Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/15 p. 32
  • “Wannan Hoton Yana da Kyau!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Wannan Hoton Yana da Kyau!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Mu Dinga Karfafa Juna a Taron Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Koyi Darasi Daga Hotuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/15 p. 32

“Wannan Hoton Yana da Kyau!”

Sau nawa ne ka taɓa furta waɗannan kalmomin ga kanka ko kuma ga wani sa’ad da ka buɗe sabuwar mujalla? Akwai dalilan da suka sa aka saka hotuna da zane-zane a cikin mujallun. Suna taimaka mana mu yi tunani. Suna taimaka mana sosai sa’ad da muke shiri da kuma ba da kalami a Nazarin Hasumiyar Tsaro.

Alal misali, ka yi tunani a kan dalilin da ya sa aka saka wani hoto a cikin talifin Hasumiyar Tsaro na nazari. Me yake nunawa? Yaya yake da nasaba da jigon talifin ko kuma nassin jigon? Ka yi tunani a kan yadda ya shafi batun da ake tattaunawa da kuma rayuwarka.

Mai gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro zai ba ’yan’uwa damar yin kalami a kan kowane hoto. Zai ce su faɗi darasin ko yadda ya shafe su. A wasu lokatai, ana rubuta kalmomin da za su nuna sakin layin da hoton ke bayyanawa. A wasu lokatai kuma, mai gudanar da nazarin zai tsai da shawara a kan sakin layin da ya dace a tattauna hoton. Da hakan, kowa zai amfana sosai daga tanadin da aka yi mana don mu fahimci darussan da ke cikin Kalmar Allah.

Wani ɗan’uwa ya ce, “Bayan ka gama karanta wani talifi mai daɗi sosai, hotunan suna kamar romo a cikin nama.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba