Abin Da Ke Ciki
15 Ga Afrilu, 2014
© 2014 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
NA NAZARI
2-8 GA YUNI, 2014
Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 33, 133
9-15 GA YUNI, 2014
Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?
SHAFI NA 8 • WAƘOƘI: 81, 132
16-22 GA YUNI, 2014
Ba Wanda Zai Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu
SHAFI NA 17 • WAƘOƘI: 62, 106
23-29 GA YUNI, 2014
Ka Kasance da Gaba Gaɗi, Jehobah Ne Mai Taimakonka!
SHAFI NA 22 • WAƘOƘI: 22, 95
30 GA YUNI, 2014–6 GA YULI, 2014
Kana Godiya don Yadda Jehobah Yake Kula da Kai?
SHAFI NA 27 • WAƘOƘI: 69, 120
TALIFOFIN NAZARI
▪ Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Musa
▪ Kana “Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa” Kuwa?
Bangaskiya ta sa Musa ya ga abin da ba za a iya gani da idanu ɓaro-ɓaro ba. Wannan talifin zai nuna yadda za mu iya kasance da bangaskiya kamar Musa kuma mu ci gaba da jimrewa ‘kamar muna ganin wanda ba shi ganuwa.’—Ibran. 11:27.
▪ Ba Wanda Zai Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu
▪ Ka Kasance da Gaba Gaɗi, Jehobah Ne Mai Taimakonka!
Miliyoyin mutane a duniya suna ƙaura zuwa wata ƙasa don neman aiki. Da yawa cikinsu suna barin matansu ko mazansu da kuma yaransu. Wannan talifin zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake so mu ɗauki hakkinmu a cikin iyali da kuma yadda yake taimaka mana mu yi hakan.
▪ Kana Godiya don Yadda Jehobah Yake Kula da Kai?
Sa’ad da muka karanta a Littafi Mai Tsarki cewa “Ubangiji yana ganin abin da ke faruwa a ko’ina,” wasu cikinmu suna iya gani cewa Allah dai yana son zartar da dokokinsa, waɗanda za su iya sa mu riƙa tsoronsa ba gaira ba dalili. (Mis. 15:3) Amma, wannan talifin zai nuna hanyoyi biyar da za mu iya amfana daga yadda Jehobah yake kula da mu.
BANGO: Wani ɗan’uwa a birnin Istanbul yana wa wani mutum da ke masa aski wa’azi sa’ad da ya sami zarafi kuma yana ba shi ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!
TURKIYA
YAWAN JAMA’A
75,627,384
MASU SHELA
2,312
NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI
1,632
KOWANE MAI SHELA A ƘASAR ZAI YI WA’AZI GA MUTANE
32,711
Tun shekara ta 2004 adadin majagaba na kullum a turkiya ya ƙaru da kashi 165