Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 pp. 3-6
  • Kalmomin da Suke Bambanta Ma’ana Za Su Taimake Ka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kalmomin da Suke Bambanta Ma’ana Za Su Taimake Ka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA KA AMFANA DAGA WAƊANNAN KALMOMIN
  • Jehobah Yana Tattara Iyalinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • “Ka Cika Hidimarka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Mu Kiyayi Duhu Kuma Mu Yi Zaman Mutanen Haske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 pp. 3-6

Kalmomin da Suke Bambanta Ma’ana Za Su Taimake Ka

Shin ka yarda cewa Yesu ne Malami mafi girma da ya taɓa wanzuwa a duniyar nan? Wataƙila, ka yi ƙoƙari ka yi koyi da fasalolin koyarwarsa, kamar yadda ya yi amfani da tambayoyi da kuma misalai. Amma, ka taɓa lura cewa yana yawan yin amfani da kalmomin da suke bambanta ma’ana a koyarwarsa kuwa?

Mutane da yawa suna yin amfani da kalmomin da suke bambanta ma’ana sa’ad da suke magana. Kai ma kana iya yin hakan sau da yawa ba da sanin ka ba. Za ka iya cewa, “Sun ce duk ’ya’yan itacen sun nuna, amma waɗannan ba su nuna ba tukun.” Ko kuma, “A dā ita shiru-shiru ce, amma yanzu, tana cuɗanya da mutane sosai.”

A irin wannan yanayin, za ka fara ambata gaskiya, sai ka faɗi akasinta ta wajen yin amfani da kalmomi kamar su, amma, sai, maimakon haka, akasin haka, ko kuma a wani ɓangare kuma. Idan ka yi magana haka, mutane za su fahimce ka domin haka suka saba yin magana.

Ko da kalmomin da suke bambanta ma’ana ba gama gari ba ne a wasu harsuna ko al’adu, duk da haka, suna da tamani sosai. Me ya sa? Domin akwai su da yawa a cikin hurarriyar Kalmar Allah. Yesu ya yi amfani da kalmomin da suke bambanta ma’ana sau da yawa. Ka yi la’akari da wannan: “Ba a kan kunna fitila, a sa ta ƙarƙashin akushi ba, amma bisa table.” “Ban zo domin in warware [Attaurat] ba, amma domin in cicika.” “Kun ji aka faɗi, Ba za ka yi zina ba: amma ni ina ce muku, dukan wanda ya dubi mace . . . ” “Kun ji aka faɗi, Ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori. Amma ni ina ce muku, Ba za ku yi tsayayya da wanda shi ke mugu ba: amma iyakar wanda ya mare ka a kumatu na dama, juya masa wancan kuma.”—Mat. 5:15, 17, 27, 28, 38, 39.

Akwai irin waɗannan kalmomi da suke bambanta ma’ana a wasu ayoyi na Littafi Mai Tsarki. Za su iya taimaka maka ka fahimci wani batu ko kuma ka san furucin da ya fi muhimmanci. Idan kai iyaye ne, ka yi la’akari da wannan furucin da ke bambanta ma’ana: “Ku ubanni kuma, kada ku yi wa ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin foron Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Da a ce manzo Bulus ya dai rubuta cewa iyaye su horar da ’ya’yansu yadda Jehobah yake so, da hakan ya yi daidai. Har ila, kalmomin nan ‘kada ku yi musu cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin foron Ubangiji da gargaɗinsa’ sun fi sa mu fahimtar batun.

Daga baya, Bulus ya ce: “Kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da . . . rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afis. 6:12) Babu shakka, waɗannan kalmomin da suke bambanta ma’ana sun taimaka maka ka san cewa kokawar da za mu yi ba cin tuwo ba ne. Wannan kokawar ba da mutane ba ne, amma da miyagun ruhohi.

YADDA ZA KA AMFANA DAGA WAƊANNAN KALMOMIN

A cikin wannan littafin Afisawa kuma, za ka ga wurare masu yawa da Bulus ya yi amfani da kalmomin da suke bambanta ma’ana. Yin bimbini a kan waɗannan kalmomin za su iya taimaka mana mu fahimci batun sosai kuma mu san matakin da ya kamata mu ɗauka.

Wataƙila za ka ji daɗin yin amfani da akwatin da ke gaba. Wannan akwatin ya nuna wasu kalmomin da suke bambanta ma’ana da ke cikin littafin Afisawa Surori na 4 da 5. Yayin da kake karanta kowanne cikin waɗannan kalmomin, ka yi tunani a kan yadda suka shafi rayuwarka. Ka tambayi kanka: ‘Mene ne ra’ayina da gaske? Wane mataki ne nake ɗauka a wannan yanayin ko makamancinsa? Wane ɓangare na waɗannan kalmomin da suke bambanta ma’ana ne ya bayyana irin halin da nake da shi?’ Idan ka lura cewa wasu kalmomin da suke bambanta ma’ana sun shafe ka, to ka yi gyara nan da nan. Ka bar hakan ya taimaka maka.

Ko kuma za ka iya yin amfani da akwatin nan sa’ad da kuke bauta ta iyali. Da farko, dukanku a cikin iyalin za ku iya karanta dukan kalmomin da suke bambanta ma’anar. Bayan hakan, ɗayanku zai iya ambata wani ɓangaren kalmomin da suke bambanta ma’ana, sai ya bari wani ya ambata wancan ɓangaren. Za ku iya tattauna yadda za ku yi amfani da ɓangare na biyun a matsayin iyali. Hakika, tattauna kalmomin da suke bambanta ma’ana a wannan hanyar zai iya taimaka wa yara da tsofaffi su kasance da halaye masu kyau a cikin iyali da kuma wasu fannonin rayuwa.

Yayin da kake sanin muhimmancin kalmomin da suke bambanta ma’ana, za ka ƙware wajen sanin wurin da suke a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma hakan zai taimaka maka sosai a hidimar Kirista. Alal misali, za ka iya ce wa mai gida: “Mutane da yawa sun gaskata cewa kurwa ba ta mutuwa, amma ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.” Ko kuma sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya yin wannan tambayar: “Yawancin mutane a wannan unguwar sun gaskata da wutar jahannama, amma mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun?”

Hakika, Nassosi suna ɗauke da ɗimbin kalmomin da suke bambanta ma’ana da za su iya taimaka mana mu yi biyayya ga dokokin Allah. Kuma za mu iya yin amfani da kalmomin da suke bambanta ma’ana don taimaka wa mutane su san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Wasu Cikin Kalmomin da ke Afisawa Surori 4 da 5

Ka ƙoƙarta ka yi amfani da akwatin nan a bautarku ta iyali!

‘Kada mu zama . . . waɗanda ana wofar da su suna lilo . . . ta wurin ruɗun mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.’—4:14.

“Amma garin faɗin gaskiya cikin ƙauna, mu yi girma cikin abu duka zuwa cikinsa, wanda shi ne kai, wato Kristi.”—4:15.

‘[Al’ummai] suna da duhun hankali, . . . saboda taurin zuciyarsu.’—4:18, 19.

“Amma ba haka kuka koyi Kristi ba; idan dai lallai kun ji shi, kun koya kuma a cikinsa.”—4:20, 21.

“Mai-yin sata kada ya ƙara yin sata.”—4:28.

“Amma gwamma ya yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da yake da kyau.”—4:28

“Kada kowane ruɓaɓɓen zance shi fita daga cikin bakinku.”—4:29.

“Sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa.”—4:29

“Fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku.”—5:3.

“Amma gwamma bada godiya.”—5:4.

“Dā ku duhu ne.”—5:8.

“Amma yanzu haske ne cikin Ubangiji.”—5:8

“Kada ku yi tarayya da ayyukan duhu marasa-amfani.”—5:11

“Ku duba fa a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar [mutane] marasa-hikima ba.”—5:15.

“Amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi.”—5:15, 16.

“Domin wannan fa kada ku zama marasa wayo.”5:17.

“Amma ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.”—5:17.

“Kada ku yi maye da ruwan anab kuma-cikinsa da hauka.”—5:18.

“Amma ku cika da Ruhu.”—5:18.

“Domin [Kristi] shi miƙo wa kansa ikilisiya, ikilisiya mai-daraja, ba tare da aibi ko cira ko kowane abu misalin waɗannan.”—5:27.

“Amma ta zama mai-tsarki marar-aibi.”—5:27

“Babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa.”—5:29.

“Amma yakan ciyar da shi ya kuma kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma yakan yi da ikilisiya.”—5:29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba