Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 3/1 p. 3
  • Ƙarin Mutuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙarin Mutuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Ra’ayinka Game da Mutuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Mutane Ke Mutuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • ‘Allah Zai Sabonta Kome’
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 3/1 p. 3

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MUTUWA CE ƘARSHE?

Ƙarin Mutuwa

Mutuwa zance ne da yawancin mutane ba sa so su tattauna. Amma ko badaɗe ko bajima, za ta shafe mu. Ƙari ga haka, mutuwa tana jawo baƙin ciki sosai.

Ba irin shirin da za mu iya yi da zai hana mu baƙin ciki sa’ad da muka rasa iyayenmu ko abokin aurenmu ko kuma ’ya ko ɗanmu. Masifa tana iya auko mana sau da sau ko kuma ta auko ba zato ba tsammani. Ko ta yaya dai, mutuwa tana jawo baƙin ciki sosai kuma ba za mu iya guje wa hakan ba.

Wani mai suna Antonio, wanda mota ta kaɗe mahaifinsa har ya mutu, ya bayyana yadda ya ji game da hakan. Ya ce: “Yanayin na nan kamar wani ya ƙulle gidanka ne kuma ya tafi da maƙullin. Ba yadda za ka iya dawowa ka shiga gida kuma ba. An bar ka da labari kawai. Ko da ka yi ƙoƙarin musanta cewa hakan ya faru, ba abin da za ka iya yi.”

Dorothy, wadda mijinta ya rasu sa’ad da take da shekaru 47, ta ƙudura ta sami amsoshi ga wasu tambayoyi da ke damunta. Ko da yake Dorothy tana koya wa yara a cocinsu cewa mutane suna ci gaba da rayuwa bayan mutuwa, ba ta san ainihin abin da ke faruwa bayan mutuwa ba. Sai wata rana ta tambayi limamin cocinsu na Angilika cewa: “Mene ne yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?” Ya ce mata: “Ba wanda ya san lallai abin da ke faruwa. Namu dai ido ne kawai.”

Shin akwai yadda za mu iya sani ko za mu iya rayuwa bayan mutuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba