Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/15 pp. 18-21
  • Na Yi Shekara Saba’in Ina Riƙe da Ƙafar Bayahude

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Yi Shekara Saba’in Ina Riƙe da Ƙafar Bayahude
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘MENE NE MATSAYINA?’
  • HIDIMAR MAJAGABA A LOKACIN YAƘI
  • NA SOMA HIDIMA A BETHEL
  • BA ZAN TAƁA MANTA DA MAKARANTAR GILEYAD BA
  • HIDIMAR KULA DA DA’IRA DA SAKE KOMA BETHEL
  • HIDIMA A ƘASAR FARANSA
  • AURE DA ƘARIN GATA
  • ‘BA KULLUM BA NE ZA KU KASANCE DA NI BA’
  • Abin da Na Cim Ma a Hidima ta Cikakken Lokaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Gayyata ga Kowa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Na Sami Albarka a Yin Aiki da Mutanen da Suka Manyanta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/15 pp. 18-21

Tarihi

Na Yi Shekara Saba’in Ina Riƙe da Ƙafar Bayahude

Leonard Smith ne ya ba da labarin

Sa’ad da nake matashi, ayoyin Littafi Mai Tsarki guda biyu sun burge ni. Yanzu, bayan shekara 70, zan iya tuna lokacin da na fahimci ma’anar Zakariya 8:23 sosai, wadda ta yi maganar “mutum goma” da za su kama “ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi.” Sun gaya wa Bayahuden: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”

BAYAHUDEN yana wakiltar shafaffun Kiristoci, kuma “mutum goma” suna wakiltar “waɗansu tumaki,” ko kuma waɗanda suke rukunin “Jonadab,” kamar yadda aka san su a lokacin.a (Yoh. 10:16) Sa’ad da na fahimci gaskiyar wannan ayar, na gane cewa idan zan rayu a duniya har abada, wajibi ne in tallafa wa rukunin shafaffu cikin aminci.

Kwatancin Yesu na “tumaki” da “awaki” da ke Matta 25:31-46 ya kuma burge ni sosai. ‘Tumakin’ suna kwatanta waɗanda suka samu lada a lokacin kwanaki na ƙarshe saboda alherin da suke yi wa shafaffun ’yan’uwan Kristi da suke duniya. A matsayin matashi wanda yake cikin rukunin Jonadab, na gaya wa kaina, ‘idan kana son Kristi ya ɗauke ka a matsayin tunkiya, wajibi ne ka goyi bayan ’yan’uwansa shafaffu, ka amince da shugabancinsu domin Allah yana tare da su.’ Na yi shekara fiye da saba’in ina bin wannan ja-gorar.

‘MENE NE MATSAYINA?’

Mahaifiyata ta yi baftisma a shekara ta 1925 a majami’ar taro da ke Bethel. Ana kiran wannan majami’ar London Tabernacle kuma ’yan’uwan da ke wannan yankin suna amfani da majami’ar. An haife ni a ranar 15 ga Oktoba, 1926. Kuma a watan Maris 1940 ne na yi baftisma a wani babban taro da aka yi a birnin Dover da ke gaɓar tekun Ingila. Ƙaunar da nake yi wa gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta ƙaru. Na fara aiki da shafaffu a lokacin da nake wa’azi tare da mahaifiyata tun da ita shafaffiya ce. A lokacin, mahaifina da yayata ba sa bauta wa Jehobah. Muna Ikilisiyar Gillingham da ke kudu maso gabas na Ingila, yawancin waɗanda suke ikilisiyar shafaffun Kiristoci ne. Mahaifiyata ta kafa misali mai kyau na yin wa’azi da ƙwazo.

A watan Satumba na 1941, a wani taron gunduma da aka yi a birnin Leicester ne na saurari wani jawabi mai jigo “aminci,” an tattauna batun wanda ya cancanci ya yi sarautar ’yan Adam a wannan jawabin. Wannan jawabin ya sa na fahimci cewa wannan batun da ke tsakanin Jehobah da Shaiɗan ya shafe mu. Saboda haka, muna bukata mu goyi bayan Jehobah kuma mu riƙe amincinmu gare shi a matsayin Wanda ya cancanci ya mulke ’yan Adam.

A wannan taron gunduma, an yi magana sosai a kan hidimar majagaba, kuma an ƙarfafa matasa su mai da ita maƙasudinsu. Wani jawabin da aka ba da mai jigon nan “Pioneer’s Place in the Organization” (Matsayin Majagaba a Cikin Ƙungiyar Jehobah) ya sa na yi wannan tambayar: ‘Mene ne matsayina?’ Wannan taron gunduma ya tabbatar mini cewa a matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda ke rukunin Jonadab wajibi ne in yi iya ƙoƙarina in taimaka wa rukunin shafaffu a aikin wa’azi. A wannan taron ne da aka yi birnin Leicester na cika afilkeshan fom na hidimar majagaba.

HIDIMAR MAJAGABA A LOKACIN YAƘI

A ranar 1 ga Disamba, 1941, sa’ad da nake ɗan shekara 15 ne aka naɗa ni majagaba na musamman. Mahaifiyata ce ta farko da muka yi hidimar majagaba tare, amma bayan wajen shakara ɗaya, ta daina hidimar majagaba don rashin lafiya. Ofishin reshe na Landan suka haɗa ni da Ron Parkin, yanzu yana hidima a matsayin ɗaya daga cikin Kwamitin Reshe na ƙasar Puerto Rico.

An tura mu hidima a garurrukan Broadstairs da Ramsgate, waɗanda ke bakin teku a yankin Kent, inda muka karɓi hayar ɗaki guda. Guzurin da ake ba wa majagaba na musamman a kowane wata dala 8 ne. Sa’ad da muka biya kuɗin haya, abin da ya rage ba ya isa kuɗin abincin da za mu ci. Amma Jehobah ba ya fasa biyan bukatunmu.

A yawancin lokaci, muna tuƙa keke da kaya masu nauyi a kai duk da iska mai ƙarfi daga North Sea [Tekun Arewa]. Kuma muna fama da harin bama-bamai da ’yan Jamus suke kai wa Landan ta yankin Kent. Akwai ranar da na yi tsalle daga kan keke na faɗa a cikin kwata don in ƙauce wa wani bom da aka harba kuma bom ɗin ya fashe a wani fili da ke kusa da mu. Duk da haka mun yi farin ciki a shekarun da muka yi muna hidima a yankin Kent.

NA SOMA HIDIMA A BETHEL

Mahaifiyata ta sha yin magana masu daɗi game da hidimar Bethel. Takan ce: “Ba abin da nake so kamar a ce kana hidima a Bethel.” Saboda haka, na yi farin ciki sosai sa’ad da aka gayyace ni zuwa Bethel da ke Landan a watan Janairu a shekara ta 1946 don yin hidima na mako uku. Bayan makonni ukun, ɗan’uwa Pryce Hughes, mai kula da reshe ya ce in ci gaba da hidima a Bethel. Koyarwa da na samu a nan ya taimaka mini a dukan rayuwata.

’Yan’uwa wajen 30 ne suke hidima a Bethel na Landan a lokacin, yawanci matasa maza marasa aure ne, amma akwai ’yan’uwa shafaffun da dama waɗanda suka haɗa da Pryce Hughes da Edgar Clay da kuma John Barr wanda ya zama ɗaya daga cikin Hukumar Mulki. Tallafa wa ’yan’uwan Kristi ta wajen yin hidima a matsayin matashi a ƙarƙashin ja-gorancin waɗannan “jigajigai” babban gata ne! —Gal. 2:9.

Wata rana a Bethel, wani ɗan’uwa ya gaya mini cewa wata ’yar’uwa tana son gani na a waje. Abin mamaki, mahaifiyata ce, ta zo da wata kyauta a hannunta. Ta ce ba za ta shigo ciki ba, don ba ta son ta katse mini aiki, sai ta ba ni kyautar kuma ta tafi. Kyautar rigar sanyi ce. Wannan kyautar da ta ba ni ta tuna mini da yadda Hannatu take kai wa Sama’ila rigar sanyi sa’ad da yake hidima a mazauni.—1 Sam. 2:18, 19.

BA ZAN TAƁA MANTA DA MAKARANTAR GILEYAD BA

An ba mu biyar da ke hidima a Bethel takardar gayyata zuwa Makarantar Gileyad a Amirka a shekara ta 1947. Kuma a shekara ta gaba muka halarci aji na 11 na makarantar. Sa’ad da muka isa, ana sanyin sosai a arewancin birnin New York, inda ake makarantar. Na yi farin ciki sosai don ina da rigar sanyi da mahaifiyata ta ba ni.

Ban zan taɓa manta da wata shida da na yi a Gileyad ba. Yin cuɗanya da abokan makaranta daga ƙasashe 16 ya sa na samu ƙarin ilimi. Ƙari ga koyarwa da ya sa na ci gaba da dangantakata da Jehobah, na amfana ta yin abokantaka da Kiristoci da suka manyanta. Ɗaya cikin abokan makarantarmu mai suna Lloyd Barry da ɗaya cikin malaman makarantar, Albert Schroeder da kuma John Booth, mai kula da Kingdom Farm (inda ake Makarantar Giliead) daga baya sun yi hidima a matsayin waɗanda suke cikin Hukumar Mulki. Ina tunawa da shawara mai kyau da waɗannan ’yan’uwa suka ba ni da kuma misalinsu mai kyau na aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.

HIDIMAR KULA DA DA’IRA DA SAKE KOMA BETHEL

An tura ni hidimar kula da da’ira a jihar Ohio na Amirka da na sauke karatu a makarantar Gileyad. A lokacin ni ɗan shekara 21 ne, amma ’yan’uwan sun amince da ƙwazo na na matashi. A wannan da’irar, na koyi abubuwa da yawa daga ’yan’uwa da suka manyanta.

Bayan ’yan watanni, an ce na koma Bethel da ke Brooklyn don na samu ƙarin koyarwa. A wannan lokacin, na san jigajigai kamar su Milton Henschel da Karl Klein da Nathan Knorr da T. J. (Bud) Sullivan da kuma Lyman Swingle, kuma dukansu sun yi hidima a matsayin waɗanda suke cikin Hukumar Mulki. Ganin yadda suke aiki da kuma lura da yadda suke rayuwa da ta dace da Kirista ya sa na samu ƙarin fahimi. Hakan ya sa na ƙara amince da ƙungiyar Jehobah sosai. Sai aka ce na koma ƙasar Turai don na ci gaba da hidimata a wajen.

Mahaifiyata ta rasu a watan Fabrairu a shekara ta 1950. Da aka gama jana’izar, sai na tattauna sosai da mahaifina da kuma yayata Dora. Sai na tambaye su abin da suke shirin su yi game da bauta wa Jehobah yanzu da Mama ta rasu kuma ni na bar gida. Sun san wani ɗan’uwa tsoho shafaffe mai suna Harry Browning kuma suna daraja shi, kuma sun yarda su tattauna da shi. Baba da Dora suka yi baftisma bayan shekara guda. Bayan haka, aka naɗa Baba bawa mai hidima a Ikilisiyar Gillingham. Kuma bayan rasuwar Baba, Dora ta auri wani dattijo mai aminci, mai suna Roy Moreton, kuma ta bauta wa Jehobah da aminci har mutuwarta a shekara ta 2010.

HIDIMA A ƘASAR FARANSA

Sa’ad da nake makaranta, na karanta Faransanci da Jamusanci da yaren Latin, kuma a cikin su uku, Farasanci ya fi mini wuya sosai. Saboda haka, ban yi farin ciki sosai ba sa’ad da aka gaya mini na je na taimaka a Bethel na birnin Paris a ƙasar Faransa. A wajen, na samu gatan yin aiki tare da wani ɗan’uwa tsoho shafaffe mai suna Henri Geiger, bawa mai kula da reshen. Aikin ba shi da sauƙi kuma na yi kurakurai da yawa, amma na koyi yadda ake sha’ani da mutane.

Ƙari ga haka, an shirya za a yi taron ƙasashe na farko a shekara ta 1951, bayan yaƙin duniya na biyu kuma ina cikin waɗanda suke shirya taron. Wani saurayi mai kula mai ziyara mai suna Léopold Jontès ya zo Bethel don ya taimake ni. Daga baya aka naɗa Léopold a matsayin mai kula da reshe. An yi taron a filin wasan Palais des sports, kusa da Eiffel Tower. Mutane daga ƙasashe 28 ne suka halarci taron. A rana ta ƙarshe, Shaidu 6,000 ’yan ƙasar Faransa sun yi farin ciki sa’ad da suka ga cewa mutane 10,456 ne sun halarci taron!

Sa’ad da na isa ƙasar Faransa, ban iya Faransanci sosai ba. Wani babban kuskuren da na yi shi ne ba na yin magana sai na tabbata cewa abin da nake son in faɗa daidai ne. Yin haka bai taimake ni ba sam. Idan ba ka yi kuskure ba, babu yadda za a iya maka gyara kuma ba za ka samu ci gaba ba.

Sai na shiga wani makarantar da ake koya wa baƙi Faransanci don in magance wannan matsalar. Ina zuwa makarantar a yammar da ba a taro. Sai na soma son Faransanci, kuma da shigewar shekaru son da nake yi wa yaren ya ƙaru. Koyon yaren ya taimaka mini sosai don daga baya na soma aikin fassara a ofishin reshe na ƙasar Faransa. Da shigewar lokaci na zama mai fassara, ina fassara daga Turanci zuwa Faransanci. Gata ne in taimaka wajen yin fassara zuwa Faransanci don ’yan’uwa da suke Faransanci a dukan duniya su amfana daga wannan koyarwar Littafi Mai Tsarki da rukunin bawa ke tanadarwa.—Mat. 24:45-47.

AURE DA ƘARIN GATA

A shekara ta 1956, na auri matata mai suna Esther. Ita wata majagaba ce ’yar ƙasar Siwizalan da na haɗu da ita shekarun baya. Mun yi aure a Majami’ar Mulki da ke kusa da Bethel na Landan (London Tabernacle na dā, inda mahaifiyata ta yi baftisma). Ɗan’uwa Hughes ne ya ba da jawabin aurenmu. Mahaifiyar Esther ta halarci bikin, ita ma tana da begen zuwa sama. Ban da abokiyar zama mai ƙauna da kuma aminci da na samu, aurena ya sa na samu suruka mai dangantaka da Jehobah sosai kuma mun yi zumunci sosai da ita kafin ta gama hidimarta a duniya a shekara ta 2000.

Bayan aurenmu, ni da Esther muka koma zama a wajen Bethel. Amma na ci gaba da fassara a Bethel, matata Esther kuma tana hidimar majagaba na musamman a garuruka da ke kusa da Paris. Ta taimaka wa mutane da yawa su zama bayin Jehobah. A shekara ta 1964 an gayyace mu mu zauna a Bethel. A shekara ta 1976 sa’ad da aka kafa tsarin Kwamitin Reshe, sai aka naɗa ni ɗaya daga cikinsu. Esther ta ci gaba ta tallafa mini sosai a duk waɗannan shekarun.

‘BA KULLUM BA NE ZA KU KASANCE DA NI BA’

Ina samun gatan zuwa hedkwata da ke birnin New York lokaci-lokaci. Sa’ad da na je, ina samun shawarwari masu kyau daga ’yan’uwa dabam-dabam da ke Hukumar Mulki. Alal misali, a wani lokacin da na bayyana damuwata na kammala wani aikin da ke bukatar a gama shi da wuri, Ɗan’uwa Knorr ya yi murmushi, sai ya ce: “Kada ka damu. Kai dai ka yi aiki kawai!” Tun daga lokacin idan aiki ya taru maimakon in riƙa yawan damuwa, sai in soma yin aikin ɗaya bayan ɗaya kuma ta hakan, sai in gama aikin a kan lokaci.

Gab da mutuwarsa, Yesu gaya wa almajiransa: “Ba ku da ni kullum.” (Mat. 26:11) Mu da muke rukunin waɗansu tumaki mun san cewa ba kullum ba ne za mu riƙa kasancewa da ’yan’uwan Kristi shafaffu a duniya. Saboda haka, babban gata ne a gare ni da na yi shekaru sama da 70 ina tarayya da shafaffu da yawa, wato, ina riƙe da kafar Bayahude.

[Hasiya]

a Domin sanin ma’anar kalmar nan “Jonadab,” ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2010, shafuffuka na 16 zuwa 17, sakin layi na 8 da 10.

[Bayanin da ke shafi na 21]

Ɗan’uwa Knorr ya yi murmushi, sai ya ce: “Kada ka damu. Kai dai ka yi aiki kawai!”

[Hotona a shafi na 19]

(Hagu) Mahaifiyata da mahaifina

(Dama) A cikin makarantar Gileyad a shekara ta 1948, sanye da rigar sanyi da mahaifiyata ta ba ni

[Hoto a shafi na 20]

Ina fassara jawabin Ɗan’uwa Lloyd Barry a bikin keɓe reshen ƙasar Faransa a shekara ta 1997

[Hotona a shafi na 21]

(Hagu) Tare da Esther a ranar bikin aurenmu

(Dama) Sa’ad da muke wa’azi tare

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba