Kada Ka Taɓa Ja da Baya!
Kai Mashaidin Jehobah ne shekaru da yawa kuma kana son matarka ta bauta wa Jehobah tare da kai?
Ko kuma ka yi sanyin gwiwa don wanda kake nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma kake ganin ba da daɗewa ba, zai soma bauta wa Jehobah amma ya ƙi yin hakan?
Wasu labarai daga ƙasar Britaniya za su taimaka maka ka ga dalilin da ya sa ba za ka taɓa ja da baya ba. Za ka koya abin da za ka iya yi don ka samu sakamako mai kyau a hidimarka, domin ka taimaka wa waɗanda ba su soma bauta wa Jehobah ba tukuna.—M. Wa. 11:1.
AMFANIN JIMREWA
Wani abu mai muhimmanci da za ka yi shi ne jimrewa. Kana bukatar ka ci gaba da bauta wa Jehobah kuma ka dogara a gare shi. (K. Sha 10:20) Abin da Georgina ta yi ke nan. Mijinta Kyriacos, ya yi fushi sosai sa’ad da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a shekara ta 1970. Ya yi ƙoƙari ya sa ta daina nazarin, ba ya barin Shaidu su shiga gidansu, kuma ya ƙwace duk littattafan Shaidun Jehobah da ya samu a hannunta.
Mijin Georgina ya fusata sosai sa’ad da ta soma halartan taron ikilisiya. Wata rana, sai ya tafi Majami’ar Mulki don ya ta da rigima. Amma, sa’ad da wata ’yar’uwa ta lura cewa Kyriacos yana jin Helenanci fiye da Turanci, sai ta kira wani ɗan’uwa Baheleni daga wata ikilisiya don ya zo ya taimaka. Don halin kirkin ɗan’uwan, Kyriacos ya saurari saƙon, kuma suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare na ’yan watanni. Amma, daga baya sai ya daina nazari.
Georgina ta ci gaba da fuskantar hamayya har na tsawon shekara uku. Mijinta ya ce zai sake ta idan ta yi baftisma. A ranar da za ta yi baftisma, sai Georgina ta yi addu’a ga Jehobah don kada ya sake ta. Sa’ad da Shaidu suka isa gidansu don su tafi taron da’ira tare, mijinta ya gaya musu: “Ku je, za mu bi ku a baya da motarmu.” Ya halarci sashe na safe, kuma ya ga sa’ad da ake wa matarsa baftisma.
Bayan hakan, sai mijinta ya rage tsananta mata, kuma a hankali ya yi canje-canje a rayuwarsa. Georgina ta yi farin cikin sosai, sa’ad da mijinta ya yi baftisma bayan kusan shekara 40 da Shaidu suka yi mata wa’azi. Mene ne ya taimaka wa Kyriacos? Ya ce: “Na yi farin ciki cewa Georgina ba ta ƙyale kome ya hana ta bauta wa Jehobah ba.” Georgina ta ce: “Ko da yake mijina yana tsananta mini, na ƙudura niyya ba zan taɓa daina bauta wa Allahna ba. Na ci gaba da yin addu’a ga Jehobah, kuma na kasance da bege.”
AMFANIN CANJA HALAYENMU
Wani abu kuma da zai taimaka wa matarka ko mijinki shi ne kasancewa da halin kirki. Manzo Bitrus ya ba mata gargaɗi: “Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu.” (1 Bit. 3:1) Christine ta bi wannan gargaɗin ko da yake mijinta ya yi shekaru da yawa kafin ya soma bauta wa Jehobah. Sa’ad da ta zama Mashaidiya fiye da shekara 20 da ta shige, mijinta John bai yi imani da Allah ba. John ba ya son ya bi addini, amma ya fahimci cewa addinin Christine yana da muhimmanci sosai a gare ta. Ya ce: “Na lura cewa addinin na sa matata farin ciki, ta zama wadda ta fi kasancewa da ƙarfin zuciya, kuma wannan ya taimaka mini sosai na jimre da yanayi mai wuya.”
Christine ba ta taɓa tilasta wa mijinta ya soma bin addininta ba. Mijinta ya ce: “Tun daga farko, Christine ta fahimci cewa ya fi kyau kada ta yi mini magana game da addininta, kuma cikin haƙuri ta ƙyale ni na koyi gaskiya yadda na ga dama.” Idan Christine ta ga wasu talifofin Hasumiyar Tsaro ko Awake! da ta san cewa mijinta John zai so ya karanta, kamar waɗanda suka yi magana a kan ilimin kimiyya da labaran halitta, sai ta nuna masa kuma ta ce, “Na san za ka ji daɗin karanta wannan talifin.”
Da shigewar lokaci, sai John ya yi ritaya kuma ya soma aikin lambu. Yanzu ya samu ƙarin lokacin yin tunani a kan tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa, kamar ‘Shin an halicci ’yan Adam ne, ko kuma sun soma wanzuwa ne haka kawai?’ Wata rana da John yake tattaunawa da wani ɗan’uwa, sai ɗan’uwan ya tambaye shi, “Za ka so a yi nazari da kai?” John ya ce: “Yanzu da na soma yin imani ga Allah, na amince a yi nazari da ni.”
Yana da muhimmanci cewa Christine ba ta fid da rai ba! John ya yi baftisma bayan shekara 20 da matarsa ta riƙa yin addu’a ya soma bauta wa Jehobah. Yanzu suna bauta wa Jehobah tare. John ya ce: “Abubuwa biyu ne suka sa na soma bauta wa Jehobah. Alheri da kuma fara’ar da Shaidu suka nuna mini. Mutumin da ya auri Mashaidiya, ya auri mace mai aminci kuma marar son kai da zai iya dogara da ita.” Hakika, Christine ta bi gargaɗin da ke cikin 1 Bitrus 3:1, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu!
SUNA IYA SAMUN CI GABA A NAN GABA
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suka daina son saƙon kuma fa? Sarki Sulemanu ya ce: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” (M. Wa. 11:6) A wasu lokatai, yakan ɗauki shekaru da yawa kafin ɗaliban su samu ci gaba. Amma, daga baya za su fahimci muhimmancin kusantar Allah. (Yaƙ. 4:8) Hakika, wata rana za ka yi mamakin cim ma burinka.
An soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Alice a shekara ta 1974, bayan ta ƙaura daga Indiya zuwa Ingila. Ta iya yaren Hindi amma tana son ta ƙware a Turanci. Alice ta ci gaba da nazari shekaru da yawa, kuma ta halarci taron ikilisiya da ake yi da Turanci. Ta san cewa tana koyon gaskiya, amma ba ta ɗauke shi da muhimmanci ba. Ban da ma haka, tana son kuɗi da kuma fati. Sai Alice ta daina nazari.
Bayan shekara 30, Alice ta rubuta wasiƙa zuwa ga Stella wadda take nazari da ita a dā. Ta ce: “Na san za ki yi farin ciki cewa wadda kika yi nazari da ita a shekara ta 1974 ta yi baftisma a taron gunduma da aka yi kwanan baya. Kin taimaka mini sosai a rayuwa. Kin koya mini gaskiya, kuma ban manta da abin da kika koya mini ba ko da yake a lokacin, ban so keɓe kaina ga Allah ba.”
Mene ne ya faru? Alice ta bayyana cewa ta yi baƙin ciki sosai bayan mutuwar mijinta a shekara ta 1997. Ta yi addu’a ga Allah. Minti goma bayan haka, sai Shaidu biyu masu yaren Punjabi suka kawo mata ziyara kuma suka ba ta warƙar nan Wane Bege Ƙaunatattu da Suka Mutu Suke da Shi? Alice tana ganin cewa Allah ya ji addu’arta kuma ta tsai da shawara ta soma tarayya da Shaidun Jehobah kuma. Amma, matsalar ita ce ba ta san inda za ta same su kuma ba. Sai ta ga adireshin ikilisiyar da ake yaren Punjabi da Stella ta ba ta a dā. Alice ta halarci taron, kuma ’yan’uwa da ke cikin ikilisiyar suka marabce ta sosai. Alice ta ce: “Yadda suka marabce ni da kuma ƙaunace ni ya taimaka mini in samu sauƙi daga baƙin ciki da nake yi.”
Ta soma halartar taro a kai a kai kuma aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Daga nan, ta koya karanta da kuma yin yaren Punjabi da kyau. An yi mata baftisma a shekara ta 2003. Ta kammala wasiƙar da ta aika wa Stella, cewa, “Na gode miki sosai da kika koya mini gaskiya shekaru 29 da suka shige da kuma misali mai kyau da kika kafa mini.”
“Na gode miki sosai da kika koya mini gaskiya shekaru 29 da suka shige da kuma misali mai kyau da kika kafa mini.”—Alice
Mene ne za ka iya koya daga waɗannan misalan? Idan mutum yana son ya san Allah kuma yana da zuciyar kirki da kuma tawali’u, Jehobah zai taimaka masa ya fahimci gaskiya kuma ya amince da shi, ko da yake hakan zai iya ɗaukan lokaci. Ka tuna da abin da Yesu ya ce a kwatancin da ya yi: “Iri kuma ya tsira ya yi girma, shi kuwa [mai shukin] ba ya san yadda ya ke yi ba. Ƙasa tana ba da amfani don kanta, soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da ƙwaya nunanna a ciki.” (Mar. 4:27, 28) Irin yana girma da kansa a hankali, kuma hakan yakan ɗauki lokaci. Hakan yana nufin cewa kowane mai shelar Mulki bai san yadda wannan zai faru ba. Saboda haka, ka ci gaba da yin shuki da ƙwazo. Za ka samu amfani sosai.
Kuma kada ka mance da muhimmancin yin addu’a. Georgina da Christine sun ci gaba da yin addu’a ga Jehobah. Idan ka “lizima cikin addu’a” kuma ka kasance da bege, “bayan kwanaki dayawa” za ka ga cewa aikinka zai kawo sakamako mai kyau.—Rom. 12:12; M. Wa. 11:1.