TARIHI
Mun Yi Hidima a Duk Inda Aka Tura Mu
Ban taɓa yin wa’azi ni kaɗai ba. Duk sa’ad da na fita wa’azi, ƙafafuna suna rawa don tsoro. Kuma mutanen da ke yankin ba sa son saƙon ko kaɗan, wasu ma sukan fusata sosai kuma su yi barazanar dūka na. Na ba da ƙasida guda kawai a wata na farko da soma hidimar majagaba!—In ji Markus.
ABIN da na ambata a sama ya faru ne shekaru 60 da suka shige, wato a shekara ta 1949. Amma, labarina ya soma shekaru da yawa kafin wannan lokacin. Mahaifina mai suna Hendrik, mai yin takalma ne da kuma manomi a ƙaramin ƙauyen Donderen a arewancin Drenthe da ke ƙasar Nedalan. An haife ni a shekara ta 1927, kuma ni ne na huɗu a cikin yara bakwai. Gidanmu yana kusa da hanya a wani yankin karkara, kuma yawancin maƙwabtanmu manoma ne. Na ji daɗin noma sosai. A shekara ta 1947 sa’ad da nake ɗan shekara 19, wani maƙwabcinmu mai suna Theunis Been ya koya mini gaskiya daga Littafi Mai Tsarki. Ban so Theunis ba sa’ad da na fara haɗuwa da shi, amma da ya zama Mashaidi bayan Yaƙin Duniya na biyu, sai na lura cewa ya fi fara’a. Hakan ya burge ni sosai, kuma na saurare shi sa’ad da ya gaya mini game da alkawarin da Allah ya yi na mai da duniya aljanna. Sai na amince da abin da nake koya kuma muka zama aminai.a
Na soma wa’azi a watan Mayu na shekara ta 1948 kuma aka yi mini baftisma a ranar 20 ga Yuni, a wani taron gunduma da aka yi a babban garin Utrecht. Na soma hidimar majagaba a ranar 1 ga Janairu a shekara ta 1949, kuma aka tura ni yin hidima a ƙauyen Borculo da ke gabashin Nedalan, inda ake da wata ƙaramar ikilisiya. Tafiya zuwa ƙauyen mil 80 ne, saboda haka na tsai da shawara in je da kekena. Na ɗauka cewa tafiyar sa’o’i 6 ne kawai, amma na yi sa’o’i 12 domin ruwan sama da kuma iska da aka yi, kuma sai da na ƙarasa tafiyar mil 55 da jirgin ƙasa. A ƙarshe, na isa ƙauyen daddare sai na sauka a gidan wata iyalin Shaidu, kuma na zauna tare da su yayin da nake hidimar majagaba a yankin.
Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, mutane sun rasa abubuwan mallaka sosai. Ina da kwat guda da wanduna uku kawai, kwat ɗin ya yi mini yawa sosai kuma wandunan sun kasa ainun. Kamar yadda na ambata ɗazu, na sha wahala sosai a ƙauyen Borculo, amma Jehobah ya sa na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Bayan wata tara, sai aka tura ni hidima a birnin Amsterdam.
DAGA KARKARA ZUWA BIRNI
Ko da yake na girma a yankin da ake noma, amma na samu kaina a Amsterdam, wani birni mafi girma a ƙasar Holan. Mutane sun saurari saƙon sosai. A wata na farko, mutanen sun karɓi littattafanmu fiye da inda nake a dā. Ba daɗewa ba, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane takwas. Bayan da aka naɗa ni bawan ikilisiya (da yanzu ake kira mai tsara ayyukan rukunin dattawa) sai aka ba ni jawabina na farko. Tunanin ba da jawabin yana tsorata ni, shi ya sa na yi farin ciki sosai sa’ad da aka ce in ƙaura zuwa wata ikilisiya kafin ranar jawabin. Ban san cewa a nan gaba zan ba da jawabai fiye da 5,000 ba.
A watan Mayu na shekara ta 1950, sai aka ce in koma hidima a birnin Haarlem. A wurin ne aka ce in cika takardar soma hidimar mai kula da da’ira. Hakan ya sa ban iya barci ba har kwana uku. Sai na gaya wa wani ɗan’uwa mai suna Robert Winkler, da ke hidima a ofishin reshe cewa ba zan iya yin wannan hidimar ba. Amma ya ce: “Ka cika takardar kawai, za ka koya.” Jim kaɗan bayan haka, aka koyar da ni har wata guda kuma na soma hidimar mai kula da da’ira. Sa’ad da na kai ziyara a wata ikilisiya, sai na haɗu da Janny Taatgen wata ’yar’uwa majagaba mai fara’a, wadda take ƙaunar Jehobah sosai kuma mai halin sadaukarwa. Mun yi aure a shekara ta 1955. Bari in dasa aya a nan, don Janny ta bayyana yadda ta zama majagaba da kuma yadda muka haɗu.
YIN HIDIMA TARE
Janny: Mahaifiyata ta zama Mashaidiya a shekara ta 1945 sa’ad da nake ’yar shekara goma sha ɗaya. Ta fahimci cewa yana da muhimmanci ta yi nazari da yaranta uku, amma takan koyar da mu sa’ad da mahaifina ba ya gida domin ba ya son saƙon Littafi Mai Tsarki.
Taro na farko da na halarta shi ne taron gunduma da aka yi a birnin Hague a shekara ta 1950. Bayan sati ɗaya, sai na halarci taro a Majami’ar Mulki da ke birnin Assen a lardin Drenthe. Mahaifina ya fusata sosai kuma ya kore ni daga gida. Sai mahaifiyata ta ce, “Kin san inda za ki ko?” Na fahimci cewa tana nufin wurin ’yan’uwa Shaidu. Na koma zama da wata iyali Shaidu da ke kusa da gidanmu, amma mahaifina ya ci gaba da masa mini. Saboda haka, na ƙaura na koma ikilisiya da ke birnin Deventer a lardin Overijssel mai nisan mil 60 daga gidanmu. Amma da yake ni ƙaramar yarinya ce, sai mahaifina ya shiga uku da hukuma don ya kore ni daga gida. Saboda haka, sai ya ce in dawo gida. Ko da yake mahaifina bai zama Mashaidi ba, daga baya ya ƙyale ni in riƙa zuwa taro da kuma wa’azi.
Ba da daɗewa ba bayan na dawo gida, sai mahaifiyata ta soma rashin lafiya sosai kuma ni kaɗai ce ke yin aikace-aikacen gida. Duk da haka, na ci gaba da bauta wa Jehobah kuma aka yi mini baftisma a shekara ta 1951 sa’ad da nake ’yar shekara 17. A shekara ta 1952, mahaifiyata ta sami sauƙi, kuma na yi hidimar majagaba na ɗan lokaci na wata biyu tare da ’yan’uwa mata uku. Muna zama a jirgin ruwa da ake amfani da shi a matsayin gida kuma mukan yi wa’azi a garuruwa biyu a lardin Drenthe. Na soma hidimar majagaba na kullum a shekara ta 1953, kuma bayan shekara guda, wani ɗan’uwa matashi mai kula da da’ira mai suna Markus ya ziyarci ikilisiyarmu. Mun yi aure a watan Mayu na shekara ta 1955, domin muna ganin za mu fi bauta wa Jehobah sosai a matsayin mata da miji.—M. Wa. 4:9-12.
Markus: An tura mu yin hidima a matsayin majagaba a garin Veendam da ke lardin Groningen, bayan aurenmu. Muna zama a wani ƙaramin ɗaki da ke da tsawon ƙafa 7 da kuma faɗin ƙafa 10. Duk da haka, matata Janny ta sa ɗakin ya yi kyau sosai. Mukan tura teburinmu da ƙananan kujerunmu gefe ɗaya don mu saukar da gadonmu da ke jikin bango da dare.
Bayan wata shida, sai aka ce mu soma hidimar mai kula, mai ziyara a ƙasar Belgium. A shekara ta 1955, akwai masu shela kusan 4,000 a ƙasar, amma a yanzu sun fi 24,000! A yankin Flanders da ke arewacin ƙasar Belgium, mutane suna yare ɗaya da ’yan ƙasar Holan. Amma yadda ake yaren ’yan Belgium ya ɗan bambanta, saboda haka, muna bukatar mu koya yarensu.
Janny: Masu kula da da’ira suna bukatar su kasance da halin sadaukarwa. Mun ziyarci ikilisiyoyi da kekenmu kuma mun zauna a gidajen ’yan’uwa. Domin ba mu da masauƙi na kanmu, mukan kasance da su har ranar Litinin, kuma mu ziyarci wata ikilisiya a ranar Talata da safe. Amma muna ɗaukan hidimarmu a matsayin albarka daga Jehobah.
Markus: Ba mu waye ’yan’uwan da ke ikilisiyoyin ba, amma sun nuna mana alheri da karimci sosai. (Ibran. 13:2) Da shigewar lokaci, mun ziyarci dukan ikilisiyoyin yaren Dutch a ƙasar Belgium sau da yawa. Hakan ya sa mun samu albarka sosai. Alal misali, mun san kusan dukan ’yan’uwa da ke yankin da ake yaren Dutch, kuma sun zama abokanmu na kud da kud. Mun ga matasa da yawa da suka girma, suka keɓe kansu ga Jehobah kuma suna saka al’amura ta Mulki farko a rayuwarsu. Muna farin ciki sosai da yake da yawa a cikinsu suna hidima ta cikakken lokaci da kuma bauta wa Jehobah da aminci. (3 Yoh. 4) Wannan “ƙarfafawa” ta sa ya yi mana sauƙi mu ci gaba a hidimarmu da zuciya ɗaya.—Rom. 1:12.
ƘALUBALE DA KUMA ALBARKA
Markus: Tun ranar da muka yi aure, muna sha’awar zuwa Makarantar Gilead. A kowace rana, mukan yi aƙalla sa’a guda muna koyon Turanci. Amma ba shi da sauƙi a koyi Turanci daga littattafai, saboda haka, muka tsai da shawara mu tafi Ingila a lokacin hutu don mu yi yaren sa’ad da muke wa’azi a wajen. A ƙarshe, mun sami wasiƙu biyu daga hedkwatarmu da ke Brooklyn a shekara ta 1963, ɗaya tawa ce ɗayan kuma ta matata ce. Tawa wasiƙar gayyata ce zuwa Makarantar Gilead ta musamman da za a yi wata goma. A makarantar, za a mai da hankali musamman ga horar da ’yan’uwa maza da kuma koya musu tsarin ƙungiyar. Saboda haka, a cikin ’yan’uwa 100 da aka gayyata, 82 maza ne.
Janny: A cikin wasiƙa da aka aiko mini, an ce in tsai da shawara ko zan yarda in zauna a ƙasar Belgium sa’ad da mijina ya tafi Makarantar Gilead. Da farko, na ji kamar Jehobah bai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen da nake yi don in daɗa ƙwazo a bautarsa ba, kuma hakan ya sa ni sanyin gwiwa sosai. Amma na tuna wa kaina cewa an kafa Makarantar Gilead ne don a taimaka wa ɗaliban su yaɗa bishara a dukan duniya. Sai na amince in zauna a ƙasar Belgium kuma aka tura ni hidimar majagaba na musamman a birnin Ghent tare da wasu ƙwararrun majagaba na musamman, wato Anna da Maria Colpaert.
Markus: An ce in je in yi hidima na wata biyar a hedkwatarmu da ke Brooklyn, don in daɗa koyon Turanci kafin a soma makarantar. Na yi aiki a sashen tura littattafai zuwa ikilisiyoyi da kuma Sashen Hidima. Yin hidima a hedkwatarmu da kuma taimaka wajen tura littattafai zuwa ƙasar Asiya da Turai da kuma Amirka ta Kudu ya sa na ƙara sani game da ’yan’uwanmu da ke dukan duniya. Na tuna musamman da Ɗan’uwa Alexander Hugh Macmillan da ya yi hidimar mai kula mai ziyara a zamanin Ɗan’uwa Russell. A lokacin ya tsufa kuma ba ya ji sosai, duk da haka yana halartan dukan taron ikilisiya. Hakan ya koya mini cewa ya kamata mu riƙa ɗaukan halartan taro da muhimmanci.—Ibran. 10:24, 25.
Janny: Ni da mijina muna rubuta wa juna wasiƙa sau da yawa a mako. Mun yi kewar juna sosai. Duk da haka, mijina ya ji daɗin koyarwa da aka yi masa a Gilead, kuma na ji daɗin hidimata. Ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 17 sa’ad da mijina ya dawo daga Amirka. Rashin kasancewa tare na shekara da wata uku ƙalubale ne sosai a gare ni, amma na ga cewa Jehobah ya albarkace mu don sadaukarwa da muka yi. Jirgin da mijina ya shiga a ranar da ya dawo bai tashi da wuri ba. Sa’ad da ya iso gida, mun rungumi juna muna ta kuka. Tun daga lokacin, ba mu sake rabuwa da juna ba.
MUNA HAMDALA DON KOWACE IRIN HIDIMA
Markus: Sa’ad da na dawo daga Makarantar Gilead a watan Disamba na shekara ta 1964, an tura mu yin hidima a Bethel. Amma, ba mu san cewa za mu ƙara barin hidimar Bethel ba. Bayan wata uku, sai aka tura mu hidimar mai kula da gunduma a yankin Flanders. Sa’ad da aka tura wani mai kula da gunduma da matarsa yin hidima a ƙasar Belgium, sai aka komar da mu Bethel inda na yi aiki a Sashen Hidima. Mun yi hidimar mai kula da da’ira da gunduma da kuma a Bethel tsakanin shekara ta 1968 zuwa 1980, hakan ya ƙunshi yin hidima a Bethel da kuma na mai kula mai ziyara. A ƙarshe, na sake yin hidimar mai kula da gunduma daga shekara ta 1980 zuwa 2005.
Ko da yake an canja hidimarmu sau da yawa, ba mu manta ba cewa mun keɓe kanmu ga Jehobah don mu bauta masa da dukan ranmu. Mun ji daɗin kowace irin hidima da muka yi, kuma mun tabbata cewa duk inda aka ce mu yi hidima don ci gaban al’amura na Mulki ne.
Janny: Na ji daɗin gatan zuwa Brooklyn tare da mijina a shekara ta 1977 da kuma Patterson a shekara ta 1997 inda ya samu ƙarin koyarwa a matsayin wanda yake cikin Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe.
JEHOBAH YA SAN DA BUKATUNMU
Markus: A shekara ta 1982, an yi wa matata fiɗa kuma ta samu sauƙi sosai. Bayan shekara uku, ’yan’uwa a ikilisiyar da ke birnin Louvain suka ba mu masaukin da ke Majami’ar Mulkin. Tun shekaru 30 da suka shige, wannan shi ne ɗaki na kanmu da muka taɓa samu. A ranar Talata, sa’ad da muka kintsa don mu ziyarci wata ikilisiya, nakan hawa da sauka sau da yawa don in kai kayanmu ƙasa! Amma, mun yi farin ciki sa’ad da aka shirya mana wani ɗaki a ƙasa. Sa’ad da na zama ɗan shekara 78, sai aka tura mu hidimar majagaba na musamman a garin Lokeren da ke lardin Flanders. Muna farin ciki sosai don wannan hidimar, kuma muna fita wa’azi kullum.
“Mun san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne wanda muke wa hidima, ba inda muke hidima ba”
Janny: Idan aka haɗa shekarun da ni da mijina muka yi hidima, za su kai 120. Mun ga cikar alkawarin da Jehobah ya yi cewa ‘daɗai ba ni yashe ka ba,’ kuma cewa idan muka bauta masa da aminci, ba abin da za mu rasa.—Ibran. 13:5; K. Sha 2:7.
Markus: Mun keɓe kanmu ga Jehobah tun muna ƙanana. Ba mu taɓa biɗan abubuwan mallaka ba. Mun kasance a shirye mu yi kowace irin hidima da aka ce mu yi don mun san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne wanda muke wa hidima, ba inda muke hidima ba.
a Da shigewar lokaci, mahaifina da mahaifiyata da yayata da ƙannena biyu suka zama Shaidu.