Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 9/15 pp. 8-12
  • Za A Yi Zaman Lafiya Na Shekara Dubu Da Kuma Har Abada!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za A Yi Zaman Lafiya Na Shekara Dubu Da Kuma Har Abada!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘ZA SU GINA GIDAJE KUMA SU DASA GONAKIN ANAB’
  • “KERKECI DA ƊAN RAGO ZA SU YI KIWO TARE”
  • “ZAI SHARE DUKAN HAWAYE”
  • ‘DUKAN WAƊANDA SUKE CIKIN KABARBARU ZA SU FITO’
  • ALLAH ZAI ZAMA “DUKA CIKIN DUKA”
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Abin Da Mulkin Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Sashe na 10—Sabuwar Duniya Mai-Ban Al’Ajibi Yin Allah
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 9/15 pp. 8-12

Za A Yi Zaman Lafiya Na Shekara Dubu Da Kuma Har Abada!

“Domin Allah ya zama duka cikin duka.”​—1 KOR. 15:28.

MECE CE AMSARKA?

Mene ne za ka shaida sa’ad da waɗannan ayoyi suka cika?

Mikah 4:4

Ishaya 11:6-9

Yohanna 5:28, 29

1. Waɗanne abubuwa ne “taro mai-girma” za su more a nan gaba?

KA YI tunanin irin alherin da sarki mai kirki da kuma juyayi zai yi wa talakawansa a cikin shekara dubu. “Taro mai-girma” za su more waɗannan albarkar. Su ne za su tsira “daga cikin babban tsananin,” wanda zai kawo ƙarshe ga wannan mugun yanayin da muke ciki a yau.—R. Yoh. 7:9, 14.

2. Mene ne sakamakon sarautar ’yan Adam suka yi na shekaru dubu shida da suka shige?

2 A cikin shekaru dubu shida da suka shige, ’yan Adam sun yi ƙoƙari su mulki kansu amma sakamakon hakan shi ne wahala da baƙin ciki. Tun da daɗewa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.” (M. Wa. 8:9) Waɗanne abubuwa ne suke faruwa a yau? Ana yaƙe-yaƙe da tawaye da talauci da cututtuka da gurɓatar mahalli da canjin yanayi da kuma sauransu. Hukumomi sun ba da gargaɗi cewa idan ’yan Adam ba su daina yin waɗannan abubuwan ba, hakan zai kawo mugun sakamako.

3. Mene ne zai faru a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

3 Mulkin Allah zai kawar da dukan matsalolin ’yan Adam kuma zai gyara duniya sa’ad da Yesu Kristi, Sarkin da Allah ya naɗa ya soma sarauta tare da mutane 144,000. A Shekara Dubu na Sarautar Yesu, Allah zai cika alkawarinsa. Allah ya ce: “Sabobin sammai da sabuwar duniya na ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” (Isha. 65:17) Waɗanne abubuwa masu al’ajabi ne za su faru a nan gaba? Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu fahimci yadda waɗannan abubuwan za su kasance ko da yake al’amura “marasa-ganuwa” ne.—2 Kor. 4:18.

‘ZA SU GINA GIDAJE KUMA SU DASA GONAKIN ANAB’

4. Waɗanne matsalolin wurin kwana ne mutane suke fuskanta a yau?

4 Wane mutum ne ba zai so ya samu gidan kansa ba, inda shi da iyalinsa za su kasance cikin kwanciyar hankali? Amma, ba shi da sauƙi a samu wurin zama a yau. Mutane da yawa suna zama a birnin da ake cunkoso sosai. Mutane da yawa suna zama a tsofaffin gidaje da ba su da tsabta da kuma tsari. A mafarki ne kawai suke gani cewa suna da nasu gida.

5, 6. (a) A wace hanya ce Ishaya 65:21 da Mikah 4:4 za su cika? (b) Ta yaya za mu more wannan albarkar?

5 Sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta, kowa zai samu nasa gida. Ishaya ya annabta cewa: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu.” (Isha. 65:21) Amma dai, ba gidan kansu kaɗai za su samu a ƙarƙashin Mulkin Allah ba. A yau, mutane da yawa suna da nasu gidaje, kuma wasu suna da manya-manyan gidaje. Duk da haka, suna yawan jin tsoro cewa za su rasa gidan saboda taɓarɓarewar tattalin arziki ko kuma ɓarayi za su shiga gidan. Amma, sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta, hakan ba zai faru ba. Annabi Mikah ya ce: “Kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratar da su.”—Mi. 4:4.

6 Me ya kamata mu yi idan muna son mu kasance cikin Mulkin Allah? Ko da yake kowannenmu yana bukatar wurin kwana, amma bai kamata mu biɗi waɗannan abubuwan yanzu ba. Wasu suna cin bashi don su cim ma waɗannan bukatun, amma ya kamata mu yi rayuwa yadda zai nuna cewa muna dogara ga alkawuran Jehobah. Yesu ya furta kalaman da ke gaba game da kansa, ya ce: “Yanyawa suna da ramummukansu, tsuntsayen sama kuma suna da sheƙunansu, amma Ɗan mutum ba shi da wurin da za ya sa kansa.” (Luk 9:58) Da a ce Yesu ya so, da ya gina gidan da ya burge na kowa domin yana da ikon yin hakan. Amma, me ya sa bai yi hakan ba? Hakika, Yesu ba ya son kome da zai raba hankalinsa daga biɗan Mulkin Allah da farko a rayuwarsa. Idan mun yi koyi da misalin Yesu, ba za mu ƙyale abin duniya ya fi muhimmanci a rayuwarmu balle ma ya jawo mana alhini ba.—Mat. 6:33, 34.

“KERKECI DA ƊAN RAGO ZA SU YI KIWO TARE”

7. Wane umurni ne Allah ya ba da game da dangantakar mutum da dabbobi?

7 Sa’ad da Jehobah ya soma halitta a duniya, mutum ne abu na ƙarshe da ya yi. Jehobah ya gaya wa Gwani-Mai-Aikinsa wato, Yesu dalilin da ya sa ya halicci mutane. Ya ce: “Bari mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu: su yi mulki kuma bisa kifaye na teku, da tsuntsaye na sama, da bisashe, da kuma bisa dukan duniya, da kowane abu mai-rarrafe wanda ke rarrafe a bisa ƙasa.” (Far. 1:26) Allah ya umurci Adamu da Hauwa’u su kula da dabbobi kuma su mulke su. Daga baya, hakan ya shafi dukan ’yan Adam.

8. Mene ne halin dabbobi a yau?

8 Zai yiwu kuwa ’yan Adam su mulki dabbobi kuma su zauna cikin salama? Mutane da yawa suna kiwon kare da mage kuma suna son waɗannan dabbobin sosai. Amma wasu namomin daji kuma fa? Masanan kimiyya da suke zama kusa da namomin daji sun ruwaito cewa dabbobi da yawa suna da motsin rai. Mun san cewa dabbobi suna jin tsoro da kuma fushi sa’ad da aka yi musu barazana, amma zai yiwu su kasance da tausayi? ’Yan kimiyyar sun ce sa’ad da dabbobi suka haifi jarirai suna bi da su a hankali.

9. Mene ne zai faru da dabbobi a nan gaba?

9 Bai kamata abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa ’yan Adam da dabbobi za su kasance cikin salama ya sa mu mamaki ba. (Karanta Ishaya 11:6-9; 65:25.) Me ya sa? Ka tuna cewa sa’ad da Nuhu da iyalinsa suka fito daga jirgin ruwa bayan Rigyawar, Jehobah ya gaya musu: “Tsoronku da kwarjininku za ya kama kowane dabba na duniya.” A yau, dabbobi da yawa suna guduwa daga mutane don kada a kashe su. (Far. 9:2, 3) Amma, Jehobah zai iya cire wannan tsoron daga dabbobi domin dangantakarsu da ’yan Adam ta zama yadda yake tun asali. (Hos. 2:18) Duk mutumin da zai kasance a duniya a wannan lokacin zai ji daɗin rayuwa sosai!

“ZAI SHARE DUKAN HAWAYE”

10. Me ya sa mutane suke zubar da hawaye a yau?

10 Sa’ad da Sulemanu ya ga “dukan irin zilama da a ke yi a cikin duniya” sai ya ce: “Duba, ga hawayen waɗannan da a ke zalumtarsu, ba su da mai-taimako; a wajen masu-zalumtarsu kuma ga iko, amma ba su da mai-taimako.” (M. Wa. 4:1) Hakan ma abubuwa suke a yau ko kuma sun fi hakan muni. Wane ne bai taɓa zubar da hawaye ba? Ko da yake a wasu lokatai, farin ciki zai iya sa mu zubar da hawaye amma ɓacin rai ne yake yawan sa mu zubar da hawaye.

11. Wane labari na Littafi Mai Tsarki ne ya fi ba ka tausayi?

11 Ka yi la’akari da labarai da yawa na mutane da suka zubar da hawaye da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Saratu ta rasu sa’ad da take ’yar shekara 127, “Ibrahim kuma ya zo domin makoki saboda Saratu, ya yi kuka kuma dominta.” (Far. 23:1, 2) Sa’ad da Naomi ta yi wa surukanta biyu ban kwana, sai “suka tada muryarsu da ƙarfi, suka yi kuka.” (Ruth 1:9, 14) Sa’ad da Sarki Hezekiah yake ciwo kuma ya kusan mutuwa sanadiyyar ciwon, sai ya yi addu’a ga Allah kuma “ya yi ta kuka mai-zafi.” Jehobah ya ga hawayensa kuma ya warkar da shi. (2 Sar. 20:1-5) Kuma bayan Bitrus ya musunci Yesu, abin da ya biyo bayan hakan abin tausayi ne sosai. Sa’ad da Bitrus ya ji zakara ya yi cara, sai “ya fita waje, ya yi ta kuka mai-zafi.”—Mat. 26:75.

12. Ta yaya Sarautar Shekara Dubu ta Yesu za ta kawo sauƙi ga ’yan Adam?

12 Mutane suna bukatar ta’aziya da kuma sauƙi domin abin baƙin ciki yana auko musu. A Shekara Dubu na Sarautar Kristi, Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” (R. Yoh. 21:4) Abin mamaki ne sosai sani cewa Allah zai cire baƙin ciki da kuka da kuma azaba. Amma, akwai wani abu da Allah zai yi da ya fi waɗannan. Zai cire mutuwa. Yaya hakan zai faru?

‘DUKAN WAƊANDA SUKE CIKIN KABARBARU ZA SU FITO’

13. Ta yaya mutuwa ta shafi mutane tun lokacin da Adamu ya yi zunubi?

13 Tun bayan da Adamu ya yi zunubi, mutuwa ta mallake mutane. Maƙiya ce da ta fi ƙarfin kowa. Babu mutum ajizi da zai iya kuɓuce mata kuma tana jawo matuƙar baƙin ciki da makoki. (Rom. 5:12, 14) Hakika, “tsoron mutuwa” ya sa miliyoyin mutane “ƙarƙashin bauta muddar ransu.”—Ibran. 2:15.

14. Mene ne zai faru sa’ad da aka kawar da mutuwa?

14 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da lokacin da “za a kawar” da “maƙiyi na ƙarshe,” wato mutuwa. (1 Kor. 15:26) Hakan zai kawo sakamako biyu. “Taro mai-girma” da suke da rai a yau za su samu damar yin rayuwa har abada a sabuwar duniya. Biliyoyin mutane kuma da suka mutu za su tashi daga matattu. Ka yi tunanin irin matuƙar farin ciki da “taro mai-girma” za su yi sa’ad da suke marabtar waɗanda suka tashi daga matattu. Idan ka karanta labaran mutanen da aka ta da daga matattu da Littafi Mai Tsarki ya ambata, za ka fahimci yadda wannan lokacin zai kasance.—Karanta Markus 5:38-42; Luka 7:11-17.

15. Yaya za ka ji sa’ad da ka ga wani ƙaunatacenka da ya mutu ya tashi daga matattu?

15 Ka yi la’akari da kalmomin nan, suka yi “mamaki mai-girma” da kuma “suka girmama Allah.” Da kai ma kana wurin, wataƙila da ka ji kamar su. Za mu yi farin ciki sosai sa’ad da aka ta da ƙaunatattunmu daga mutuwa. Yesu ya ce: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.” (Yoh. 5:28, 29) Babu kowannenmu da ya taɓa shaida irin wannan abu, amma babu shakka, hakan zai zama ɗaya daga cikin al’amura “marasa-ganuwa” mafi girma.

ALLAH ZAI ZAMA “DUKA CIKIN DUKA”

16. (a) Me ya sa ya kamata mu yi ɗokin yin magana game da albarkar da ba mu taɓa gani ba? (b) Mene ne Bulus ya faɗa don ya ƙarfafa Kiristocin da ke Korinti?

16 Mutanen da suka kasance da aminci ga Jehobah a wannan yanayi mai wuya za su ji daɗi a nan gaba! Ko da yake ba mu taɓa shaida waɗannan albarkar ba, amma yin tunani a kansu zai taimaka mana mu mai da hankali ga abubuwa masu muhimmanci sosai. Idan mun yi hakan, za mu ci gaba da bauta wa Jehobah kuma abin duniyar nan ba zai janye hankalinmu ba. (Luk 21:34; 1 Tim. 6:17-19) Ku yi magana game da wannan batun sa’ad da kuke bauta ta iyali da yamma da sa’ad da kuke hira da ’yan’uwa da ɗalibanku na Littafi Mai Tsarki da waɗanda suke son saƙonmu. Hakan zai sa mu riƙa tunawa da wannan begen sosai. Yadda manzo Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci ke nan. Kalmominsa sun taimaka musu su yi tunani a kan abin da zai faru a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu. Ka ƙoƙarta don ka fahimci ma’anar kalmomin Bulus da ke littafin 1 Korintiyawa 15:24, 25, 28.—Karanta.

17, 18. (a) A wace hanya ce Jehobah “duka cikin duka” ne a lokacin da ya halicci Adamu da Hauwa’u? (b) Mene ne Yesu zai yi don a sake samun kwanciyar rai da haɗin kai?

17 Kalmomin nan “Allah ya zama duka cikin duka” ne suka bayyana daidai yadda rayuwa za ta kasance bayan shekara dubu da Yesu zai yi sarauta. Mene ne hakan yake nufi? Ka yi tunanin lokacin da Adamu da Hauwa’u suke cikin iyalin Jehobah kuma suke zaman lafiya. A lokacin, Jehobah Maɗaukakin Sarki ne yake mulki a kan dukan halittunsa da ke sama da duniya. Suna da damar yin magana da Jehobah da bauta masa da kuma more albarkarsa. Shi ‘duka ne cikin duka.’

18 Sun rasa wannan dangantakar sa’ad da Shaiɗan ya rinjayi Adamu da Hauwa’u su yi tawaye da Jehobah. Amma tun shekara ta 1914, Mulkin Allah ya soma sarauta don ya yiwu a sake more wannan kwanciyar rai da haɗin kai da suka yi hasara. (Afis. 1:9, 10) A lokacin Sarautar Yesu ta Shekara Dubu, abubuwa masu ban al’ajabi “marasa-ganuwa” za su faru. Bayan haka, sai “matuƙa,” wato ƙarshen Sarautar Yesu ta Shekara Dubu. Mene ne zai faru a lokacin? Ko da yake an ba Yesu “dukkan iko a sama da ƙasa” amma shi ba mai son matsayi ba ne. “Zai bada mulki ga Allah, Uba” cikin tawali’u. Zai yi amfani da matsayinsa na musamman da ikonsa don “darajar Allah.”—Mat. 28:18; Filib. 2:9-11.

19, 20. (a) Ta yaya talakawan Mulkin Allah za su nuna cewa suna goyon bayan Jehobah a matsayin Maɗaukakin Sarki? (b) Waɗanne abubuwa masu ban al’ajabi ne za mu more a nan gaba?

19 A lokacin, dukan talakawan Mulkin Allah za su zama kamiltattu. Za su bi misalin Yesu. Kuma domin suna da sauƙin kai, za su yi farin ciki don Jehobah yana mallakarsu. Za su tsira daga gwaji na ƙarshe idan suka nuna cewa suna son Jehobah ya mallake su. (R. Yoh. 20:7-10) Bayan haka, za a halaka dukan mala’iku da ’yan Adam masu tawaye. Hakika, za a yi farin ciki sosai a lokacin! Dukan waɗanda ke iyalin Jehobah, a sama da kuma duniya za su yabe shi, kuma zai zama “duka cikin duka.”—Karanta Zabura 99:1-3.

20 Waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi da Mulkin zai kawo za su motsa ka ka mai da hankali kuma ka ƙoƙarta sosai wajen yin nufin Jehobah? Za ka iya yin ƙuduri kada ka ƙyale jin daɗi na ɗan lokaci na duniyar Shaiɗan ya janye hankalinka? Ka ƙuduri aniya cewa za ka goyi bayan Jehobah a matsayin Maɗaukakin Sarki? Bari ayyukanka su nuna cewa kana son ka yi hakan har abada. Idan ka yi haka, za ka samu damar more kwanciyar hankali da lumana a lokacin sarautar Yesu na Shekara Dubu da kuma har abada!

[Hotona a shafi na 11]

Sa’ad da Yesu ya kammala sarautarsa, zai miƙa Mulkin ga Ubansa cikin tawali’u

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba