Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/15 p. 29
  • Shin Josephus Ne Ya Rubuta?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Josephus Ne Ya Rubuta?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yohanna mai Baftisma ya Taba Wanzuwa Kuwa?
    Karin Batutuwa
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/15 p. 29

Shin Josephus Ne Ya Rubuta?

A cikin littafin da wani ɗan tarihi mai suna Flavius Josephus ya rubuta, ya ambata mutuwar “Yaƙub, ɗan’uwan Yesu wanda ake irin Kristi.” Masana da yawa sun ce wannan furucin gaskiya ne. Amma, wasu sun yi shakkar wani furucin da aka rubuta a cikin wannan littafin game da Yesu. Wannan furucin da ake kira Testimonium Flavianum, ya ce:

“Akwai wani mutumi mai hikima, sunansa Yesu, idan ya dace a kira shi mutum, domin yana yin ayyuka masu ban al’ajabi. Mutane da yawa suna jin daɗin sauraron koyarwarsa. Ya rinjayi Yahudawa da ’Yan Al’ummai da yawa. Shi Kristi ne, kuma sa’ad da Bilatus ya ce a giciye shi, waɗanda suke ƙaunarsa tun da farko sun ci gaba da yin haka. Sa’ad da ya tashi bayan kwana uku, ya sake bayyana a gabansu kamar yadda annabawa suka annabta. An kuma annabta wasu abubuwa masu ban al’ajabi guda dubu goma game da shi. Kuma har yau, ba a halaka Kiristoci da aka samo sunansu daga Kristi ba.”—Littafin Josephus—The Complete Works, wanda William Whiston ya fassara.

Mutanen da suka gaskata cewa Josephus ne ya rubuta wannan littafin da waɗanda ba su yarda ba, sun yi darurruwan shekaru suna ta cin mūsu a kan wannan batun. Wani Ba’faranse ɗan tarihi da kuma gwanin adabi, mai suna Serge Bardet ya nemi ya warware wannan mūsun da an daɗe ana yi. Ya wallafa binciken da ya yi a cikin littafi mai jigo Le Testimonium Flavianum—Examen historique considérations historiographiques.

Josephus ba Kirista ba ne. Shi Bayahude ne kuma yana rubuta tarihin Yahudawa. Amma, abin da ya jawo mūsu sosai shi ne yadda ya kira Yesu “Kristi.” Binciken da Bardet ya yi, ya nuna cewa wannan laƙabin ya jitu da yadda Helenawa suke ambata sunan mutane. Daɗin daɗawa, Josephus ya ambata “Kristi” wataƙila domin da yaren Helas ne ya rubuta littafin. Kuma a Helenanci, gama gari ne a ambata sunan mutum hakan. Yin hakan ba abin mamaki ba ne, amma, alama ce cewa Yesu sananne ne. Ya kamata masu sūkar Littafi Mai Tsarki su san da hakan tun da daɗewa.

Shin wani ne ya daɗa gishiri a littafin da Josephus ya rubuta shekaru da yawa bayan mutuwarsa? Bardet ya ambata tarihi da kuma fasalin rubutun Josephus, don bayyana cewa yin hakan ba zai yiwu ba. Ba zai taɓa yiwu a samu wani a zamanin dā, da zai iya kwaikwayon fasalin rubutun Josephus ba.

To, me ya sa masana suke shakkar wannan furucin? Bardet ya ce, masana da yawa sun yi shakkar wannan furucin Josephus fiye da wasu rubuce-rubuce na zamanin dā, domin yawancinsu ba sa son su gaskata cewa Yesu ne Kristi.

Ana nan ana ta sa ido a ga ko binciken da Bardet ya yi game da wannan furucin Josephus zai canja ra’ayin masana. Wani ƙwararren ɗan tarihin Helenawa da Yahudawa da kuma Kiristanci na dā mai suna Pierre Geoltrain, ya amince da wannan binciken da Bardet ya yi. Ya daɗe yana gaskata cewa an ƙara gishiri a wannan furucin, kuma yana wa waɗanda suka gaskata da furucin ba’a. Amma, ya canja ra’ayinsa. Yanzu, ya amince da binciken da Bardet ya yi. Pierre Geoltrain ya ce kada kowa ya kuskura ya yi sūkar littafin da Josephus ya rubuta kuma.

Hakika, Shaidun Jehobah suna da ƙwaƙƙwarar dalili na gaskata cewa Yesu ne Kristi. Kuma wannan dalilin yana cikin Littafi Mai Tsarki.—2 Tim. 3:16.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba