ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MUTUWA CE ƘARSHE?
Yaƙin da ’Yan Adam Suke Yi da Mutuwa
Mutuwa babban magabci ne. Muna yaƙarta da duk iyawarmu. Sa’ad da wani abokinmu ko kuma danginmu ya mutu, muna iya ƙin amincewa da hakan. Muddin muna da rai kuma muna ji da ƙuruciya, muna iya ganin kamar ba za mu taɓa mutuwa ba.
Babu wanda ya kai su Fir’auna na dā tunani a kan yin rayuwa har abada. Sun dage sosai a kan yaƙar mutuwa, kuma sun ba da ransu da kuma na ma’aikatansu wajen yin hakan. Dalolin da suka gina sun tabbatar da muradinsu. Waɗannan dalolin manya-manyan gine-gine ne, inda akwai kaburbura da ake adana gawawwakin sarakuna. Sarakunan suna ganin kamar idan suka mutu, kurwarsu za su iya shiga cikin gawawwakinsu da ake adanawa. Amma, ɓarayi sukan shiga waɗannan kaburburan, har ma a wasu lokatai su halaka gawawwakin da aka adana. Saboda da haka, waɗannan dalolin sun nuna cewa su Fir’auna sun kasa yaƙar mutuwa.
Sarakunan ƙasar Sin ma sun yaƙi mutuwa, amma sun yi hakan ta wajen amfani da magungunan da suke ganin za su iya hana mutuwa. Wani sarki mai suna Qin Shi Huang, ya sa masu harhaɗa masa magani su yi masa haɗin da zai iya raba shi da mutuwa. Amma, haɗe-haɗensu da dama sun ƙunshi gubar ƙarfe, kuma wataƙila ɗaya daga cikin haɗe-haɗen ne ya zama sanadin mutuwarsa.
A shekara ta 1513, Juan Ponce de León, wani ɗan Sifen mai bincike, ya yi tafiya a faɗin tsibirai da ke kudancin Amirka yana neman maɓulɓular da ke mai da mutum matashi. Yayin da yake wannan tafiyar, ya gano wata jiha da ake kira Florida a Amirka, amma bayan wasu ’yan shekaru, ya mutu sanadiyyar yaƙin da ya ɓarke tsakanin shi da mutanen jihar. Har wa yau, ba a gano maɓulɓula da ke mai da mutum matashi ba.
Burin waɗannan Fir’auna da sarakuna da kuma masu bincike shi ne su yi nasara a kan mutuwa. Shin za mu raina burinsu ne, ko da ba mu yarda da yadda suka yi ƙoƙarin cim ma hakan ba? Gaskiyar ita ce fa, kowannenmu yana so ya ci gaba da rayuwa.
ZA A IYA YIN NASARA A KAN MUTUWA KUWA?
Me ya sa muke adawa da mutuwa? Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin hakan. Ga abin da ya faɗa game da Mahaliccinmu, Jehobah.a Ya ce: ‘Ya sa kowane abu ya yi jamali a lokacinsa: ya kuma sa madawwaman zamanai a cikin zuciyar [’yan Adam].’ (Mai-Wa’azi 3:11) Za mu so mu ji daɗin rayuwa a duniya har abada, ba kawai na tsawon shekaru 80 ba. (Zabura 90:10) Babu shakka, muradin kowannenmu ke nan.
Me ya sa Allah ya sa “madawwaman zamanai” a cikin zuciyarmu, wato, sha’awar yin rayuwa har abada? Don kawai ya wahal da mu ne? A’a. Akasin haka, Allah ya yi mana alkawari cewa za a yi nasara a kan mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya ambata sau da sau cewa za a kawar da mutuwa, kuma ya bayyana alkawarin da Allah ya yi wa mutane cewa za su iya rayuwa har abada.—Ka duba akwati mai jigon nan “Yin Nasara a Kan Mutuwa.”
Yesu Kristi ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Hakan ya nuna cewa za a yi nasara a kan mutuwa. Amma, Yesu ya tabbatar mana cewa Jehobah ne kaɗai zai sa hakan ya yiwu.
a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.