Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 3/1 pp. 6-7
  • Mutuwa Ba Ƙarshe Ba Ce!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mutuwa Ba Ƙarshe Ba Ce!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘IDAN MUTUM YA MUTU, ZAI SAKE RAYUWA?’
  • YAUSHE NE ZA A TA DA MATATTU?
  • Begen Waɗanda Suka Mutu Shi Ne Tashin Matattu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Za a Ta da Matattu!
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 3/1 pp. 6-7

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MUTUWA CE ƘARSHE?

Mutuwa Ba Ƙarshe Ba Ce!

Bait’anya wani ƙaramin ƙauye ne mai nisan mil 2 daga Urushalima. (Yohanna 11:18) Wani abin baƙin ciki ya faru a ƙauyen nan ’yan makonni kafin mutuwar Yesu. Wani abokin Yesu mai suna Li’azaru ya soma ciwo ba zato ba tsammani har ya rasu.

Sa’ad da Yesu ya ji labarin, ya gaya wa almajiransa cewa Li’azaru yana barci, kuma yana so ya je ya tashe shi. (Yohanna 11:11) Amma almajiran Yesu ba su fahimci abin da yake nufi ba. Saboda haka, Yesu ya gaya musu dalla-dalla cewa: “Li’azaru ya mutu.”—Yohanna 11:14.

Bayan kwana huɗu da binne Li’azaru, Yesu ya je Bait’anya kuma ya yi ƙoƙarin ta’azantar da Martha, ’yar’uwar mamacin. Martha ta gaya masa cewa: “Da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” (Yohanna 11:17, 21) Yesu ya ce mata: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu.”—Yohanna 11:25.

“Li’azaru, ka fito”!

Yesu ya yi wani abu don ya nuna cewa abin da ya faɗa gaskiya ne. Ya je bakin kabarin kuma ya yi kira da babbar murya, cewa: “Li’azaru, ka fito”! (Yohanna 11:43) Mutanen da ke wurin sun yi mamaki sa’ad da suka ga wannan mutumin da ya mutu ya fito.

Kafin wannan lokacin, Yesu ya ta da matattu biyu. Akwai lokacin da ya ta da wata yarinya, wato ’yar Yairus. Amma kafin Yesu ya ta da ita, ya ce tana barci.—Luka 8:52.

Ka lura cewa Yesu ya kamanta mutuwa da barci a lokacin da Li’azaru da kuma ’yar Yairus suka rasu. Me ya sa wannan kwatancin ya dace? Domin idan mutum yana barci, ba ya sanin kome, balle ma ya sha wahala ko azaba. (Mai-Wa’azi 9:5; ka duba akwatin nan, “Mutuwa Tana Kama da Barci Mai Nauyi.”) Almajiran Yesu na farko sun fahimci ainihin yanayin da matattu suke ciki. Littafin nan Encyclopedia of Religion and Ethics ya bayyana cewa: “Mabiyan Yesu sun ɗauki mutuwa a matsayin barci, kabari kuma a matsayin wurin hutu . . . ga waɗanda suka mutu da bangaskiya.”a

Sanin cewa matattu ba sa shan azaba amma suna barci ne kawai a kabari yana ƙarfafa mu, ko ba haka ba? Saboda haka, ba ma jin tsoron mutuwa domin mun san abin da zai faru da mu idan muka mutu.

‘IDAN MUTUM YA MUTU, ZAI SAKE RAYUWA?’

Babu shakka cewa muna jin daɗin barci sosai, amma akwai wanda zai so ya yi barci har abada? Mene ne ke sa mu kasance da bege cewa matattu za su sake rayuwa, kamar yadda Li’azaru da ’yar Yairus suka yi?

Wani bawan Allah mai suna Ayuba ya yi makamancin wannan tambayar a lokacin da yake shan azaba. Ya ce: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?”—Ayuba 14:14.

Ayuba ya amsa wannan tambayar da kansa sa’ad da yake magana game da Allah. Ya ce: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayuba 14:15) Ayuba ya tabbata cewa Jehobah yana marmarin ta da amintaccen bawansa daga mutuwa. Shin mafarki ne Ayuba yake yi? Ko kaɗan.

Yadda Yesu ya ta da matattu tabbaci ne cewa Allah ya ba shi iko bisa mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce yanzu Yesu yana riƙe da “maƙullai na mutuwa.” (Ru’ya ta Yohanna 1:18) Saboda haka, Yesu yana da iko ya ta matattu nan gaba, kamar yadda ya ta da Li’azaru.

Littafi Mai Tsarki ya yi alkawarin tashin matattu sau da sau. Wani mala’ika ya gaya wa annabi Daniyel cewa: “Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.” (Daniyel 12:13; Littafi Mai Tsarki) Yesu ya gaya ma wasu shugabannin Yahudawa da ba su amince da alkawarin tashin matattu ba cewa: “Kun yi kuskure, don rashin sanin Litattafai da ikon Allah kuma.” (Matta 22:23, 29) Manzo Bulus ya ce: “Ina da bege ga Allah, . . . [cewa] za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayyukan Manzanni 24:15.

YAUSHE NE ZA A TA DA MATATTU?

A yaushe ne za ta da masu adalci da marasa adalci? Mala’ikan ya gaya wa Daniyel cewa zai tashi “a ƙarshen kwanaki.” Hakazalika, Martha ta gaskata cewa ɗan’uwanta Li’azaru zai ‘tashi kuma a cikin tashin matattu a rana ta ƙarshe.’—Yohanna 11:24.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wannan “rana ta ƙarshe” tana nufin lokacin Sarautar Kristi ne. Bulus ya ce: “Gama shi [Kristi] dole za ya yi mulki, har [Allah] ya sa dukan maƙiyansa ƙarƙashin sawayensa. Maƙiyi na ƙarshe da za a kawar, mutuwa ne.” (1 Korintiyawa 15:25, 26) Wannan ya ba mu dalili mai kyau na roƙon Mulkin Allah ya zo kuma a yi nufinsa a duniya.b

Ayuba ya san cewa nufin Allah ne ya ta da matattu. A ranar tashin matattu, za a kawar da mutuwa, kuma babu wanda zai sake yin tambayar nan, ‘Mutuwa ce ƙarshe?’

a A Helenanci, kalmar nan “makabarta” tana nufin “wurin barci.”

b Za ka sami ƙarin bayani game da mulkin Allah a babi na 8 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Za ka iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha.

Mutuwa Tana Kama da Barci Mai Nauyi

  • “Ka haskaka idanuna, domin kada in yi barci na mutuwa.”—Zabura 13:3.

  • ‘Abokinmu Li’azaru yana barci; amma zan tafi, domin in tashe shi daga barci. Almajiran fa suka ce masa, Ubangiji, idan barci ya ɗauke shi, zai farka. Amma Yesu ya yi batun mutuwarsa ne.’—Yohanna 11:11-13.

  • “Dauda, bayan da ya yi bautar tsararsa bisa shawarar Allah, ya yi barci.”—Ayyukan Manzanni 13:36.

  • “An ta da Kristi daga matattu, ’ya’yan fari daga cikin waɗanda ke barci.”—1 Korintiyawa 15:20.

  • “Ba mu sonku da jahilci, ’yan’uwa, ga zancen waɗanda sun yi barci; kada ku yi baƙin ciki, kamar sauran mutane, waɗanda ba su da bege.”—1 Tasalonikawa 4:13.

Matattu Za Su Tashi

  • “Matattunka za su yi rai, gawayena za su tashi. Ku farka, ku rera waƙa”!—Ishaya 26:19.

  • “Da yawa kuwa daga cikin waɗanda suke barci cikin turɓayar ƙasa za su farka.”—Daniyel 12:2.

  • “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba