Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 1/15 pp. 3-6
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Ƙasar Norway

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Ƙasar Norway
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TAMBAYAR DA BA MU YI TSAMMANI BA
  • WANE ZAƁI NE ZA SU YI?
  • MATAKAN DA SUKA ƊAUKA
  • YADDA WASU SUKA DAƊA ƘWAZO A HIDIMARSU
  • ‘KA ƊANƊANA, KA DUBA, UBANGIJI NAGARI NE’
  • Yin Shiri Sosai Kwalliya Ce da ke Biyan Kuɗin Sabulu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ta Yaya Za Ka Yi Addu’a Kuma Allah Ya Amsa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—a Madagaska
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 1/15 pp. 3-6

Sun Ba Da Kansu Da Yardar Rai​—A Ƙasar Norway

WANI ɗan’uwa mai suna Roald da matarsa Elsebeth ’yan kusan shekara 50 ne kuma suna zama a Bergen, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a ƙasar Norway. Kuma suna zaman jin daɗi a wannan birnin. Suna saka hannu sosai a ayyuka na ikilisiyarsu tare da ’yarsu Isabel da ɗansu Fabian. Roald dattijo ne a cikin ikilisiya kuma matarsa majagaba ce. Yaransu kuma masu shela ne, kuma suna da ƙwazo sosai.

Amma, ka san shawarar da wannan iyalin ta yanke a watan Satumba na 2009? Za su je wani yanki mai nisa sosai don yin wa’azi na mako guda. Roald da matarsa tare da ɗansu Fabian wanda ɗan shekara 18 ne a lokacin sun je wani garin Nordkyn da ke ƙasar Finnmark. Sun yi wa’azi tare da wasu ’yan’uwa da su ma suka zo yin wa’azi a ƙauyen Kjøllefjord. Roald ya ce: “A farkon makon, na yi matuƙar farin ciki cewa na yanke shawarar yin hidima na mako guda a wurin.” Amma, kafin ƙarshen mako, wani abu ya faru da ya dame Roald sosai. Ka san abin da ya faru?

TAMBAYAR DA BA MU YI TSAMMANI BA

Roald ya ce: “Wani majagaba da ke hidima a ƙasar Finnmark mai suna Mario, ya tambaye mu ko za mu so mu ƙaura zuwa wani garin da ke ƙasar don mu taimaka a wata ikilisiya da akwai masu shela 23.” Wannan tambayar ta ba ni mamaki sosai domin ban yi zato ba. Ya daɗa: “Ni da matata mun taɓa tattauna ko zai yiwu mu yi hidima a inda ake da bukata sosai, amma mun ce za mu yi hakan bayan yaranmu sun yi girma kuma sun bar gida.” Amma duk da haka, a ’yan kwanakin da Roald ya yi wa’azi a wannan yankin, ya lura cewa mutane suna ɗokin koyo game da Jehobah. Suna bukatar taimako yanzu, ba an jima ba. Roald ya ce: “Tambayar ta dame ni sosai, kuma ya hana ni barci kwanaki da yawa.” Sai Mario ya tuƙa Roald da iyalinsa zuwa garin Lakselv, wanda ke da nisan mil 150 daga kudancin Kjøllefjord. Yana son su ga ikilisiyar da idanunsu.

Sa’ad da suka isa garin, sai Andreas wanda dattijo ne a wurin, ya zagaya da su garin da kuma Majami’ar Mulkin. ’Yan’uwan da ke ikilisiyar sun marabce su sosai, kuma suka gaya wa Roald da matarsa cewa za su yi farin ciki sosai idan suka ƙaura zuwa garin don su taya su yin wa’azi. Sai dattijon ya yi murmushi, kuma ya ce ya riga ya shirya wa Roald da ɗansa intabiyun aiki. Mene ne waɗannan baƙin za su yi?

WANE ZAƁI NE ZA SU YI?

Abin da Fabian ya fara cewa shi ne: “Ba zan iya ƙaura zuwa garin nan ba.” Bai ji daɗi ba cewa zai bar abokansa da suka yi girma tare a cikin ikilisiya kuma ya ƙaura zuwa wani ƙaramin gari. A lokacin, yana koyan aikin lantarki kuma bai kammala ba tukun. Amma, sa’ad da aka tambayi Isabel wadda ’yar shekara 21 ce a lokacin ko za ta so ta ƙaura, sai ta ce: “Ainihin abin da nake neman zarafin yi ke nan.” Daɗin daɗawa, sai ta ce: “Sa’ad da na daɗa yin la’akari sosai, sai na soma mamaki ko zai dace na ƙaura zuwa wannan garin. Shin zan yi kewar ƙawayena? Zai fi dacewa na zauna kurum a ikilisiyarmu inda abubuwa suka fi sauƙi?” Yaya matar Roald ta ji game da wannan gayyatar? Ta ce: “Na soma ji cewa Jehobah ya ba iyalinmu aiki. Amma, na kuma yi tunani game da gidanmu da muka gyara kwana kwanan nan da kuma dukan abubuwan da muka yi shekara 25 muna tarawa.”

Bayan wannan mako guda, sai Roald da iyalinsa suka koma gida, amma ba su daina tunani game da waɗannan ’yan’uwan da ke garin Lakselv mai nisan mil 1,300 da gidansu ba. Matar Roald ta ce: “Na yi addu’a sosai ga Jehobah. Na kuma ci gaba da abokantaka da ƙawayen da na yi a garin ta wajen aika musu hotuna da kuma labarai.” Roald ya ce: “Ina bukatar ɗan lokaci don na amince da wannan gayyatar. Kuma na yi la’akari da yadda za mu biya bukatunmu a garin. Na yi addu’a sosai ga Jehobah, kuma na tattauna da ’yan’uwan da suka manyanta.” Ɗansu Fabian ya ce: “Sa’ad da na daɗa yin la’akari sosai, sai na ankara cewa ba ni da hujjar ƙin wannan gayyatar. Na yi addu’a sau da yawa ga Jehobah, sai da sannu-sannu na soma marmarin ƙaura zuwa wannan garin.”’Yarsu Isabel kuma fa? Ta soma hidimar majagaba, don ƙaura zuwa wannan garin ya yi mata sauƙi. Bayan wata shida da yin wannan hidimar da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, sai ta yi na’am da wannan gayyatar.

MATAKAN DA SUKA ƊAUKA

Sa’ad da iyalin suka soma marmarin ƙaura zuwa inda ake da bukata sosai, sai suka ɗauki wasu matakai don su cim ma burinsu. Roald yana aikin da ake biyansa albashi mai tsoka sosai, amma sai ya ce a ba shi hutu na shekara guda. Sai shugaban aikinsa ya ce ya riƙa aiki na ɗan lokaci. Zai riƙa aiki mako biyu, sai ya yi hutu na mako shida. Roald ya ce: “An rage albashina sosai, amma kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu.”

Elsebeth ta ce: “Maigidana ya ce na nemi gida a garin Lakselv, kuma na ba da hayar gidanmu da ke birnin Bergen. Yin hakan ba cin tuwo ba ne, amma mun yi nasara. Ba da daɗewa ba, yaranmu suka samu aiki na ɗan lokaci, kuma suna biyan bukatunmu na abinci da sufuri.”

’Yarsu Isabel ta ce: “Tun da garin bai da girma, abin da ya fi ci mini tuwo a ƙwarya shi ne samun aikin da zai sa na riƙa biyan bukatuna a matsayin majagaba. A wasu lokatai, abin bai zo mini da sauƙi ba.” Amma duk da haka, ta yi aiki na ɗan lokaci guda tara da ta samu a farkon shekarar da suka ƙaura zuwa wannan garin. Yin hakan ya sa ta biya bukatunta. Ɗansu Fabian kuma fa? Ya ce: “Na kammala aikin da nake koya a garin Lakselv. Daga baya, na ci jarabawa na kuma na samu aikin gyaran lantarki na ɗan lokaci.”

YADDA WASU SUKA DAƊA ƘWAZO A HIDIMARSU

Marelius da matarsa Kesia, suna son su yi hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Marelius wanda shi ɗan shekara 29 ne yanzu ya ce: “Jawabai da ganawa da aka yi a taron gunduma game da yin hidimar majagaba ya ƙarfafa ni. Sun sa na yi la’akari da yadda zan iya daɗa ƙwazo a hidimata.” Amma, rabuwa da dangi bai yi wa matarsa Kesia wadda ’yar shekara 26 ce yanzu sauƙi ba. Ta ce: “Na ƙi jinin zama a wuri mai nisa daga dangina.” Bugu da ƙari, Marelius yana aiki na cikakken lokaci don ya biya bukatunsu. Ya ce: “Mun yi addu’a sosai ga Jehobah cewa ya taimaka mana mu yi canje-canje, kuma ya taimaka mana mu ƙaura.” Da farko, sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Sai suka sayar da gidansu, suka yi murabus da aikinsu, kuma suka ƙaura zuwa birnin Alta da ke arewancin ƙasar Norway a watan Agusta na 2011. Wane aiki za su riƙa yi don su biya bukatunsu a matsayin majagaba? Marelius ya soma aikin akanta kuma matarsa tana aiki a wani shago.

Knut da matarsa Lisbeth ma’aurata ne da suka yi wa shekara 34 baya. Abin da suka karanta a cikin littafin Yearbook game da waɗanda suke hidima a inda ake da bukatar masu shela sosai ya burge su. Matarsa ta ce: “Abin da muka karanta ya sa mu soma yin la’akari ko za mu iya hidima a wata ƙasa. Amma, na yi jinkiri domin ina tunani hakan ya fi ƙarfi na.” Duk da haka, sun ɗauki matakai don su cim ma burinsu. Knut ya ce: “Muka sayar da gidanmu, kuma muka soma zama tare da mahaifiyata domin mu rage kashe kuɗi. Domin mu ɗan gwada yadda yin hidima a wata ƙasa take, sai muka ƙaura zuwa ikilisiyar da ake Turanci a birnin Bergen na tsawon shekara guda. A wannan birnin, muka zauna tare da mahaifiyar matata.” Ba da daɗewa ba, sai suka tsai da shawara cewa za su ƙaura zuwa wata ƙasa. Amma, ka san ƙasar da suka zaɓa? Ƙasar Yuganda. Sukan koma ƙasar Norway na tsawon wata biyu a shekara don su yi aiki. Da hakan, suna samun isashen kuɗin da za su biya bukatunsu kuma su yi wa’azi na cikakken lokaci a ƙasar Yuganda.

‘KA ƊANƊANA, KA DUBA, UBANGIJI NAGARI NE’

Waɗanne sakamako ne waɗannan ’yan’uwa suka samu? Roald ya ce: “Muna kasancewa tare sosai a matsayin iyali a wannan garin, fiye da yadda muka yi a birnin Bergen. Kuma dangantakarmu ta yi danko sosai. Ina matuƙar farin ciki don yadda yaranmu suke samun ci gaba a bautarsu ga Jehobah.” Daɗin daɗawa: “Kuma yanzu, ba ma neman kuɗi ruwa a jallo. Ba ma ɗaukansa da muhimmanci kamar dā.”

Elsebeth ta ga cewa tana bukatar ta koyi wani yare. Don me? Ƙauyen Karasjok yana yankin Ikilisiyar Lakselv kuma suna yaren Sami. Mutanen ƙauyen su ne asalin ’yan arewancin ƙasar Norway da Sweden da Finland da kuma Rasha. Domin Elsebeth ta samu sauƙin tattaunawa da waɗannan mutanen, sai ta soma koyon yarensu. A yanzu haka, tana iya ɗan tattaunawa da yaren. Shin Elsebeth tana jin daɗin sabon yankinta kuwa? Ta ce cike da murna: “Ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane shida. A wane wuri kuma zan kasance idan ba nan ba?”

Ɗansu Fabian wanda majagaba da kuma bawan mai hidima ne yanzu, ya ce shi da yarsa Isabel sun ƙarfafa matasa uku a sabuwar ikilisiyarsu su daɗa ƙwazo. Yanzu haka, dukansu uku suna yin wa’azi da himma sosai. Biyu cikinsu sun yi baftisma, kuma sun yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Maris na shekara ta 2012. Ɗaya cikinsu da ta soma bijirewa daga ƙungiyar Jehobah, ta gode wa Fabian da Isabel sosai don yadda suka taimaka mata ta sake yin ƙwazo. Fabian ya ce: “Na yi farin ciki sosai sa’ad da ta ce hakan.” Isabel ta ce: “Hakika, a wannan hidimar, na ‘ɗanɗana, na duba, cewa ubangiji nagari ne.’” (Zab. 34:8) Ta daɗa cewa: “Bauta wa Jehobah yana da daɗi sosai.”

A yanzu, Marelius da Kesia sun sauƙaƙa salon rayuwarsu, kuma rayuwarsu ta fi ma’ana. Akwai masu shela 41 yanzu a sabuwar ikilisiyarsu a garin Alta. Marelius ya ce: “Ina murna sosai domin yadda salon rayuwarmu ta canja. Muna godiya ga Jehobah domin muna masa hidima a matsayin majagaba. Babu abin da ya fi hakan sa mutum wadar zuci.” Kesia ta ce: “Na koya in dogara baki ɗaya ga Jehobah. Kuma yana kula da ni sosai. A yanzu da ba ma zama kusa da dangina, na fi daraja dangantakata da su. Ban taɓa yin da-na-sani ba.”

Yaya Knut da matarsa Lisbeth sun ji da zama a ƙasar Yuganda? Knut ya ce: “Ya ɗan ɗauki lokaci kafin mu saba da ƙasar da kuma al’adarsu. Muna yawan rashin ruwa da wutan lantarki da kuma ciwon ciki, amma muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane har ya ishe mu.” Lisbeth ta ce: “Akwai yankunan da ke kusa da gidanmu da ba a taɓa yin wa’azi ba. Duk da hakan, a lokacin da muka ziyarce su, mun tarar da mutane suna karanta Littafi Mai Tsarki, kuma suka ce mu yi nazari da su. Muna farin ciki sosai don yin nazari da waɗannan mutane masu sauƙin kai.”

Babu shakka, Ubangijinmu Yesu Kristi wanda ya soma wa’azi, yana farin ciki sa’ad da ya lura daga sama, kuma ya ga yadda ake samun ƙaruwa sosai a bishara. Hakika, bayin Jehobah suna matuƙar farin cikin ba da kansu da yardar rai don bin umurnin Yesu na “ku almajirtarda dukan al’ummai.”—Mat. 28:19, 20.

Bin waɗannan ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki zai shirya ka yin hidima a inda ake bukatar masu wa’azi sosai:

  • Ka yi addu’a ga Jehobah don ya sa ka yi marmarin ƙaura zuwa inda ake da bukata, kuma ka kasance da “sahihiyar hikima.”—Mis. 3:21; Filib. 2:13; Yaƙ. 1:5.

  • Ka nemi shawara daga ’yan’uwa masu hikima. “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.”—Mis. 12:15; 13:20.

  • Ka yi shirye-shirye. “Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka.”—Mis. 21:5, Littafi Mai Tsarki.

  • Ka aikata shirye-shiryen da ka yi. “Ka yi aikin nagarta.”—Zab. 37:3.

Idan ka ɗauki waɗannan matakan, babu shakka, Jehobah zai albarkace ka!—Mis. 16:3.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba