Makarantu na Ƙungiyar Jehobah—Tabbaci Ne Cewa Jehobah Yana Ƙaunarmu
JEHOBAH shi ne ‘Mai Koyar da Mu Mafi Girma.’ (Isha. 30:20) Ƙauna ce ta sa yake ilimantar da kuma koyar da mu. Alal misali, matuƙar ƙauna ce ta motsa Jehobah ya nuna wa Yesu “dukan abin da yana yi da kansa.” (Yoh. 5:20) Ƙaunar da Jehobah yake mana a matsayinmu na Shaidunsa ne ya motsa shi ya ba mu “harshe na koyayyun mutane,” yayin da muke iya ƙoƙarinmu don mu girmama shi kuma mu taimaki mutane.—Isha. 50:4.
Kwamitin Koyarwa na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, yana koyi da Jehobah ta wajen yin amfani da makarantun Littafi Mai Tsarki dabam-dabam don koyar da waɗanda suke so kuma suna da hali su halarci waɗannan makarantun. Shin kana ɗaukan waɗannan makarantun a matsayin cewa Jehobah yana ƙaunarmu?
Muna gayyatarka ka samu ƙarin bayyani game da makarantu dabam-dabam na ƙungiyar Jehobah da kuma yadda mutane da yawa suka amfana daga waɗannan makarantun. Sai ka tambayi kanka, ‘A wace hanya ce zan amfana daga wannan ilimantarwar?’
KA AMFANA DAGA KOYARWA TA ƘUNGIYAR JEHOBAH
Tun da Jehobah ‘Allah mai nuna ƙauna ne,’ yana tanadar da ilimantarwa da ke kyautata rayuwarmu. Koyarwar da Jehobah yake tanadar mana tana shirya mu mu shawo kan ƙalubale kuma tana sa mu ji daɗin hidimarmu sosai. (2 Kor. 13:11) Muna kama da almajiran Yesu na ƙarni na farko, domin muna a shirye sosai mu taimaka wa mutane ta wajen “koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da” aka umurce mu.—Mat. 28:20.
Ko da yake wataƙila ba za mu iya halartar dukan makarantun nan ba, amma za mu iya amfana daga ɗaya ko biyu daga cikinsu. Kuma za mu iya yin amfani da shawarwari na Littafi Mai Tsarki da muka koya daga makarantun. Idan mun kuma fita wa’azi tare da waɗannan bayin Jehobah da aka koyar sosai, za mu iya koyon abubuwa da yawa da za su kyautata hidimarmu.
Ka tambayi kanka, ‘Shin yanayina zai iya ƙyale ni na daɗa ƙoƙari don na cancanci halartar ko da ɗaya ne cikin waɗannan makarantun?’
Gata ne sosai ga bayin Jehobah su tallafa da kuma koya daga waɗannan makarantu masu amfani sosai. Muna fatan cewa abubuwan da za ka koya za su motsa ka ka kusaci Allah sosai kuma za ka ƙware don cika hakkokinka, musamman hakkinka mai gaggawa sosai na yin wa’azin bishara.
[Akwati/Hotona a shafi na 13-17]
BAYANAI GAME DA TSARIN MAKARANTU NA LITTAFI MAI TSARKI
Makarantar Hidima ta Allah
Manufa: Don koyar da masu shela su ƙware wajen koyarwa da kuma yin wa’azin bishara.
Tsawon Lokaci: Ba a sauke karatu.
Wuri: Majami’ar Mulki da ke yankin. Wanda Zai Iya Halarta: Dukan waɗanda suke halartar taro a kai a kai, da suka amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma rayuwarsu ta jitu da ƙa’idodin Kirista.
Yadda Za a Shiga: Ka tattauna da dattijon da ke kula da Makarantar Hidima ta Allah don ya saka sunanka.
Wata mai suna Sharon da take fama da ciwon shanyewar jiki ta ce: “Makarantar Hidima ta Allah ta koya mini yin bincike da kuma bayyana abubuwa da basira. Makarantar ta taimake ni sosai, amma ta kuma sa na taimaki mutane su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.”
Wani mai suna Arnie da ya daɗe yana hidimar mai kula mai ziyara ya ce: “Ina in’ina tun ina ƙarami, kuma sa’ad da nake magana ba na iya kallon fuskar mutane. Amma, makarantar ta taimaka mini na samu gaba gaɗin yin magana a gaban mutane. Jehobah ya yi amfani da wannan makarantar don ya taimaka mini sosai. Yanzu ina yin magana ba tare da yin in’ina ba. Ina godiya sosai don ina yabon Allah a cikin ikilisiya da kuma sa’ad da nake wa’azi.”
Makarantar Sababbi Masu Hidima a Bethel
Manufa: Don a taimaki sababbi su yi nasara a hidimarsu a Bethel.
Tsawon Lokaci: Minti 45 duk mako har tsawon mako goma sha shida.
Wuri: A Bethel.
Ƙwarewa: Dole ne mutumin ya kasance ɗaya daga cikin iyalin Bethel ko kuma wanda ya ba da kansa na ɗan lokaci, kamar shekara ɗaya ko fiye da hakan.
Yadda Za a Shiga: Za a sa sunan sababbi da suka zo Bethel ba tare da sun ce a yi hakan ba.
Wani mai suna Demetrius wanda ya halarci makarantar tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1989 ya ce: “Wannan makarantar ta kyautata yadda nake nazari kuma ta shirya ni don hidima ta shekaru da yawa da nake yi a Bethel. Malaman makarantar da abubuwan da aka koya mana da kuma shawarwari masu kyau da aka ba mu sun sa na amince cewa Jehobah yana ƙauna na sosai kuma yana son ya taimaka mini na yi nasara a hidimata a Bethel.”
Wata mai suna Kaitlyn ta ce: “An taimaka mini na mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, wato, zama wadda take yin abubuwa yadda Jehobah yake so. Makarantar ta sa na ƙara sani da kuma nuna godiya ga Jehobah da gidansa da kuma ƙungiyarsa.”
Makarantar Hidima ta Mulki
Manufa: Don a koyar da masu kula masu ziyara da dattawa da kuma a wasu lokatai bayi masu hidima su kula da aikinsu na masu kula da kuma hakkinsu a ƙungiyar Jehobah. (A. M. 20:28) Ana tattauna yanayi da abubuwa da suke tasowa a cikin ikilisiyoyi. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce za ta tsai da lokacin da za a yi wannan makarantar bayan wasu shekaru.
Tsawon Lokaci: A kwana-kwanan nan, masu kula masu ziyara suna makarantar na tsawon kwana biyu ko biyu da rabi, dattawa kuma kwana ɗaya da rabi, na bayi masu hidima kuma kwana ɗaya ne.
Wuri: Galibi, a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.
Ƙwarewa: Wajibi ne mutum ya zama mai kula mai ziyara ko dattijo ko kuwa bawa mai hidima.
Yadda Za a Shiga: Mai kula da da’ira zai sanar da dattawa da kuma bayi masu hidima da suka cancanta. Ofishin reshe na gayyatar masu kula masu ziyara.
“Ko da yake ana tattauna abubuwa da yawa cikin ɗan lokaci a makarantar, tana taimaka wa dattawa su ci gaba da farin ciki kuma ‘su mazakuta’ a hidimar Jehobah. Waɗanda suka daɗe a matsayin dattawa da kuma sababbi suna koya yadda ake ƙarfafa ’yan’uwa da kyau kuma su kasance da haɗin kai ‘da ra’ayi ɗaya.’”—In ji Quinn (wanda aka nuna a ƙasa).
“Wannan koyarwa ta taimaka mana mu fahimci abubuwan da suka shafi bangaskiyarmu sosai, kuma ta yi mana gargaɗi a kan haɗarurruka da za mu guje wa da kuma ba mu shawarwari masu kyau game da yadda za mu kula da ’yan’uwa. Muna godiya ga Jehobah da ya yi mana wannan tanadin.”—In ji Michael.
Makarantar Hidima ta Majagaba
Manufa: Don taimaka wa majagaba su ‘cika hidimarsu sosai.’—2 Tim. 4:5.
Tsawon Lokaci: Mako biyu.
Wuri: Inda ofishin reshe ya zaɓa, sau da yawa a Majami’ar Mulki.
Ƙwarewa: Waɗanda suka yi hidimar majagaba na kullum aƙalla na tsawon shekara guda ko kuma fiye da haka.a
Yadda Za a Shiga: Za a zaɓa majagaban da suka cancanta ba tare da saka takarda ba kuma mai kula da da’ira zai sanar da su.
“Wannan makarantar ta taimaka mini na jimre da matsaloli da nake fuskanta a hidima da kuma rayuwata,” in ji Lily (wadda ke hannun dama). “Makarantar ta kyautata yadda nake nazari da koyarwa da kuma yin amfani da Littafi Mai Tsarki. Na fi kasancewa a shirye na taimaki mutane da goyi bayan dattawa da kuma sa ikilisiyar ta samu ƙaruwa.”
Brenda, wadda ta halarci makarantar sau biyu ta ce: “Makarantar ta taimaka mini na kasance da ƙwazo a hidimata ga Jehobah kuma ta sa na samu zuciyar kirki da kuma mai da hankali ga taimaka wa mutane. Hakika, Jehobah mai karimci ne!”
[Hasiya]
a Idan babu isashen sababbin majagaba a cikin wani aji, ana iya gayyatar majagaba da ba su halarci makarantar ba cikin shekara biyar da ta shige.
Makaranta don Dattawan Ikilisiya
Manufa: Don taimaka wa dattawa su kula da hakkokinsu a cikin ikilisiya kuma su fahimci yadda ya kamata su bauta wa Jehobah.
Tsawon Lokaci: Kwana biyar.
Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓa, galibi a Majami’ar Mulki ko Majami’ar Taro.
Ƙwarewa: Wajibi ne mutum ya zama dattijo.
Yadda Za a Shiga: Ofishin reshe zai gayyaci dattawan da suka cancanta.
Ka lura da abin da wasu da suka halarci aji na 92 a Amirka suka ce:
“Na amfana sosai daga makarantar don ta taimaka mini na sake bincika kaina don na ga yadda zan iya kula da tumakin Jehobah.”
“Ina shirye na riƙa ƙarfafa dukan ’yan’uwana ta wajen nanata ainihin darussa da aka koyar a cikin Nassosi.”
“Wannan koyarwa za ta taimaka mini a rayuwata.”
Makaranta don Masu Kula Masu Ziyara da Matansu
Manufa: Don a taimaki masu kula masu ziyara da masu kula da gunduma su ƙware sosai a hidimarsu ga ikilisiya kuma su sa ƙwazo a “aiki cikin kalma da koyarwa.”—1 Tim. 5:17; 1 Bit. 5:2, 3.
Tsawon Lokaci: Wata biyu.
Wuri: Inda ofishin reshe ya zaɓa.
Ƙwarewa: Wajibi ne ya zama mai kula da da’ira ko mai kula da gunduma.
Yadda Za a Shiga: Ofishin reshe ne yake gayyatar masu kula masu ziyara da matansu.
“An sa mu ƙara nuna godiya ga yadda Yesu yake shugabanci bisa ƙungiyar Jehobah. Mun koya cewa muna bukatar mu ƙarfafa ’yan’uwa da muke ziyarta kuma mu sa ikilisiya ta ƙara kasance da haɗin kai. Makarantar ta koya mana cewa ainihin maƙasudin mai kula da da’ira shi ne ya taimaka wa ’yan’uwa su san cewa Jehobah yana ƙaunarsu ko da yake a wasu lokatai yana ba su shawara da kuma yi musu gyara.”—In ji Joel, wanda ya halarci aji na farko, a shekara ta 1999.
Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure
Manufa: Don a koyar da dattawa da bayi masu hidima da ba su yi aure ba don su kula da ƙarin hakki a cikin ƙungiyar Jehobah. Za a aika yawancin waɗanda suka sauke karatu su yi hidima a inda akwai bukata a ƙasarsu. Za a iya aika kalila cikinsu su yi hidima a wata ƙasa idan suka ba da kansu. Wasu suna iya yin hidimar majagaba na musamman na ɗan lokaci don su soma wa’azi da kuma taimaka a samu ƙaruwa a wuraren da babu ikilisiya.
Tsawon Lokaci: Wata biyu.
Wuri: Ofishin reshe ne ke zaɓan inda za a yi makarantar; ana yi a Majami’ar Taro da Majami’ar Mulki.
Ƙwarewa: ’Yan’uwa maza marasa aure da ke tsakanin shekara 23 da 62 da suke da koshin lafiya kuma suna son su yi hidima a duk inda ake da bukata sosai. (Mar. 10:29, 30) Wajibi ne su yi hidimar majagaba aƙalla na shekara biyu kuma su dattawa ne ko bayi masu hidima aƙalla na tsawon shekara biyu ba tare da fashi ba.
Yadda Za a Shiga: Ana ba da ƙarin bayani game da wannan makarantar a taron da ake yi a taron da’ira.
Wani mai suna Rick, wanda ya sauke karatu a aji na 23 na wannan makarantar a Amirka ya ce: “Fahimtar wannan koyarwar sosai ya sa ruhu mai tsarki na Jehobah ya yi gyare-gyare a rayuwata. Idan Jehobah ya ba ka aiki, yana tabbata cewa ya taimaka maka ka cim ma aikin. Na koyi cewa Allah zai ƙarfafa ni idan na mai da hankali ga yin nufinsa.”
Andreas wanda ke hidima a ƙasar Jamus ya ce: “Na koyi cewa yadda ƙungiyar Jehobah take aiki a yau kamar mu’ujiza ce. Abin da na koya ya shirya ni don aikin da zan yi a nan gaba. Kuma na koya daga labarai na Littafi Mai Tsarki cewa ya kamata na yi wa ’yan’uwana da kuma Jehobah hidima, kuma yin hakan yana kawo farin ciki na gaske.”
Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata
Manufa: Don a yi wa ma’aurata koyarwa ta musamman don Jehobah da ƙungiyarsa su yi amfani da su sosai. Za a tura yawancinsu da suka sauke karatu zuwa wuraren da ake da bukata a ƙasarsu. Ana iya tura kalilan yin hidima a wata ƙasa idan sun amince da hakan. Waɗanda suka sauke karatu za su iya zama majagaba na musamman na ɗan lokaci kuma za su soma wa’azi a wasu yankuna da babu ikilisiya kuma su sa a samu ci gaba a wurin.
Tsawon Lokaci: Wata biyu.
Wuri: Ana yin wannan makarantar a ƙasar Amirka, kuma za a soma ta a wasu ƙasashen da aka zaɓa somawa daga watan Satumba na 2012, galibi a Majami’ar Taro ko kuma Majami’ar Mulki.
Ƙwarewa: Ma’aurata masu shekara 25 zuwa 50 da suke da koshin lafiya kuma yanayinsu zai ƙyale su su yi hidima a duk inda ake da bukata kuma suna da halin “Ga ni; ka aike ni.” (Isha. 6:8) Bugu da ƙari, za su kasance ma’aurata na aƙalla shekara biyu kuma suna hidima ta cikakken lokaci na aƙalla shekara biyu ba tare da fashi ba. Dole ne mijin ya yi hidima a matsayin dattijo ko bawa mai hidima aƙalla na shekara biyu.
Yadda Za a Shiga: Za a yi taron waɗanda suke son su shiga a taron gunduma. Ana ba da ƙarin bayani a wannan taron. Idan ba a yin wannan taron a taron gunduma a ƙasarku kuma kuna son ku yi wannan hidimar, za ku iya rubuta wasiƙa ga ofishin reshe da ke ƙasarku don ƙarin bayani.
“Waɗannan makonni takwas sun canja rayuwarmu sosai kuma sun ba mu zarafi a matsayin ma’aurata don yin ƙarin ayyuka a hidimar Jehobah! Mun ƙuduri aniyar daidaita salon rayuwarmu don mu yi amfani da lokacinmu yadda ya kamata.”—In ji Eric da Corina (a ƙasa), waɗanda suka halarci aji na farko a shekara ta 2011.
Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead
Manufa: Don a koyar da ɗalibai su yi hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje a yankunan da akwai jama’a sosai. Za su zama masu kula masu ziyara ko kuma za su yi hidima a Bethel. Abin da ake son a cim ma da wannan makarantar shi ne a ƙarfafa ’yan’uwa a yankuna da kuma yadda ake hidima a ofishin reshe.
Tsawon Lokaci: Wata biyar.
Wuri: A Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka.
Ƙwarewa: Ma’aurata da suke hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarci makarantar ba ko majagaba na musamman ko masu kula masu ziyara ko kuma masu hidima a Bethel. Dole ne su yi wannan hidimar tare babu fashi na aƙalla shekara uku. Suna bukatar su iya faɗa da karanta da kuma rubuta Turanci sosai.
Yadda Za a Shiga: Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah zai iya gayyatar ma’aurata su saka afilkeshan.
Lade da Monique daga Amirka suna hidima yanzu a Afirka. “Makarantar ta shirya mu mu yi hidima a ko’ina a duniya kuma mu yi hidima tare da ’yan’uwanmu ƙaunatattu,” in ji Lade.
Monique ta daɗa cewa: “Yayin da nake yin amfani da abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki, ina jin daɗin hidimata sosai. Kuma hakan ya nuna mini cewa Jehobah yana ƙauna ta sosai.”
Makaranta don ’Yan Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah da Matansu
Manufa: Don a taimaka wa Kwamitin da ke kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah ya kula da gidajen Bethel da kuma mai da hankali ga batutuwa da suka shafi ikilisiyoyi da da’irori da kuma gundumomi. Suna kuma koyo game da yin fassara da buga littattafai da kuma aika su zuwa ikilisiyoyi.
Tsawon Lokaci: Wata biyu.
Wuri: Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, a birnin New York, Amirka.
Ƙwarewa: Dole ne ɗan’uwan ya kasance cikin Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah ko Kwamiti na Ƙasar ko kuma an naɗa shi ya yi wannan hidimar.
Yadda Za a Shiga: Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ce take gayyatar ’yan’uwa maza da suka cancanta da matansu.
Lowell da Cara da suka sauke karatu a aji na 25 suna hidima a Nijeriya. “An tunasar mini cewa ko yaya na shagala da aiki ko kuma kowanne irin aiki ne aka ba ni, abin da zai taimaka mini shi ne na yi abubuwan da za su faranta wa Jehobah rai,” in ji Lowell. “Mun kuma koyi muhimmancin yin koyi da ƙaunar da Jehobah yake wa bayinsa.”
Cara ta ce: “Ga wani kalami da na yi bimbini sosai a kai, idan ba zan iya bayyana abu a hanya mai sauƙi ba, ya kamata na sake yin nazarin abin kafin na koya wa wasu.”