Yin Shiri Sosai Kwalliya Ce da ke Biyan Kuɗin Sabulu
Akwai wata matashiya mai ƙwazo mai suna María Isabel da ke birnin San Bernardo a ƙasar Chile da ke Amirka ta Kudu. Ita da iyalinta ’yan ƙabilar Mapuche ne. Iyalin tana ƙoƙari sosai don su ga cewa an ƙafa sabuwar ikilisiya a yaren Mapudungun.
An sanar cewa za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu a yaren Mapudungun kuma an buga takardar gayyata guda 2,000. Wannan sanarwar ta sa María Isabel tunani. Yaya za ta iya saka hannu don rarraba waɗannan takardun? Sai ta tuna da wasu Shaidu matasa da suka yi nasara wajen yi wa malamansu da abokan ajinsu wa’azi. Bayan hakan, ta tattauna batun da iyayenta, sai suka tsai da shawara cewa za ta gwada rarraba takardar a makaranta. Wane tsari ta bi don rarraba takardun?
Da farko, ta karɓi izini daga hukumar makarantar don ta manna takardar a ƙofar makarantar. Hukumar ta amince da hakan, kuma ta yaba mata don ƙoƙarin da ta yi. A wani lokaci da ake kiran suna a layi, shugaban makarantan ya yi sanarwa a lasifika game da takardar gayyatar.
María Isabel ta karɓi izini don ta bi aji-aji tana rarraba takardun. Bayan an amince ta yi hakan, sai ta bincika ɗaliban da suke yaren Mapudungun. Da farko, ta yi zato cewa ba za su wuce 10 ko 15 ba a makarantar baki ɗaya. Amma, ta yi mamaki sosai sa’ad da ɗalibai 150 suka karɓi takardar gayyatar.
“TANA ZATO BABBAN MUTUM NE”
Wata mata da ta ga takardar gayyatar da aka manna a ƙofar makarantar, ta nemi ta samu ƙarin bayani daga mutumin da ya manna takardar. Sai aka tura ta wajen ’yar shekara goma. Hakan ya ba ta mamaki sosai. María Isabel tana murmushi sa’ad da ta ce, “Matar tana zato za ta ga babban mutum.” Bayan ta ba matar takardar kuma ta ɗan bayyana mata, sai ta karɓi adireshin matar don ita da iyayenta su je gidanta su tattauna game da Mulkin Allah da ita. A ranar taron tunawa da mutuwar Yesu, masu shela 20 da suke yaren Mapudungun sun yi mamaki sosai sa’ad da suka ga matar ta zo da mutane 26. Yanzu, wannan rukunin ya zama ikilisiya kuma ana samun ƙaruwa sosai.
Ko da kai yaro ne ko babba, za ka iya yin koyi da wannan yarinyar ta wajen gayyatar abokan makaranta ko aiki zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu, ko jawabi ga jama’a ko kuma taron gunduma. Zai dace ka yi bincike a littattafanmu, don ka ga labaran da za su iya taimaka maka ka san shawarar da za ka yanke. Ka kuma roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki, don ka kasance da gaba gaɗi kuma ka tattauna da mutane. (Luk 11:13) Idan ka yi hakan, za ka yi farin ciki kuma za ka samu ƙarfafa don irin sakamakon da za ka samu domin ka yi shiri sosai.