa, kuma mu yi koyi da misalinsa. (1 Bit. 2:21; 4:1) Yana da muhimmanci mu yi nazari sosai game da rayuwar Yesu da kuma hidimarsa.

3:10-15; 4:17. Ya kamata mu bincika kuma mu kyautata yadda muke koyarwa da kuma almajirantarwa. (Mat. 28:19, 20) Idan ba ma koyarwa da kyau, wataƙila ɗalibanmu ba za su tsira daga gwaji na bangaskiyarsu ba, hakan zai sa mu yi hasara sosai har tsirarmu ta kasance kamar ta “wurin tsakiyar wuta.”

6:18. “Guje ma fasikanci” yana nufin guje wa por·neiʹa da kuma batsa, lalaci, tunanin jima’i, kwarkwasa, wato, dukan abin da zai iya kai ga fasikanci.—Mat. 5:28; Yaƙ. 3:17.

7:29. Ya kamata ma’aurata su mai da hankali kada su yi tunanin bukatar juna har su mance da al’amuran Mulki ko kuma su sa ta zama abu na biyu a rayuwarsu.

10:8-11. Jehobah ya yi fushi sosai sa’ad da Isra’ila suka yi gunaguni game da Musa da Haruna. Za mu amfana idan muka guji halin gunaguni.

16:2. Za mu ci gaba da ba da gudummawa don tallafa wa’azin mulki idan muka yi shiri sosai kuma muka tsara yadda za mu riƙa bayarwa.

‘KU CI GABA DA YIN GYARA’

(2 Kor. 1:1–13:14)

Bulus ya gaya wa Korinthiyawa cewa su ‘gafarta, su yi ta’aziya’ ga mutum mai laifi da aka yi masa horo da ya tuba. Ko da yake wasiƙarsa ta farko ta sa su baƙin ciki, Bulus ya nuna farin cikinsa saboda ‘ɓacinzuciya da suka yi ya kawo tuba.’—2 Kor. 2:6, 7; 7:8, 9.

‘Kamar yadda sun yalwata cikin dukan abu,’ Bulus ya gargaɗi Korinthiyawa su ‘yalwata cikin alheri.’ Bayan da ya amsa masu yi masa hamayya, ya ba da shawara ta ƙarshe ga dukan mutane: “Ku [yi gyara]; ku ta’azantu; hankalinku ya zama ɗaya; ku zama cikin salama: Allah kuwa na ƙauna da na salama za ya zauna tare da ku.”—2 Kor. 8:7; 13:11.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

2:15, 16—Ta yaya ne muka zama “shesheƙi mai-daɗi . . . na Kristi”? Haka yake saboda muna yin biyayya da Littafi Mai Tsarki kuma muna yin wa’azi. Ko da yake “man ƙamshi” yana wa marasa adalci wari, yana da ƙamshi mai daɗi ga Jehobah da masu zuciyar kirki.

5:16—Ta yaya ne shafaffun Kiristoci ‘ba su ƙara sanin kowane mutum bisa ga zancen jiki ba’? Ba sa ɗaukan mutane bisa ga zancen jiki, wato, nuna son kai don arziki, launin fata, ko kuma ƙasarsu. Abin da ya fi musu muhimmanci shi ne dangantakarsu da ’yan’uwansu masu bi.

11:1, 16; 12:11—Yadda Bulus ya yi wa Korinthiyawa magana ya dace ne? E, ya dace. Amma, mai yiwuwa wasu suna ganin yana da fahariya kuma abin da ya faɗa bai dace ba saboda abin da ya ce don ya kāre manzancinsa.

12:1-4—Wanene “aka fyauce shi zuwa cikin [Aljanna]”? Tun da Littafi Mai Tsarki bai yi maganar wani mutum da ya ga irin wannan wahayin ba, kuma ayar da ta biyo baya ta yi maganar yadda Bulus ya kāre manzancinsa, wataƙila yana magana ne a kan abin da ya fuskanta. Mai yiwuwa manzon ya hangi aljanna ta ruhaniya da ikilisiyar Kirista za ta more a “kwanakin ƙarshe.”— Dan. 12:4.

Darussa Dominmu:

3:5. Hakika, wannan ayar ta gaya mana cewa Jehobah ne yake sa Kiristoci su cancanta don hidima ta wurin amfani da Kalmarsa, ruhunsa mai tsarki, da ƙungiyarsa ta duniya. (Yoh. 16:7; 2 Tim. 3:16, 17) Yana da kyau mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai masu bayyana Littafi Mai Tsarki sosai, mu nace da yin addu’a don ruhu mai tsarki, mu halarci taron Kirista a kai a kai kuma mu yi kalami.—Zab. 1:1-3; Luk 11:10-13; Ibran. 10:24, 25.

4:16. Tun da yake Jehobah yana sabonta ‘mutum namu na ciki,’ ya kamata mu yi amfani da tanadin Jehobah a kai a kai, kada mu bari rana ɗaya ta wuce ba tare da yin abubuwa na ruhaniya ba.

4:17, 18. Tuna cewa “ƙuncinmu mai-sauƙi [ne], wanda ke na lokaci kaɗan,” zai iya taimakonmu mu kasance da aminci ga Jehobah a lokacin wahala.

5:1-5. Bulus ya furta kalamin shafaffun Kiristoci game da begensu na rai a sama da kyau!

10:13. Yadda yake, sai dai ko an yi shiri na musamman don mu je mu taimaka a inda ake da bukata mai girma, ya kamata mu yi wa’azi a yankin ikilisiyarmu kaɗai.

13:5. Don mu ‘gwada kanmu ko muna cikin imani,’ ya kamata mu tabbata ko halinmu ya yi daidai da abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki. Don mu ‘yi wa kanmu ƙwanƙwanto,’ ya kamata mu bincika yadda ruhaniyarmu take, har da yadda za mu yi amfani da ‘hankalinmu’ da kuma yawan ayyukanmu na bangaskiya. (Ibran. 5:14; Yaƙ. 1:22-25) Ta wajen yin amfani da shawara mai kyau na Bulus, za mu ci gaba da yin tafiya a hanyar gaskiya.

[Hoto a shafi nas 26, 27]

Menene kalmomin nan “kowane lokacin da ku ke cin wannan gurasa, kuna kuwa shan ƙoƙon” suke nufi?—1 Kor. 11:26

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba