Tarihi
Na Zaɓi Tsofaffi Masu Hikima Su Zama Abokaina
Elva Gjerde ce ta ba da labarin
Wajen shekara saba’in da ta shige, wani baƙo da ya zo gidanmu ya gaya wa mahaifina wani abu da ya canja rayuwata gabaki ɗaya. Tun waccan muhimmiyar ranar, na yi abota da mutane da yawa amma akwai abota da na yi da ya fi kowanne. Bari in gaya muku labarin.
AN HAIFE ni a birnin Sydney, a ƙasar Ostareliya, a shekara ta 1932. Iyayena sun yi imani da Allah amma ba sa zuwa coci. Mahaifiyata ta koya mini cewa Allah yana kallona a kowane lokaci kuma zai yi mini horo a duk lokacin da na yi taurin kai. Hakan ya sa ba na son jin kome game da Allah. Duk da haka, ina son Littafi Mai Tsarki. Gwaggota takan ziyarce mu a ƙarshen mako kuma ta gaya mini labarai masu daɗi daga cikin Littafi Mai Tsarki. Ina jin daɗin ziyararta a kowane lokaci.
Sa’ad da nake matashiya, mahaifina ya karanta wani jerin littattafai da wata tsohuwa da Mashaidiyar Jehobah ce ta ba mahaifiyata. Abin da ya karanta a cikin waɗannan littattafan ya burge shi sosai har ya yarda Shaidu su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Wata yamma da suke nazarin Littafi Mai Tsarki, mahaifina ya kama ni ina sauraron abin da suke faɗa a ɓoye. Yana so ya kore ni in je in yi barci, amma sai baƙon ya ce: “Ka ƙyale Elva ta zauna ta saurara.” Wannan abin da ya faɗa ya sa rayuwata ta fara canjawa kuma shi ne somawar abota ta da Allah na gaskiya, Jehobah.
Ba da daɗewa ba bayan haka, ni da mahaifina muka fara halartar taron Kirista. Abubuwan da ya koya a waɗannan taron sun sa shi ya yi canje-canje a rayuwarsa. Har ya daina saurin fushi. Wannan ya sa mahaifiyata da wana Frank, suka soma halartar taro.a Dukanmu huɗu muka yi canje-canje, da shigewar lokaci muka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Tun daga lokacin, na yi abota da tsofaffi da yawa waɗanda suka taimaka mini lokatai dabam-dabam a rayuwata.
MENE NE ZAN YI A RAYUWA?
Sa’ad da nake matashiya, na yi abota da tsofaffi da ke cikin ikilisiyarmu. Ɗaya daga cikinsu ita ce Alice Place, wata tsohuwa da ta fara yi wa iyalinmu wa’azi. Ta zama kamar kaka a gare ni. ’Yar’uwa Alice ce ta koya mini yadda ake wa’azi kuma ta ƙarfafa ni in yi baftisma. Saboda haka, na yi baftisma sa’ad da nake ’yar shekara 15.
Na kuma yi abota da wasu tsofaffin ma’aurata, Percy da Margaret Dunham. Zaman da muka yi tare ya taimake ni sosai a rayuwata. Ina sha’awar lissafi sosai, kuma ina son in zama malama mai koyar da lissafi. ’Yan’uwa Percy da Margaret masu wa’azi a ƙasashen waje ne da suka yi hidima a ƙasar Latvia tsakanin shekara ta 1930 da 1939. Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na biyu a ƙasan Turai, aka gayyace su hidima a Bethel na Osatareliya da ke wani gari kusa da birnin Sydney. ’Yan’uwa Percy da Margaret suna ƙauna ta sosai, kuma suka gaya mini labarai da yawa masu daɗi game da aikin wa’azi a ƙasashen waje. Na fahimci sarai cewa koya wa mutane Littafi Mai Tsarki zai fi sa ni farin ciki. Saboda haka, na yanke shawara na zama mai wa’azi a ƙasashen waje.
Percy da Margaret Dunham sun ƙarfafa ni na soma hidimar majagaba na kullum don hakan ya shirya ni yin hidima a ƙasashen waje. Saboda haka, a shekara ta 1948, sa’ad da nake ’yar shekara 16, na zama majagaba. Kuma a lokacin akwai matasa goma da suke hidimar majagaba da farin ciki a cikin ikilisiyarmu a garin Hurstville, a birnin Sydney.
Cikin shekara huɗu, na yi hidima a garuruwa huɗu a jihar New South Wales da Queensland. ’Yar’uwa Betty Law (yanzu sunanta Betty Remnant ce) tana ɗaya cikin waɗanda na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Betty ta girme ni da shekara biyu kuma tana da kirki. Daga baya mun yi hidimar majagaba tare a garin Cowra, mai nisan mil 145 a yammacin birnin Sydney. Ni da Betty kawaye ne har yau, ko da yake mun yi hidima tare na ɗan lokaci.
Na zama majagaba na musamman kuma aka tura ni hidima a garin Narrandera, mai nisan mil 137 a kudu maso yamma na garin Cowra. Na yi hidimar majagaba tare da Joy Lennox, (wadda yanzu sunanta Joy Hunter). Ita majagaba ce mai ƙwazo da ta girme ni da shekara biyu. Mu ne kaɗai Shaidu a garin. Ni da ’yar’uwa Joy mun zauna tare da Ray da Esther, ma’aurata masu karimci. Suna da ɗa da yara mata uku, kuma dukan iyalin suna son gaskiya. Ray da ɗansa suna kiwon tumaki kuma suna noman alkama a waje da garin. Esther da ’yammatan kuma suna sana’ar ba mutane masauki. A kowace ranar Lahadi, ni da Joy muna dafa wa iyalin Iron da kuma mutane 12 da suke zama a gidansu abincin dare mai yawan gaske. Waɗannan mutanen da ke aiki a tashar jirgin ƙasa suna cin abinci sosai! Don wannan aikin da muke yi ba ma biyan kuɗin haya. Bayan mun gama wannan dahuwar sai mu yi wanka kuma mu yi nazarin Hasumiyar Tsaro na makon da iyalin Iron. Da Ray da Esther da yaransu huɗu sun shigo cikin gaskiya kuma suka zama mutane na farko da suka kafa Ikilisiyar Narrandera.
A shekara ta 1951, na halarci taron gunduma na Shaidun Jehobah a ƙasar Sydney. A wajen na halarci taro na musamman da aka yi da majagaba da suke son hidima a ƙasashen waje. ’Yan’uwa fiye da 300 uku ne suka halarci wannan taron da aka yi a babban tanti. Ɗan’uwa Nathan Knorr daga Bethel da ke Brooklyn ne ya yi magana da mu kuma ya faɗa cewa ana bukatar a yi wa’azi a kowane ɓangare na duniya, kuma muna ɗokin jin kome da ya faɗa. Daga baya, majagaba da yawa da suka halarci wannan taro sun soma wa’azi a Kudancin Tekun Pasifik da wasu wurare. Na yi farin ciki sosai da aka gayyace ni da ’yan’uwa maza da mata guda 17 daga Ostereliya zuwa aji na 19 na Makarantar Gileyad da aka yi a shekara ta 1952. Ni ’yar shekara 20 ce a lokacin, sha’awa ta na yin hidima a ƙasashen waje ya zama gaskiya!
INA BUKATAR NA YI CANJE-CANJE
Makarantar Gileyad ta sa na ƙara samun cikakken sani na Littafi Mai Tsarki kuma ta ƙarfafa bangaskiyata. Ban da haka, makarantar ta shafi halina a hanya mai kyau. Ni matashiya ce kuma ina son ayyukana da kuma na wasu su kasance babu kuskure ko kaɗan. Ina da tsattsauran ra’ayi game da abubuwa. Alal misali, sa’ad da na ga Ɗan’uwa Knorr yana wasan ƙwallo da wasu matasa a Bethel, abin ya ba ni mamaki.
’Yan’uwa da suke koyarwa a Gileyad maza ne masu fahimi da kuma ƙwarewa sun lura cewa ina fama da wannan ra’ayin da bai dace ba. Suka yi abota da ni kuma suka taimake ni in canja ra’ayina. A hankali, na fahimci cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna kuma yana jin daɗin ƙoƙarin da muke yi amma ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne, ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Wasu ’yan ajina ma sun taimaka mini. Na tuna ɗaya daga cikinsu ta ce mini: “Elva, Jehobah ba ya amfani da tsumagiya don ya sa mu bauta masa. Kada ki cika damun kanki!” Abin da ta gaya mini ya taɓa zuciyata.
Bayan makarantar Gileyad, aka tura ni da ’yan ajina guda huɗu zuwa ƙasar Namibiya, a Afirka. Ba da daɗewa ba, muna nazarin Littafi Mai Tsarki guda 80. Ina son ƙasar Namibiya da kuma aikin wa’azi a ƙasashen waje, amma na riga na soma soyayya da wani ɗan ajina a Gileyad wanda aka tura zuwa Siwizalan. Saboda haka, bayan shekara ɗaya a ƙasar Namibiya, sai na je na sami saurayi na a ƙasar Siwizalan. Muka yi aure, sai na fara bin maigidana a hidimarsa na mai kula da da’ira.
SA’AD DA NAKE FUSKANTAR GWAJI MAI TSANANI
Bayan mun yi shekara biyar muna hidimar kula da da’ira, aka gayyace mu hidima a Bethel na ƙasar Siwizalan. Na yi farin ciki cewa mun kasance cikin iyalin Bethel, kuma cewa muna tare da ’yan’uwa da suka manyanta sosai a cikin gaskiya.
Ba da daɗewa ba bayan muka isa Bethel, sai na gano cewa mijina ya ci amanata kuma ya yi rashin aminci ga Jehobah. Bayan haka, sai ya bar ni, kuma hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Abokaina da suke Bethel sun taimaka mini na jimre da wannan yanayin. Sun saurare ni sa’ad da nake son in yi magana kuma sun bar ni in huta sa’ad da nake bukatar hutu. Kalamansu sun ƙarfafa ni kuma alherinsu ya taimaka mini in jimre da baƙin cikin. Saboda haka dangantakata da Jehobah ta ƙara ƙarfi.
Na kuma tuna da kalaman da abokaina tsofaffi da suka jimre da gwaji suka gaya mini shekarun baya. Wannan ya haɗa da kalaman da Margaret Dunham ta taɓa gaya mini. Ta ce: “Elva, a hidimarki ga Jehobah” za ki fuskanci gwaje-gwaje da yawa, amma za ki fuskanci gwaje-gwaje mafi sa baƙin ciki daga ƙaunatattunki. Sa’ad da kike fuskantar waɗannan gwaje-gwajen, ki dogara ga Jehobah kuma ki tuna cewa kina bauta masa ne ba ’yan Adam ajizai ba.” Wannan shawarar da Margaret ta ba ni ta taimaka mini sosai a waɗannan yanayin masu wuya. Na ƙudura aniya cewa ba zan taɓa ƙyale rashin amincin maigidana ya raba ni da Jehobah ba.
Da shigewar lokaci, sai na koma ƙasar Ostareliya domin in riƙa hidimar majagaba kusa da dangina. Sa’ad da nake doguwar tafiyar zuwa gida, na ji daɗin tattaunawa da wasu fasinjojin jirgin ruwan da muka shiga. A cikin mutanen da nake tattaunawa da su akwai wani mutum shuru-shuru mai suna Arne Gjerde, ɗan ƙasar Norway. Ya ji daɗin tattaunawar da muka yi. Daga baya ya ziyarce ni da iyalina a birnin Sydney. Ya amince da abin da yake koya ba tare da ɓata lokaci ba kuma ya yi baftisma. A shekara ta 1963, ni da Arne muka yi aure, kuma bayan shekara biyu sai na haifi ɗa kuma mun ba shi suna Gary.
NA SAKE FUSKANTAR WANI GWAJI
Da ni da mijina Arne da kuma ɗanmu Gary mun ji daɗi sosai a zamanmu na iyali. Ba da daɗewa ba mijina Arne ya ƙara gina ɗakuna a gidanmu don mu zauna tare da iyayena da suka tsufa. Amma bayan mun yi shekara shida da aure, wani abin baƙin ciki ya faru. Likita ya gano cewa yana da ciwon daji na ƙwaƙwalwa kuma aka kwantar da shi a asibiti. Mijina Arne ya jima a asibiti kuma ina ziyartar sa kowace rana sa’ad da ake ba shi magani. Bayan haka, sai ya ɗan samu sauƙi, amma daga baya sai yanayinsa ya daɗa muni kuma jikinsa ya shanye. Aka gaya mini cewa ’yan makonni ne ya rage kafin ya mutu. Amma Arne ya farfaɗo. Da shigewar lokaci, aka sallame shi kuma na soma kula da shi har ya samu sauƙi. Bayan ɗan lokaci, ya soma tafiya kuma ya ci gaba da hidima a matsayin dattijo. Shi mai fara’a ne da mai ban dariya. Wannan ne ya taimaka masa ya samu sauƙi kuma ya taimaka mini na kula da shi.
Arne ya sake rashin lafiya a shekara ta 1986, bayan shekaru da yawa da samun sauƙi. A lokacin iyayena sun riga sun rasu, saboda haka muka ƙaura zuwa wani kyakkyawan yanki da ake kiran Blue Mountains, a bayan birnin Sydney, kuma muka zauna kusa da abokanmu. Daga baya, ɗanmu Gary ya auri wata kyakkyawar ’yar’uwa mai suna Karin, sai suka ce mu zauna tare a gida ɗaya. Saboda haka, dukanmu muka ƙaura zuwa wani gida da ke kusa da inda ni da Arne muka taɓa zama.
Shekara ɗaya da rabi kafin Arne ya mutu, ba ya iya tashiwa daga gado kuma hakan ya sa yana bukatar a riƙa kula da shi a kowanne lokaci. Tun da yanayinsa ya sa ina kasancewa a gida yawancin lokaci, ina amfani da sa’o’i biyu a kowace rana don karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da nake wannan nazarin na koyi abubuwa da yawa da suka taimaka mini in jimre da yanayina. Kuma na yi farin ciki sosai don ziyarar tsofaffin da ke ikilisiyarmu. Wasu daga cikinsu sun jimre da irin waɗannan matsalolin da nake fuskanta kuma kasancewarsu tare da ni ya ƙarfafa ni sosai! Arne ya rasu a watan Afrilu na shekara ta 2003, kuma yana da begen tashi daga matattu.
TAIMAKO MAFI GIRMA DA NA SAMU
Sa’ad da nake matashiya, ina da tsattsauran ra’ayi, kuma ina son kome ya kasance babu aibi. Amma na koya cewa ba haka rayuwa take ba. Na samu albarka masu yawa kuma na jimre da gwaji masu tsanani guda biyu. Na rasa mijina na farko don ya ci amanata kuma na yi rashin mijina na biyu don ya rasu sanadin rashin lafiya. A cikin dukan waɗannan matsalolin, na samu ja-gora da kuma ƙarfafa a hanyoyi dabam-dabam. Amma wanda ya fi taimaka mini shi ne “mai-zamanin dā,” wato, Jehobah Allah. (Dan. 7:9) Shawararsa ta sa na canja halina kuma saboda haka, na more abubuwa masu ban farin ciki a aikin wa’azi a ƙasashen waje. Sa’ad nake fuskantar matsaloli, ‘jinƙan Jehobah ya ta’azantar da ni.’ (Zab. 94:18, 19) Dangina da abokaina sun ƙaunace ni kuma suna tallafa mini. Sun taimaka mini sosai a waɗannan lokatan matsaloli. (Mis. 17:17) Yawancinsu tsofaffi ne.
Ayuba ya ce: ‘Hikima tana wurin tsofaffi, a cikin tsawon kwanaki kuma fahimi ya ke.’ (Ayu. 12:12) Idan na tuna da rayuwata, zan iya ce abin da Ayuba ya ce gaskiya ce. Shawarwarin da tsofaffi suka ba ni sun taimaka mini, ƙarfafa da suka ba ni ya tallafa mini kuma abota da na yi da su ya inganta rayuwata. Ina godiya cewa na yi abota da su.
Yanzu ni ma tsohuwa ce kuma shekara ta 80. Abubuwan da na fuskanta a rayuwa sun sa na riƙa kula da tsofaffi. Har yanzu, ina sha’awar zuwa wurinsu don in taimaka musu. Amma kuma ina jin daɗin kasancewa da matasa. Ƙarfinsu yana burge ni kuma ƙwazonsu yana ƙarfafa ni. Sa’ad da matasa suka nemi shawara daga wurina, ina jin daɗin taimaka musu ƙwarai.
[Hasiya]
a Wan Elva, Franka Lanbert, ya zama majagaba mai ƙwazo a ƙauyuka na ƙasar Ostareliya.
[Hoto a shafi na 14]
Sa’ad da nake hidimar majagaba tare da Joy Lennox a garin Narrandera
[Hoto a shafi na 15]
Elva tare da ’yan’uwa da ke Bethel na ƙasar Siwizalan a shekara ta 1960
[Hoto a shafi na 16]
Sa’ad da nake kula da mijina Arne a lokacin da yake rashin lafiya