Ka Dogara Ga Jehobah, Allah Na “Lokatai Da Kwanaki”
“Ya kan sāke lokatai da kwanaki, ya kan tuɓe sarakuna, ya kan sarautar da sarakuna.”—DAN. 2:21.
MECE CE AMSARKA?
Ta yaya abubuwa da aka halitta da annabci suka nuna cewa Jehobah ne Babban Mai Tsara Lokaci?
Mene ne sanin cewa Jehobah ne Allah na “lokatai da kwanaki” yake sa mu yi?
Me ya sa Jehobah ba ya bukatar ya canja lokacin da yake son ya cika nufinsa ko da mene ne ’yan Adam suke yi?
1, 2. Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa Jehobah zai iya bayyana ma’anar lokaci?
TUN da daɗewa kafin Jehobah Allah ya halicci ’yan Adam, ya sa ya yiwu su san lokaci. A ranar halitta ta huɗu, Allah ya ce: “Bari haskoki su kasance cikin sararin sama domin su raba tsakanin yini da dare; su zama kuma domin alamu, da wokatai, da kwanaki da shekaru.” (Far. 1:14, 19, 26) Hakan ya faru, daidai da nufin Jehobah.
2 Har ila, masana kimiyya ba su iya bayyana ko mene ne lokaci ba. Wani kundin sani ya ce: “Babu mutumin da zai iya bayyana ainihin ma’anar lokaci.” Amma Jehobah ne kaɗai zai iya yin hakan. Domin shi ne “ya halicci sammai . . . mai-sifanta duniya mai-yinta kuma.” Jehobah ne kuma “mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.” (Isha. 45:18; 46:10) Bari mu tattauna yadda halitta da annabci da suka cika suke nuna cewa Jehobah ne Babban Mai Tsara Lokaci, kuma hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu a gare shi da kuma Littafi Mai Tsarki.
HALITTUN JEHOBAH SUNA ƘARFAFA BANGASKIYARMU
3. Ta yaya halittun Allah suke bin tsarin lokaci sosai?
3 Halittun Allah suna bin tsarin lokaci. Alal misali, yadda duniyar tauraro da kuma tauraro suke tafiya suna nuna hakan. Duniyar tauraro da kuma tauraro suna tafiya a daidai lokacin da aka tsara musu. Ana yin amfani da tafiyar duniyar tauraro da tauraro a cikin sama don sanin yanayin duniya. Kuma sa’ad da mutane suke yin tafiya, duniyar tauraro da kuma tauraro suna taimaka musu su san ko suna a arewa ko kudu ko gabas ko kuma yamma. Tun da Jehobah ne ya halicci dukan waɗannan abubuwan, Shi “mai-ƙarfi” ne sosai kuma ya kamata mu yaba masa.—Karanta Ishaya 40:26.
4. Ta yaya sanin cewa abubuwa masu rai suna ayyuka bisa lokaci ya nuna cewa Jehobah mai hikima ne?
4 Abubuwa masu rai suna ayyuka bisa lokaci. Shuke-shuke da dabbobi da yawa suna bin tsarin lokaci da ke cikin jikinsu. Shi ya sa tsuntsaye da yawa suka san lokacin da za su ƙaura zuwa wani wuri. (Irm. 8:7) ’Yan Adam ma suna yin abubuwa bisa lokaci. Alal misali, jikinmu yana sa mu san lokacin da gari ya waye da kuma lokacin da dare ya yi. Idan muka yi tafiya da jirgin sama zuwa wata ƙasa inda lokaci ya yi dabam da inda muka saba, zai ɗauki ’yan kwanaki kafin mu saba da tsarin lokaci na wannan ƙasar. Saboda haka, a cikin abubuwa da Jehobah ya halitta, akwai misalai da yawa da suka nuna cewa shi ne Allah na “lokatai da kwanaki” kuma yana da iko sosai da kuma hikima. (Karanta Zabura 104:24.) Domin Jehobah yana da hikima da iko marar iyaka, muna da tabbaci cewa zai iya cika nufinsa!
ANNABCE-ANNABCE DA SUKA CIKA A KAN LOKACI SUN ƘARFAFA IMANINMU
5. (a) A wace hanya ce za mu san abin da zai faru da ’yan Adam a nan gaba? (b) Me ya sa Jehobah zai iya gaya mana abin da zai faru nan gaba da kuma lokacin da zai faru?
5 Abubuwan da Jehobah ya halitta sun koya mana abubuwa da yawa game da ‘al’amuransa marasa ganuwa,’ amma ba su bayyana mana abin da zai faru da ’yan Adam a nan gaba ba. (Rom. 1:20) Don mu san amsar, dole ne mu bincika abin da Allah ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi hakan, za mu ga annabce-annabcen da suka cika a kan lokaci! Jehobah zai iya bayyana abin da zai faru a nan gaba. Bugu da ƙari, abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa yakan faru a kan lokaci domin Jehobah Allah zai iya sa abubuwa su faru daidai da nufinsa da kuma ma’ajin lokacinsa.
6. Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana son mu fahimci yadda annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki suka cika?
6 Jehobah yana son waɗanda suke bauta masa su fahimci annabci na Littafi Mai Tsarki kuma su amfana. Ko da yake Allah ba ya ɗaukan lokaci yadda muke, sa’ad da ya gaya mana ainihin lokacin da wani abu zai faru, yakan bayyana yadda za mu fahimta. (Karanta Zabura 90:4.) Alal misali, littafin Ru’ya ta Yohanna ya yi maganar “mala’ikun nan huɗu” waɗanda “aka shirya saboda sa’an da ranan da watan da shekaran,” kuma mun fahimci abin da wannan yake nufi. (R. Yoh. 9:14, 15) Ya kamata sanin yadda annabce-annabce suka cika a kan lokaci, ya sa mu ba da gaskiya ga Allah na “lokatai da kwanaki” da kuma Kalmarsa. Bari mu tattauna wasu misalai.
7. Ta yaya cikar annabcin Irmiya game da Urushalima da Yahuda suka nuna cewa Jehobah ne Babban Mai Tsara Lokaci?
7 Bari mu fara tattauna abin da ya faru a ƙarni na bakwai kafin zamanin Kristi. Maganar Babban Mai Tsara Lokaci “ta zo wurin Irmiya a kan dukan mutanen Yahuda a cikin shekara ta huɗu ta Jehoiakim ɗan Josiah, sarkin Yahuda.” (Irm. 25:1) Jehobah ya annabta cewa za a halaka Urushalima kuma Yahudawa daga ƙasar Yahuda za su koma zaman bauta a ƙasar Babila. Za su “bauta wa sarkin Babila shekara saba’in.” Sojojin Babila sun halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin zamanin Kristi, kuma aka kwashi Yahudawa daga Yahuda zuwa ƙasar Babila. Amma, mene ne zai faru a ƙarshen shekara ta saba’in? Irmiya ya annabta: “In ji Ubangiji, bayan shekara saba’in sun cika domin Babila, zan ziyarce ku, in cika maganata mai-alheri gareku, ina komo da ku a wurin nan.” (Irm. 25:11, 12; 29:10) Wannan annabcin ya cika daidai lokacin da Jehobah ya faɗa, a shekara ta 537 kafin zamanin Kristi bayan Midiya da Farisa suka sa Yahudawa su samu ’yanci daga ƙasar Babila.
8, 9. Ta yaya annabci game da bayyanuwar Almasihu da kuma kafa Mulkin sama suka nuna cewa Jehobah ne Allah na “lokatai da kwanaki”?
8 Za mu tattauna wani annabci da ya shafi mutanen Allah na zamanin dā. Kusan shekara biyu kafin Yahudawa su bar Babila, Allah ya annabta ta bakin annabi Daniyel cewa Almasihu zai bayyana a shekara ta 483 bayan da aka ba da doka a sake gina Urushalima. Sarki na Midiya da Farisa ya ba da wannan dokar a shekara ta 455 kafin zamanin Kristi. Bayan shekara ta 483, a shekara ta 29, aka shafa Yesu Banazari da ruhu mai tsarki a lokacin da ya yi baftisma kuma ya zama Almasihu.a—Neh. 2:1, 5-8; Dan. 9:24, 25; Luk 3:1, 2, 21, 22.
9 Yanzu ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta game da Mulkin. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za a kafa Mulkin Almasihu a sama a shekara ta 1914. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi hakan ta wajen ba da “alamar” bayyanuwar Yesu. Kuma ya yi nuni ga lokacin da za a kawar da Shaiɗan daga sama, kuma hakan zai sa a yi matuƙar wahala a duniya. (Mat. 24:3-14; R. Yoh. 12:9, 12) Wasu annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun yi nuni ga ainihin lokacin, wato, shekara ta 1914, sa’ad da “zamanan Al’ummai [za su] cika” kuma za a soma sarauta a sama.—Luk 21:24; Dan. 4:10-17.b
10. Wanne annabci ne zai cika a kan lokaci?
10 Ba da daɗewa ba, za a fara “ƙunci mai-girma” da Yesu ya annabta. Bayan haka, Yesu zai yi sarauta ta shekara dubu. Babu shakka cewa dukan waɗannan abubuwa za su faru a kan lokaci. Sa’ad da Yesu yake duniya, Jehobah ya riga ya tsara ‘ranar da sa’an’ da waɗannan abubuwa za su faru.—Mat. 24:21, 36; R. Yoh. 20:6.
KA YI AMFANI DA LOKACI YADDA YA DACE
11. Idan mun gaskata cewa muna zama a lokaci na ƙarshe, me ya kamata mu yi?
11 Tun da yake mun san cewa Kristi ya zama Sarki kuma muna zama a “kwanakin ƙarshe,” me ya kamata mu yi? (Dan. 12:4) Mutane da yawa sun lura cewa yanayin duniya yana daɗa muni, amma ba su fahimci ba cewa Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa hakan zai faru a kwanaki na ƙarshe. Suna tsammani cewa wata rana, abubuwa za su lalace, wasu kuma sun gaskata cewa ’yan Adam za su kawo “kwanciyar rai da lafiya.” (1 Tas. 5:3) Mu kuma fa? Idan muka gane cewa muna zama a kwanaki na ƙarshe na duniyar Shaiɗan, hakan zai sa mu yi ƙoƙari mu yi amfani da lokacin da ya rage mu bauta wa Allah na “lokatai da kwanaki” kuma mu taimaki mutane su zo ga saninsa. (2 Tim. 3:1) Dole ne mu yanke shawara mai kyau game da yadda za mu yi amfani da lokaci.—Karanta Afisawa 5:15-17.
12. Mene ne za mu koya daga kalamin Yesu game da kwanakin Nuhu?
12 Da yake duniya tana cike da abubuwa da za su iya raba hankalinmu, ba shi da sauƙi mu yi amfani da lokacinmu yadda ya dace. Yesu ya gargaɗe mu: “Kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayanuwar Ɗan Mutum za ta zama.” Yaya ne kwanakin Nuhu suke? Allah ya gaya wa Nuhu cewa zai kawo ƙarshe ga miyagun mutane na zamaninsa. A lokacin, mugayen mutane za su halaka a ruwan tufana. Nuhu, cikin aminci, ya sanar da saƙon Allah ga mutanen zamaninsa a matsayin “mai-shelan adalci.” (Mat. 24:37; 2 Bit. 2:5) Amma suna “ci, suna sha, suna aure, suna auraswa, . . . ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” Saboda haka, Yesu ya gargaɗe mabiyansa: “Ku zama da shiri: gama cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.” (Mat. 24:38, 39, 44) Wajibi ne mu zama kamar Nuhu amma ba kamar mutanen zamaninsa ba. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da shiri?
13, 14. Sa’ad da muke jiran zuwan Ɗan mutum, me ya kamata mu tuna game da Jehobah da zai taimaka mana mu bauta masa?
13 Ko da yake Ɗan mutum zai zo a sa’ar da ba mu sani ba, yana da kyau mu tuna cewa Jehobah shi ne Babban Mai Tsara Lokaci. Ko mene ne zai faru a duniya, ko kuma abubuwan da ’yan Adam suka yi shirin yi, ba za su hana Jehobah aiwatar da abubuwan da ya shirya da kuma yadda sakamakon za su kasance ba. (Karanta Daniyel 2:21.) Hakika, Misalai 21:1 ya ce: “Zuciyar sarki tana hannun Ubangiji kamar magudanan ruwaye: Ya kan juya ta dukan inda ya ga dama.”
14 Jehobah zai iya sarrafa abubuwa don ya cika nufinsa a kan lokaci. Muhimman canje-canje da suke faruwa a duniya suna cika annabci, musamman ma annabci game da wa’azin bishara Mulkin Allah da ake yi a dukan duniya. Ka yi tunanin wargajewar Ƙasar Rasha ta Dā da sakamakon da ya biyo bayan hakan. Mutane da yawa ba su yi zato cewa waɗannan gagarumin canje-canjen da aka yi za su faru nan da nan ba. Amma, saboda waɗannan canje-canjen, yanzu ana wa’azin bishara a ƙasashe da yawa da aka hana aikinmu a dā. Bari mu yi iya ƙoƙarinmu domin mu riƙa amfani da lokacinmu da kyau don bauta wa Jehobah, Allah na “lokatai da kwanaki” cikin aminci.
KA YI IMANI CEWA JEHOBAH ZAI CIKA ANNABCINSA A KAN LOKACI
15. Sa’ad da aka yi canje-canje a ƙungiyar Jehobah, yaya za mu nuna cewa muna da aminci?
15 Yin wa’azin Mulkin a waɗannan kwanaki na ƙarshe yana bukatar mu kasance da imani cewa Jehobah zai cika nufinsa a kan lokaci. Da yake yanayin duniya yana canjawa a kai a kai, wani lokaci muna bukatar mu canja yadda muke wa’azi. A wasu lokatai, ƙungiyar Jehobah tana yin gyara don ta taimaka mana mu yi wa’azin bishara a hanyar da ta fi ba da amfani. Sa’ad da muka ba da haɗin kai ga waɗannan canje-canjen da kuma yin hidima a ƙarƙashin Ɗansa, “shugaban ikilisiya,” muna nuna cewa mun dogara ga Allah na “lokatai da kwanaki.”—Afis. 5:23.
16. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana a kan kari?
16 Jehobah yana son mu riƙa yin addu’a a gare shi a kowane lokaci kuma mu gaskata da dukan zuciyarmu cewa zai “taimake mu a kan kari.” (Ibran. 4:16, Littafi Mai Tsarki) Wannan ya nuna mana cewa yan ƙaunarmu kuma ya damu da kowannenmu. (Mat. 6:8; 10:29-31) Muna nuna cewa muna da bangaskiya ga Jehobah idan muna neman taimakonsa ta yin addu’a a kai a kai kuma muna bin ja-gorancinsa. Bugu da ƙari, mu riƙa tunawa da ’yan’uwanmu Kiristoci a cikin addu’a.
17, 18. (a) Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka a kan maƙiyansa nan ba da daɗewa ba? (b) Wane tunanin banza ne ya kamata mu guji?
17 Yanzu ba lokacin “raurawa ta wurin rashin bangaskiya” ba ne, amma lokaci ne da za mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi sosai. (Rom. 4:20) Maƙiyan Allah, wato, Shaiɗan da mabiyansa suna ƙoƙari su hana mu yin aikin da Yesu ya ce mabiyansa su yi. (Mat. 28:19, 20) Duk da harin da Iblis yake kawo mana, mun san cewa Jehobah ‘Allah mai-rai ne, Mai-ceton dukan mutane, musamman waɗanda ke ba da gaskiya.’ Ya “san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba.”—1 Tim. 4:10; 2 Bit. 2:9.
18 Ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo ƙarshen mugun yanayi da duniya take ciki a yau. Ko da yake ba mu san yadda da kuma lokacin da hakan zai faru ba, amma mun san cewa Kristi zai halaka maƙiyan Allah a lokacin da ya dace, kuma kowa zai san cewa Jehobah ne ya cancanta ya yi sarautar sararin sama da kuma duniya. Saboda haka, za mu yi babban kuskure idan ba mu san ma’anar “lokatai da kwanaki” da muke rayuwa a ciki yanzu ba. Wajibi ne mu yi hattara kada mu fara tunani cewa “al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.”—1 Tas. 5:1; 2 Bit. 3:3, 4.
KA KASANCE DA HALIN “JIRA”
19, 20. Me ya sa za mu kasance da halin jiran Jehobah?
19 Ainihin nufin Allah ga ’yan Adam ya haɗa da yin rayuwa har abada don su ci gaba da koyo game da shi da kuma abubuwa masu kyau da ya halitta. Littafin Mai-Wa’azi 3:11 ya ce game da Jehobah: “Ya sa kowane abu ya yi jamali a lokacinsa: ya kuma sa madawwaman zamanai a cikin zuciyarsu, yadda mutum ba za ya bincike aikin Allah ba da ya yi tun farko, har ƙarshe kuma.”
20 Muna farin ciki sosai cewa Jehobah bai canja nufinsa ga ’yan Adam ba! (Mal. 3:6) A wajen Allah “sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” (Yaƙ. 1:17) Inuwa tana juyawa domin duniya tana zagayawa, amma shigewar lokaci ba ya shafan Jehobah. Shi ne “Sarki na zamanu.” (1 Tim. 1:17) Saboda haka, bari mu kasance da halin ‘jiran Allah mai cetonmu.’ (Mi. 7:7) Hakika, “ku ƙarfafa, bari zuciyarku ta yi gaba gaɗi, dukanku masu-sauraro ga Ubangiji.”—Zab. 31:24.
[Hasiya]
a Ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shafuffuka na 197-199.
b Ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shafuffuka na 215-218.
[Hoto a shafi na 19]
Daniyel ya gaskata cewa annabcin da Allah ya nuna masa zai cika
[Hoto a shafi na 21]
Kana amfani da lokaci yadda ya dace don ka yi nufin Jehobah?